Sashe 57
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Haka yanayin ya cigaba da tafiya, Ummi tana zuwa kuma ina jin labarin yadda suke zaune da halin Addah, murmushi nayi domin Allah ya tsamo ni daga cikin masifar Addah babu dalilin komawa cikinshi, matar Yallabai Yazid ma ta gama jarabararta ta kyale ni, har cewa take ya ajiye karuwa yana abin da yaso da ni, kuma Ni tsakani na da shi bai tab'a min kallon wani abu ba, asalima y'ata yake dauka, idan tana hannuna ya amshe ta, ko ma bata hannuna zai dauketa. A iya zaman da nayi da shi ko da wasa bai tab'a yunkurin yi min wani abu ba, idan akwai abinda yake son ya gani shine na zama mai tsayuwa da kafarta, wannan shi ne mutum na farko da ya tsaya min, sannan zuwa yanzu na san yana rike dasu Addah ne domin ni, ba don haka ba da sun bar mishi yankinshi,. Tow nice karfin zamansu.
Ko ranar da ta b'ata min rai shi ya ce min. "Ke ni zan Kore su, na gaji da ganin suna kuntata miki. Gara su baki wuri ki huta." Girgiza masa kai nayi ina faɗin. "Ko daya, kawai nafi son na gansu a tare dani. Ko babu komai nasan wata rana zasu min adalci." Wato idan rana ta fito tafin hannun bai isa kare ta ba, wannan shine adadin abinda zan fada domin Addah tun kafin a haife ni take adawa da mahaifiyata, da aka haife ni kuma dole ta hakura da abin da take mata, sai dai babban abunda yake min ciwo mahaifiyata da ban san dalilin da yasa ta manta dani ba, nasan dai duk inda take zata so da ina tare da ita,
A hankali kome yake tafiya tare da zama tarihi, kusan shekara daya da rabi kenan, da barin mu Nijeriya, sannan muna wannan ma'aikatar sarrafa maganin Yazid, zuwa yanzu na kara fahimtar abin da suke aikatawa, musamman da ya fahimci yadda nake da baiwar ilimi, haka yake sakani duk wani lissafin Kudi ko wani abu, a gefe guda kuwa Babyna tana yawo ko ina, domin tana tafiya dagwai-dagwai abin ta, duk wanda ya ganta zai dauka ta shekara biyu, nan kuwa shekara daya ne da yan watannin. Yarinyar Kyakyawar gaske ce, don ma ina boyeta, idan na kalleta sai naga bata kama da Zuzu,babu abinda zaka gani kace tana kama da Zuzu sai kwayar idonta.
---
Kallon Addah yayi cikin fushi da b'acin rai ya ce mata. "Na gaya miki, zata tafi karatu , iya abinda nazo gaya miki kenan ke kuma da yarki na shirya yadda zaku tafi sansanin gudun hijira da yake Agadaz OIM,."
Kura mishi ido daya tayi sannan ta ce mishi. "Na gaya maka ka saye ta, domin matukar ina raye zan amshi kudin wani." Shiru yayi yana mamakin taurin kan Addah, kafin ya ce mata. "In sha Allah ba zaku tab'a haduwa ba." Sannan ya juya ya bar gidan,
Ina zaune na ga ya shigo har dakin ina aiki da laptop. Rike hannuna yayi yana faɗin. "Nasan wata rana zaki tambaye ni dalilin da yasa na kawo ku nan." Ya fada yana hada kayanmu. "Lafiya?" Cusa kayan yayi ya tattara kome nawa, "Idan muna raye ki ajiye a ranki zan neme ki." Ya ciro wata sarkar da yake wuyarshi ya saka min.
Sai da muka bar yankin gaba daya yakaini wannan underground tunnels din. "Me yasa zan tafi ban yi sallama da dangina ba." "Ka
Min bayani ina zan tafi." Haka ya cigaba da tafiya har na tsawon awa biyu, sannan muka fito bakin tunnels din, ya kai ni har zuwa inda wata mota take ya ce. "Aseem ka kaita iyakar inda ka ajiye su Reshmah, zan zo idan damar haka ta samu, motar Ansar zai kaita har inda zata zauna. Ka fahimta ko?"
"Eh Sultan na fahimta."
Haka ya saka baby a motar, sannan ya janyo ni, ya rungume ni. "Ina son na gaya miki a kurarren lokaci, ina kaunarki." Ya sumbaci goshina sannan ya saka ni cikin motar. "A'a Yazid!" Ban san me ya min ba, sai dai na zube a jikinshi ban kuma sanin kome ba, haka ya gyara min kwanciya. "Na gode Aseem." Daga haka ya koma cikin tunnels din.
Tsawon awa biyar ina sume, sai da muka isa iyakar da yace da shi. yasa shi yayyafa min ruwa, ina farkawa na zubawa inda muke ido. "Sannu, ga motar Ansar nan."
"Don Allah ina yallabai Yazid?"
"Kiyi hakuri nasan shi namijin duniya ne, yadda ya ƙare iyalinshi haka ya ƙare ki, don haka kiyi karatu yadda zai yi alfahari dake. Ki kula da Amirah sugrah."haka yake kiran Baby. Kuka nasaka ya kwashe kayan mu ya saka a cikin motar Ansar ɗin., daga nan ya tada motar muka bar wurin, sai da muka kwana muka wuni, kafin muka isa Marad'i.
A wata unguwar masu hali ya kai mu, ya kai ni har cikin gidan. Babu abinda babu a cikin gidan, sannan ya mika min wata jaka. "Gashi wannan duk wani abun da kike bukata yana cikin nan, sannan ina kara baki hakuri da ta'aziyar rashin da kuka kuma yi, domin a lokacin da kuka iso labari ya zo min Yallabai Yazid da yan uwanki, sun rasu." Ji nayi kamar duniyar tana juya min, daga nan ban kuma sanin kome ba, na zube a wurin, kwana biyu ina kwance a gadon asibiti babu kowa sai nurse da likitocin da suke kaiwa da komowa, sai wata mata da take dauke da Baby. Kunsan yadda nake cikin tashin hankali? Babu Addah babu Ummi, babu kowa sai Allah sai baby!"
"Sannu Allah ya baki lafiya." Kallonta nayi na lumshe idanuwana, ina son kara haska fuskarshi, a wannan yanayin ya ce min yana sona. A wannan ranar kome ya kara sauyawa. Wata kaddara wata rayuwa, wata duniyar, kome ya tafi kamar bai faru ba. Da taimakon Matar nan nayi wanka na gyara jikina nazo na sauke ibadar da yake kaina. Ruwan zafi ta haɗa min na sha, ina kallon Baby da tayi barci, turo kofar aka yi likita ne da nurse. Suka gama duba ni, zasu fita nace musu. "Ku sallame ni " "Jikinki da saura." Inji likitan, "A'a zan karasa a gida don Allah ku sallame ni." Haka suka bani sallame, muka fito Matar nan ita ta nimo mana abin hawa muka nufi gida, har cikin gidan muka shiga. A daya daga cikin kujerun falorn na kwanta, "Maman Amirah sugrah, zan turo yarinyata, tazo ku kwana domin ba zan barku ku kadai ba." Gyada mata kai nayi, ta fita can sai gata da wasu yan mata uku. "Assalamu alaikum!". "wa'alaikimus Salam!" Na amsa muryarta a ciki ciki, "Maman Amirah sugrah, ga Barakatu zata kwana anan, sauran sun zo miki ya jiki ne."
"Ayya na gode." Na fada a hankali, "muna BQ dinki ne."
"A cikin gidan nan kuke?" Gyada min kai tayi. Sallamar wani magidanci ne yasa suka mike tare da amsa mishi, ya shigo muka gaisa. "Shine maigidana, yana kula da gidan nan." "Na gode!" Na fada. "Ya Jikinki?"
"Da sauki Baba na gode sosai." Daga haka suka watse aka bar ni da Barakatu, ina kwance kamar ruwa ya cinye ni. A hankali na mike na nufi hanyar kitchen, nayi ta bincike, akwai kome babu abinda Yazid bai saka min ba, wasu kayan abincin zasu shekara uku hudu, zama nayi na fashe da kuka, sai da nayi me isata. Duk abincin da ya dace gasu nan, freezer biyu ne a kitchen din, da na bude daya cike yake da nama na kaza da na saniya, ga kifi da turkey. Taliya na dauka da kayan miya Barakatu ta shigo taga ina ciro kayan abincin, ta tayani na kunna gas, muka yi jallof da busashen kifi, ita ta karasa na koma daki nayi sallar Magariba, nayiwa baby wanka, ban fito ba sai bayan Isha. Abincin ta kwashe min, na ce ta zuba ta ci, ni kadan na saka saboda Baby ne ma, haka ta dauki nata zata fita nace ta kara musu, idan ta je kada ta damu zan iya kwana. Sai da safe ta min na rufe gidan Baby na gama cin abincin ta, na wanke mata baki da jiki, muka shige daki. Kwanciyarta tayi jikina, ina shafa bayanta. Har barci ya dauke ta, baki daya rayuwata nake tunawa tun daga ranar da narasa mahaifiyata, har zuwa mutuwar Baffa'm ya dawo min haka nayi kuka har na godewa Allah, tashi nayi nasha magani na hada da alola nayi sallar nafilla, sannan na jima ina addu'a da rokon sauki a cikin al'amarina... A hankali na kwanta barci ya dauke ni, haka na kwana cikin mafarkai marasa kai da fasali..