Sashe 107
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Sai da ya rakata sannan ya fito ta ce mishi. "Sau daya tak ake samun dama, idan aka rasa har abada an rasa kenan, kayi amfani da damar da kake da ita ka sakata farin ciki da nuna mata zaka iya kome dominta, idan kayi haka tabbas zaka samu kyakkyawar dangantaka daga gare ta." Daga haka ta wuce dakinta. Ya kai minti biyar a tsaye kafin ya wuce ya samu suna hira a falon. Zaytoona tana waya da Mamanta. Wucewa sama zai yi Hajiya ta ce mishi. "Ya Zahra da jiki?" "Lafiya lau!" Amaan da yake kwance a wurin ya ce mishi. "Majid da sauki sosai?"
"Eh da sauki kai! Don zasu iya sallamarta ma an jima, ya wuce, tashi Amaan yayi ya bi bayanshi, ya same shi cikin duhun dakin,yana kwance. Kunna wutar dakin yayi yana faɗin."Abdul Majid!" Juyawa yayi yana kallon shi. Kafin ya lumshe idanunshi. "Me yasa ka dawo daga asibitin?" "Saurayinta yana tare da ita!" "Tow amma ai."
"Kasan dai babu kyau nima a cikin nima? Sannan." Yadda Amaan ya kafe shi da idanun yasa yin shi shiru, yana nazarin abin da zai fada. "Suna son junansu har haka ne?"
"Yadda yake sonta bana jin a raina zan iya mata wannan son, yadda yake kaf -kaf da ita bana tunanin ina da wannan jimirin yin haka. Yarinyar tana bukatar nutsuwa da kulawa ina tsoron kada na kawo ta wannan gidan ta kuma samun matsala da kowa.
Balle ma zai yi wuya ta amshi tayi na, nasan nayi kuskure amma ba zata amshi soyayya ta ba."
"Wani irin soyayya yake mata?" "Kulawa bata lokaci, haka kawai zai iya barin abin da yake ya taso ya zo domin ta, duk yadda naso na samu kusanci da ita, ya kanenayeta bata iya kwakkwaran motsi ba tare da ya ce mata me kike so bs."
"Ni kuwa sai nake ganin wannan damar na ka ne malam sikagon, idan aka sallameta ka bata hutu na wata guda,sauran kuma sai muga yadda zamu yi." "Hmmmm ba xaka gane ba ne." "Zan gane mana!" Ya faɗa yana kallon Majid din, shigowar Aryan ya saka su a gaba yana basu labarin yadda kome yake tafiya, don haka da dare suka shirya zasu shiga Asibitin. Domin karfafa mishi gwiwa. Abin gwanin dad'i.
Haka aka yi da zasu kai abincin dare, Majid jikinshi a sabule suka isa, har dakin.
Muna cin abinci da Baraka Amirah tana cinyarshi, suka shigo kallonsu yayi sau daya ya dauke kai. "Assalamu alaikum! Sannunku!" "Yawwa sannunku Hamma Amaan, ya jikinka?" "Ai kin bari na zauna sai ki tambaye ni."
"Afwan!" Suka zauna a kafet, sama sama suka gaisa da Yazid, da ya ga ana hira sama sama. Ya ce min. "Little bird bari na tafi, ina ga wani sati ko ta sama zan zo ki shirya zaki tafi kamaru."
"Tow Allah ya kai mu!" Har zai tafi sai kuma ya dawo ya zo har inda nake ya ɗan duka kaɗan ya sumbaci goshina."zan yi kewarki."
"Na gode sosai!" Na fada ina murmushi. "Abhna nifa!" Ta nuna mishi goshinta. "Hmm!" Itama ya bata kiss din, mikewa nayi na bi bayanshi. Har waje inda security din shi suke jiran shi. Hannuna ya rike. "Shi Chairman dinkun nan, ya fa takura min."
"Kayi hakuri!"
"Tow nayi, amma gaskiya ya dame ni."
"Ayi hakuri!"
"Matata idan muka je Kamaru zan roke su a bani aurenki, kin ji."
"Hm" na ce.
"Me yasa?"
"A'a ina son koda xan yi aure, na yi kokarin niman Maman Amirah, domin ta nima mata Babanta. Ban san me zai faru ba amma tabbas yana da kyau na nima mata Babanta."
"Ni ban isa ba ne sai an nima mata wani abu?" Murmushi nayi tare da faɗin. "Ka isa har ka zarta." Dakyar muka yi sallama na koma dakin na zauna, ina shiga dakin na samu ana ta hira, zama nayi a bakin gado. "Ga abinci Zahra."
"Na koshi wallahi, Sultan ya mana odar abinci."
"Hm! Ba zata ci ba, tunda ba shi ne ya ce ta ci ba." Kallon shi nayi cikin takaici nace mishi. "kamar ya?" "Ku tashi mu tafi!" "Wani irin mu tashi mu tafi, ke Barakatu ko? Ke da Amirah kuzo ku raka ni" Amaan ya kwashe su har da Aryan,suna fita na mike ina gyara dakin, ban san dalilin da yasa nake jin a matukar takure ba, idan na juya sai naga idanunshi a kaina, daga karshe sai da na juya kawai na ganshi a bayana, a hankali na ja da baya ina son tambayarshi. "Lafiya?"
"Lau!" Ya faɗa yana kallon yadda nake ja da baya. "Ni babu abinda xan miki, kawai ina mamakin yadda. Kike kasa fahimtar."
Kura mishi idanu nayi nace mishi. "Don Allah ka matsa min, bana son haka."na faɗa tare da matsawa zan bar inda yake. Fisgo ni yayi ta baya tare da k'amk'ame ni.
"Please! Calm down!" Ya faɗa, a karo na biyu da naji sautin bugun zuciyar shi, wanda ya tunomin da wancan daren da ya taimaka min a cikin duhu, yana wani irin bugawa. "Ki saurare ni kin ji yadda yake bugawa." Hawaye ne ya shiga zuba a idanuna. "Na sha wahalar nimanki, na san ban kyauta ba,.amma tabbas ban yi haka don ki tozarta ba, ban yi haka don na bata miki lokaci ba, na nime miki sama da kasa ban ganki ba, na yi ƙoƙarin bin kauyika da sansanonin gudun hijira a nima min ke amma babu me kama da ke. Ni nasan da na juya ko sau daya ne na ga fuskarki tabbas da zaki zama abin tunawa a rayuwata. Sai dai kash ban yi haka ba a gado daya mun kwanta ban duba wacece ba."
A hankali ya kai hannunshi inda ya soka min wuka, "Ki bani damar kankare abubuwa a ranki a cikin shi har da wannan ciwon, idan kika duba lamarina zan kasance adali a tare dake." Daga haka ya sake ni, ya fita daga dakin ni kuma na koma bakin gado na zauna ina me sakin kuka a hankali, ina jin bugun zuciyar a kunnena da zuciyata.
"Me yasa? Me yasa sai yanzu ? Me yasa sai yanzu xan shiga yakin masoya." Na fada ina kuka, Yazid ya faɗa min shi kuma ya gaya min me yasa, haka ya fita ya bar ni na yi kuka har na godewa Allah, bakiɗaya sai naji kamar na tsani kaina, koda su Baraka suka dawo, ina kwance suka zo da kayan ciye-ciye, ban kalli abin da suka zo da su
ba da suka dame ni nace musu su kwanta ko su koma gida.
Yadda na ga rana haka na ga dare, na kasa barci na kasa motsin kirki, karshe tashi nayi na shiga ban daki nayi Alola, ina ga bani da abinda ya wuce na gayawa Allah matsalata. Kafin wani lokaci na ji sauƙin kome kamar babu abinda ya addabi zuciyata.
Washe gari.
Nayi ta barci har yazo ya duba ni, yadda yaki yarda ya kalle ni haka nima naki yarda na kalle shi haka shima sai gashi mun zama surukan juna, ganin haka yasa ni mikewa na fara tattara kayana,ina haɗawa Barakatu ta shigo tana faɗin. "Tante da kanki zauna na hada kayan." Haka ta haɗa kayan muka fito, dake ta kai Amirah makaranta.