← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 138

Sashe 55

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
```Hajiya ga kaya nan Masha Allah, Available price
Huluna da Mayafai, da na yara sai Wanda ranko yakeso gasunan kala kala, Hajiya muna dasu ba iya hulana da Mayafai ba, har da shadodin na fitar sallah, Hajiya domin hutar dake da fitar dake kunya na tanadi yadda ba zaku sha wahalar yawo kasuwa a cikin azumi ba, don haka kafin kishiyarki tazo ta sata au 🤣😹😂 kafin kishiyarki tazo ta saya na tayiwa mijinku shakara gara kizo ki sata au 😔🤣😹 baki ya saba gara kizo ki saya, barauniyar gida, kai Sarauniyar gida 😂😹 atow kayana na Uwaren gida da na Amare ne```
*TUNTUBE WANNAN NUMBER 08130269641*

*026*
Yadda ya karya hula zaka rantse cikakken bahaushe ne, amma yanayin fatarshi zai nuna maka cewa bai da alaka da hausawa. Lokacin da ya fito daga dakin shi, Hajiya tana kallonshi daga kasa, kamilalliyar fuskar shi, me cike da kamewa ta kalla sannan ta shiga tasbihi ga Allah madaukakin sarki. "Ya Allah ka tsare min bawan nan naka." Ta fada tana cigaba da tasbihi har ya iso inda take, takalmin kafarshi kawai abin dubawa ne. Haka ya wuce ta suka fita tana bayan shi yana gabanta, sai da suka isa wurin kofar ya bude mata, sannan suka shiga bangaren Nana, haka suka iske falon a cike, gaban Hajiya ne ya fadi, tunda ta gan su tasan Babu alkhairi a wannan zaman nasu, don haka ta shiga da addu'a a bakinta.

"Assalamu alaikum jama'a, Barkanku dai."
"Wa'alaikimun Salam, barkanki Sa'adatu." Yadda suka amsa mata, yasa jikinta ya kara bata akwai wani abu. Zama tayi a daya daga cikin kujerar falon, Shi kuma ya zauna a kasar kafarta. Sai da aka yi gaishe gaishe hankalinshi yana kan wayarshi. Kafin aka bude taron da addu'a. Shiru falon ya ɗauka aka rasa wanda zai fara magana, Hajiya Fauziya ta ce. "Nana kinyi shiru abin arziki ya tara mu ba na tsiya ba"
"Eh wallahi fa, dama Sa'adatu." D'ago kai Hajiya tayi tana kallon Nana, baki daya sai ta cika mata idanu. "Na'am Nana!" "Hmmm dama dama!" "Dama me Nana?" "Wai cewa nayi a cikin yan matan gidan nan ya duba daya ya zab'a."
"Ai shine maganar? Tow ai Nana na gaya miki tsakaninku ne na Familyn Ba'are, ni a caca aka ciyo ni gaki ga Majid din Allah ya baku sa'a."
"Ashe akwai babban Al'amari Hajiya shine baku gayyace ni ba?" Inji Aryan yana shigowa falon, yadda yake tafiya zaka tabbatar da iskanci yake ji A ranshi. Domin kuwa bai kawo haka ba, shi dai yana shiga gidan ya ga basu nan, har zai fita yake tambayar Lawe yake gaya mashi ya fito ban daki ya ga fitarsu ta kofar Nana. Zama yayi a stool bakinciki ne ya kama Nana, tasan da babu Aryan zata iya rarrashin Majid,. Amma da Aryan yazo ko ta kulla sai ya kunce mata.
"Alhajina Maisarah ko Afiyyah." Ajiye wayar shi yayi yana kallon yadda ta ririta fuska. Alamar tana son kada ya bata kunya. "Ni ba zan aure su ba, matar da zan aura Hajiyata ce zata nima min, sannan Nana na gaya miki ki daina shiga harkana baki ji ko."
"A'a Alhaji!" Ta faɗa tana ware idanun tana kallon yadda ya saka hannu a cikin aljuhun rigar shi. Tasan bindigarshi zai ciro "Alhaji Fauziya uwar munafukai ce ta ce na had'aka aure da Maisarah da Afiyyah, wallahi ba tunanina ba ne, tunaninta ne."
"Hajiya tashi muje!" Ya fada yana mikewa, "Kenan idan baka amshi auren nan ba yana nufin kai ba cikakken namiji ba ne? Ko dai baka da lafiya ana boye mana ne, aeeeeh da alamu mutumin hotiho ne, babu karfin da zai raxana mace, koda yake kai idan aka baka mace karshe a shiga hakkinta aikin sojan shi ya kamace ka."

Inji Sajjid da ya fito tare da Amaan.
"Idan hakan ce zata saka ya zama cikakken namiji, tow ba zai amshi auren ba. " Inji Hajiya ta juya tana kallon Tani. "Da alamu bata gaya maka cewa shi aure da Yaron ciki aure darajarsu ba daya ba ne, shi dan aure yana da wata isa da kamala da duk inda ya shiga sai an girmama shi domin iyayenshi sun san cewa ba zasu b'ata mishi gobenshi ba, duk da a caca aka ciyo ni, ban yi zaman dandi ba, zaman aure nayi na haifi kyawawan irin da babu irinsu." Sannan ta juya ga Amaan da yake zare idanu. Takawa tayi har inda yake ta ce mishi. "Kayi kokari muje!" Ta fada tana jin kamar ta fashe da kuka, ita kuma shi ne jarabawar ta, ace yaro baka isa kayi kome ba sai ya gayawa kowa. Kowa ma abokan gabanka waɗanda basu da buri sai ganin bayanka.

"Hajiya ni fa ban gaya musu kome ba." Bata ce mishi cikanka ba, har suka isa falonta. Sakin hannunshi tayi ta zube a kujerar , tana kallonshi ranta a b'ace yake kuma abinda zuciyarta ke son faɗa zai iya saka ya kara lalacewa sama da yanzu, "Hajiya na rantse da Allah, ban fadi kome ba." "Gaskiya baka fadi kome ba, sharri aka maka ko? Taya wancan tsinannen ya san matsalarshi? Wato kai dai ina ga baka da banbanci da jaki, domin kwanyarka bata daukar lissafi."
"Meeting din da za ayi gobe ka soke sunanshi a cikin board director." Inji hajiya ta kara kallon Aryan, "akai shi matsayin karamin ma'aikaci kamar kowa jahilcinshi ba zai bashi damar aiki ba."
"A'a Hajiya, tsanar da Amaan yayi min ni ba zan tab'a mishi ba, tayiyu shi yana da dalilinsa, amma ni bani da hujjar tsanarshi. Don haka ki kyale shi a matsayinsa, haka da yayi min yana kara min son shine, domin akwai wani abu da yake boyewa sama da tsanar da yayi min ba iya tsana ce take fitowa daga kalamanshi ba, har da kauna da bai san yana min ba. Shi yasa nake mishi uziri.". Ya faɗa, kafin ya wuce dakinshi, rufe kofar dakin yayi ya jingina a jikin kofar. Yana jin kamar ya fashe da kuka, me yasa shi yake jin ciwo sama da kowa? Me yasa yake jin zafin haka? Da yana da wata hanya da ya nisanta kanshi da kasar nan bakiɗaya.
Bayan barin Majid falon, Hajiya ta kalle shi, "ka ji dadinka wallahi, Allah ya shirye ka" tsaki Aryan yayi ya bar falon, hatta Matarshi sai da ta fahimci ranshi ya b'aci, don har dare bai da walwala.
Sai lokutan sallah yake fito da shi, bakiɗaya sai ya tsangwame kanshi. Da dare Hajiya da kanta ta kai mishi ruwan tea, yana cikin duhun shi na fama dama tasan za ayi haka, "tashi ka sha ruwan zafi!" Tashi yayi zaune, ya amshi kofin tana tsaye akanshi ya sha ya ajiye kofin a gefen gadonshi, "Zaka yi aure!" Da sauri ya d'ago kai. "Eh zaka yi aure koda kuwa babu wani tarayya, idan kayi auren ka tafi da matarka."
"Hajiya!"
"Maisarah ta bar gidan nan tun kafin rasuwar Babanku, Sannan mahaifiyarta kawai take mu'amala da ita, sau biyu muna haduwa a Saudiya, tana son yin magana amma tana ganin Mahaifiyarta zata yi shiru mu gaisa."
"Hajiya idan ta san ba zan mata..."
"Kada ka damu, dazun na kira Hajiya Sanah na tambaye ta, ko tana da saurayi ne? Ta ce babu hankalina ya fi kwanciya da Maisarah domin Afiyyah suna tare da Sajjid, duk abinda zai haɗaka da Tani ina avoiding ɗinshi."
"Hajiya!"
"Kada ka ce min kome!"ta faɗa tana barin dakin, zuwa yanzu Hajiya tana son fitar da wani abin da ba kowa ya sani ba, daga ita sai Majid dangane da Mutuwar Mamman Ba'are, idan har tayi hi jack points, tow ba makawa zata iya saka wanda yayi kisan motsi. Duk da bata san meye ake shiryawa ba, sai dai tafi tunanin ana shirin da bata san ta inda xa a fito mata ba.
***
Monday.
A yau monday akwai batutuwa da yawa da ake son aiwatarwa a kamfanonin BA'ARE GOLDEN EMPIRES, sai dai wani abin da ya tab'a zuciyar al'umma shine tashi da samun labarin mutuwar babban manajan kamfanin.
Daga Hajiya har yaranta hankalinsu a tashe yake, kuma abin tambayar anan shi ne, waye ya kashe shi? Shin kashe kansa yayi ne? Tow akan me?
Majid kan kin saka kanshi yayi cikin maganar, kuma bai da niyyar haka kuma har Hajiya ta fahimci haka, shi yasa ta tsaya ita da Aryan suka yi ta shige da fice. A cikin kwanaki uku sun jigata, jinin Hajiya hawa yake yana sauka, dole Aneesah ta tsaya a gefen Aryan, ga sintirin yan sanda a kwanakin.
Sai da aka kwashi sati daya ana abu ɗaya, karshe tafiyar Majid da bai samu yayi ba kenan, ya kara niman excuse.
A cikin sati biyu da yin abin, aka ga wasu mutane haka kawai suka rufe Kamfanin. Tsawon awa takwas aka dauka, kafin aka bude kamfanin kamar babu abinda ya faru.
Chapter 55 · 0% Book details