Sashe 49
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Wannan abin yayi matukar yiwa mahaifinshi ciwo, har kwanan gobe yana zuba idon ganin shi, Yazid yana matukar tausayin mata da Yara, akan mahaifiyarshi ya kara jin tausayin Yaya mata, kuma wani abin da yake kara saka shi tausayinta, ita sikila ce. Sai akayi dace shi bai da shi, haka yasa yake son Reshmah kamar zai haukace da ta fara haihuwa ma bai tab'a ce mata ga zab'in shi ba, sunan da takeso take sakawa. Tozali da yayi da Zahrah yaji duniya bai tab'a tausayi da son wata Y'a mace ba kamar ta, sannan baki daya sansanin da suka zauna mutanen Yazid ne, hatta Uwar mugu dalilin da yasa Nawwas yazo nimanshi wurinta kenan, sai gashi kuma Nawwas din jin kamar Yazid din yana zuwa yasa shi guduwa da yan matan.
Matarshi itama balarabiya ce, Reshmah mace ce mai tsananin kishi da saurin fushi, sannan shima Yazid yana matukar kiyayye abinda zai saka kishinta ya fito har ayi tunanin wani abu. A wannan dajin idan kana son ka fita sai ka je an saka maka wasu kwayoyin da zaka masa safara da shi idan ka sha zaka je a cire maka, sannan kayi tafiyarka daga nan ka samu yanci, ba kuma zai barka ba domin abin shi kamar da siddabaru domin ko ka bar dajin ka manta kenan. Ba zaka kara tunawa ba, da haka Yazid yafi karfin abokan gabanshi, domin yana fito da kayanshi ta kowace fuskar ya sayar a waje.
Lokacin da muka zo garin ina cikin waɗanda aka rabawa aikin shara da goge gogen gidanshi, idan har Matarshi ta rigashi tashi hatta bango sai na goge, sannan babu ruwanta da ina da baby ko bani da Babyn, matar nan yar bala'i ce. Kafin Yazid ya fito na gama kome na bar gidan. Sai yamma kuma na koma.
Ban san me yasa ba ko yana sane da yadda matarshi take saka ni a gaba da fitinar aiki, ranar ina zaune a kofar gidan da muke sai gashi ya zo ina jijjiga Baby. "Babyn Zahran bata yi barci ba ne?" Juyawa nayi zan yi magana domin ban zata shi ba ne. Sunkuyar da kai nayi na ce mishi. "Yallabai kai ne?" Na fada ina jijjiga ta, ajiye wata jakar takarda yayi ya ce min. "Kawo min ita." A hankali na mika mishi ita har hannunmu yana gogan juna. Da sauri na janye nawa hannun, shi kuma ya cigaba da kallona. Yana me kallon inda kwanon abincina yake, na bude zan ci ta fara rigima. "Ki ajiye abincin anjima sai ki ci ga wannan ki ci." Ya nuna min jakar da idanunshi. Sai gashi na rikice baki daya, domin ina jin yadda yake bina da idanu, ban saba ba sai nake ganin kamar ba zan iya tsayawa da kafata ba. Jingina nayi na dauki jakar na bude, madara ce a kwalba sai gassashen nama, hadiye yawu nayi duk da ba laifi tunda muka zo ba laifi abincin mu yana da kyau, sannan a wadace muke samu. A hanya muka fuskanci matsala amma tunda muka zo abincinmu babu laifi. A hankali na fara bude takardar da ya nad'e namar, kamshinsa kawai yasa na hadiye yawu yafi sau goma. Na d'ago kai naga yana hidimar baby da sauri na fara ci, ban sani ba ko yana kallona domin ganin nama yasa ni jin duk wata yunwar da nake ji na tsawon watanni bakwai ta dawo min sabo fil, "ki ci a hankali." D'ago kai nayi naga Babyn yake wasa da ita, goge bakina nayi na cigaba da cin namar, har na koshi. "Zan tafi!" "Allah ya saka da alkhairi." Na faɗa ina sunkuyar da kai, koda su Addah suka dawo a gajiye, idanunta ya sauka akan jakar takardan, dauka tayi zata buɗe Ummi ta fauce. "Dalla bani." Dama kuma na rage musu ne, ganin kowannensu ya samu ba zai bawa dan uwanshi ba. Yasa na amsa. "Idan kuka yi hakuri na ku ne, idan kun yi faɗa ma naku ne." Na fada ina ciro musu na mika musu, faucewa suka yi suna jan tsaki.
"Wani dan iskan kika samu ya kawo miki?" Inji Addah, ban bata amsa ba na gyara mana kwanciyarmu da Baby. Washi gari da na shiga gidan aiki naga Matarshi sai hawa da sauka take, har na gama aiki zan fita ya fito dauke da Yarshi. Murmushi yayi min na sunkuyar da kaina, na fita da sauri.
A harabar gidan naga alamar zasu fita ne, haka yasa na bar gidan domin yau bata min kakale-kakale ba, asalima kamar sauri suke. Ina dawowa nayiwa baby wanka. Sannan muka kwanta bayan mun karya.
12:30pm,
Ji nayi kamar ana tsaye a kaina a hankali na bude idona, ya sauka akanshi yana bakin gadon Ummi yana latsa wayarshi, da dan sauri na tashi zaune ina kallonshi. "Yau Baby bata yi rikici ba kenan?" Ya ajiye min irin jakar jiya.
"Wai ya sunan Babyn?" Tiririn da nake ji na kamshi yasa ni rikicewa domin yunwa nake ji, kuma sai karfe biyu za a kawo mana abinci. "Ban mata suna ba, baby muke kiranta."
"Ya sunan Mamanta?" D'ago kai nayi ina kallon shi, kawai sai ya cika min idanu. Sunkuyar da kai nayi ina faɗin. " Zulaiha!" Na zabi na fadi haka ne domin ya min kwarjini. "Ok bani ita!" A hankali na mika mishi ita, kamar mai tunani sai kuma ya ce min. "Hmmm! Ba zan saka mata sunan Uwarta ba, domin zata iya gadon halinta."
"Ka saka mata sunan Addah." "Ita criminal ce zata tashi da shaidancinta."
"Tow ka saka mata sunan Mamana!" "Ya sunan yake?" "Aminatu!" Murmushi yayi ya ce "sunan Kakata ce da tasoni sama da kanta." Ya fada yana shafa kan Babyn yana me mata huduba. "Maman Aminatu!" Murmushi nayi, tare da Mikewa zan karbeta ya ce min. "Ci abinci" ba musu na zauna na ci grill fish da chips a gefenshi. Sai da na gama ci ya mike, ya ajiye min yarinyar.
Ya tafi, lokacin sallah yayi na mike na wuce ban daki nayi alola sannan.na dawo nayi sallah, sannan muka kara kwanciyarmu, domin kifin akwai maiko. A hankali wata irin shakuwa da bansan daga inda ya samo asali ba, ta shiga tskanina da Yallabai Yazid, da farko sau daya yake zuwa, daga baya ya koma yana zuwa sau biyu. Da rana da kuma Yamma, a hankali idan yazo shirya Baby Aminatu, Addah kamar zata rufe ni da duka da taji sunan har da Min Allah ya isa, bata yafe ba don na saka sunan Mamana.
Da yamma idan ya zo ɗaukarmu yake muna zaga cikin garin, gonarshi da lambun shi har da gidan dabbobin shi. Yau ma haka ya saka ni a gaba, bayan ya kawo min wata doguwar riga da mayafinta. Muka shiga wani yanki ta Cikin gonar, mun yi dogon tafiya kafin ya kawo mu wani wuri a ƙarƙashin ƙasa, ya ce min. "Kin ga wannan wuraren? Akwai kofar da xasu fitar da ke har wani kauye, daga nan zaki wuce bodar Nijeriya da nijar ne da yake dole kaina, mu nan muna yankin River Benin ne.
"Ban gane ba?" Zama yayi yana kara murmushi ya buɗe kofar ya shiga shi da Babyn sannan ya mika min hannu na rike shi na sauko. "Kina da saurayi?" "Na'am?" Na ce mishi, ina kallon shi. Murmushi yayi min sannan muka cigaba da tafiya.