Sashe 108
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
** Addah dai sun isa najeriya lafiya, amma babban burinta bai wuce yadda zata samu damar ganin ko wayar da zata na kiran Zahrah ba. Haka yasa koda ta iso jalingo bata yi wani farinciki na gata a cikin danginta ba, kawai abin da ta fara yi binciken me Zahra take musu me ake kawo.musu daga Zahra. Shi kuwa Babangida zuciya daya yake bata labarin, jin yadda Babangida yake bata labarin yasa Ummi ta ce mishi. " Da dai kayi shiru, domin duk abin da xaka faɗa ba zai taba burge Addah ba." "Zaki min rashin mutuncin da kika saba ko? Haka ta saka ni a gaba da rashin kunya da rashin mutunci!" Yadda tayi ta fadar abin da Ummi take mata yasa Babangida hawa kan Ummi da fada, kamar zai dake ta. "Indai Addah da kanka zaka bukaci ta bar gidanka. Ita tauraruwa mai wutsiya ce." Bai saurare ta ba, don gani yake kamar sharri takewa Addah. ** Rayuwa dai ta cigaba da tafiya kamar yadda muke hasashe, ina kuma tsaka mai wuya, domin kuwa Yazid baya sati daya biyu zai zo Majid kuma ya kankane min rayuwa kowannensu lallai ala tilas sai na bayyana ina sonshi. Na Majid ma yafi na kowa yawa, domin hatta abokan aikina ya hana ni magana dasu Hatta Dan Larai sai da ya kira shi ya mishi kashedin kada ya kuma ganin shi da ni, shi kuma Ɗan Larai ya zata saransa na kai, sai gashi..... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 8130269641 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB258 Sai gashi ya zo kaina yana min tijara, har fa da kirana munafuka don naga ya fini samun damar zama a kamfanin idan na kara mishi munafinci sai mub daku. "Da wa zamu daku?" "Da ni mana." Ya faɗa yana murguda min baki, akwai yanayin da idan fitina ta taso gara ka nime tsari da shi, yadda ya tsaya yana min tijara yasa ban kula shi ba, nayi kasa da kaina har ya gama ya bar kaina, duk abin da muke Majid yana kallonmu, sai bayan mun tafi sallah na gan shi da Dan Larai. Da farko yadda yake girgiza ya sani fahimtar rigima yake yi da dan larai amma daga yadda naga ya sha mur tuni dan larai ya nutsu yana bada hakuri. Bayan mun koma ya biyo ni inda nake ya tsaya a kaina, ban d'ago kai ba kuma ban damu da lallai nayi magana ba. "Kina da lokaci ne mu fita" "ina da bako daga Algers!" Daga haka na ja bakina shiru. "Wai shi bai da mafada ne?" Ban ce mishi cikanka ba, domin bana son magana. "Gaskiya ya kamata ki fahimci me kike ciki?" "Saboda a yanzu ban fahimci me nake ciki ba ko? Ko qkwai wani abu da ake son na fahimta ne ban sani ba?" Na tambaye shi idanuna akan shi. "Baki bani amsar bukatatta a gare ki ba?" Kashe laptop din da nayi tare da ɗaukar wayata na nufi hanyar waje. "Ba sai na baka amsar ba, don tuni zuciyata tayi, nisan zangon akan wanda kansa." Fadar haka yasa gabana faɗuwa, har sai da ya tambaye ni. "Lafiya kuwa?" "Lau!" Na faɗa ina jin wani irin kuka kamar xan yi shi amma ina zuciyata tayi wani irin narkewa, Shiru yayi kamar ya bini, amma ina na shiga elevator, daga kamfani makarantarsu Amirah na wuce, ina zuwa suna tashi, na tsaya a jikin motana, a wurin yau nake saka ran fitowarta har aka fara watsewa, haka kawai sai naji kamar na fashe da kuka, amma ina a hankali sai naji zuciyata kamar an karfafa mata, ina tsaye har mallamai suka fito a lokacin ne na nufe su. "Amirah bata fito ba, ban ganta ba?" "Kamar Ya? Ai kuwa tazo yau." Tashin hankali wacce ba a sa mata rana, hawaye ne ya fara ƙoƙarin kwace min, nan aka shiga bincike tun karfe uku har aka yi la'asar, aka kira yan sanda babu Amirah. Suka saka ni kiran gida ko an dauke ta babu wanda ban kira ba, hatta Amaan na.kira kafin wani lokaci duk sun hadu a kaina. A hankali duk sunzo babu wani wanda bai zo ba, amma ina Babu Amirah babu me kama da ita, nayi kuka har na godewa Allah. Idan ka kalle ni zaka zata jinya nayi, domin nayi kuka har na godewa Allah na, bana iya dogon magana, bakiɗaya tausayin kaina nake ji, har zuwa dare babu labarin ko za a iya turo sakon ana son ba biya biya wani abu a karbeta. Dare nayi aka ce mu koma gida, amma ina kasa mikewa nayi, ya d'ago ni ina kuka. "Don Allah ka nimo min ita!" "In sha Allah" Haka ya ɗauke ni muka nufi gida, a ranar kwana nayi a zaune, washi gari da safe kuwa ina mikewa na yanki jiki na faɗi. Haka aka kai ni asibiti, lokacin da na farka na ga kowa kaina babu Amirah. "Ina Aminatu?" "Kiyi hakuri ana kan nimanta." Ji nayi dakin yana juya min. Suma nayi ta musu ga jini na da yayi azabar hawa, haka yasa naji kamar zan mutu. A cikin kwana biyu, na zama kamar mahaukaciya. Da na fahimci suma da kuka ba zai min ba, wurin asuba na fita daga asibitin, na tafi makarantar na zauna, ina kallon kofar makarantar. Haka yasa har gari ya waye kowa sai gani na yake. "Fadima me yasa kike haka ne?" D'ago kai nayi ina faɗin. "ban sani ba, ko rayuwata ce tazo karshe amma babu inda zani sai naga Yarinyata." "Fadima tashi." Inji Aryan. "Babu inda zaki Aryan, yarinyata ina zan je? Ba zan iya tafiya ba." Na fada ina share hawaye, dakyar ya d'aga ni daidai zuwan Majid. "Me yasa baki jin magana? Me yasa ba zaki sakawa zuciyarki sallama ba." Durkusawa nayi kasa, ina tsuguno har ya gaji ganin zan tara musu mutane, yasa shi d'aga cak, ya saka ni a mota. "Kiyi hakuri da rayuwa." Ya faɗa min kasar kunnena. Yadda nake ihu tare da ƙoƙarin kwace kaina. "Ka kyale ni, ku nimo min Yarinyata wayyo Allah Aminatu." Cusa ni cikin motar yayi, ya ja muka bar makarantar. Ba karamin fama na sha ba, muna isa asibitin har lokacin babu wani labarin. Karfe biyu daidai na rana, sai ga Yazid. Lokacin da ya iso yaji labarin, makarantar ya nufa anan, a kasa da awa biyu da rabi sai ga labari ya fito. Ina kwance ya shigo dakin, ina ganin shi na fashe da kuka. "Ya isa haka." Yana zuwa na tashi, daura kaina nayi a kafadarshi. "Wacece kika tura makarantar ta dauke ta?" Hawaye ne ya zubo min ina faɗin. "waye xan tura? Ban tura kowa ba." Shafa bayana yayi. "Ki kwantar da hankalinki." Kuka nake tare da jin kirjina yana zafi. "Ina ji kamar zan mutu." "Ba zaki mutu ba." Ya faɗa yana matsa hannuna, "me yasa aka dauke Amirah?" "Saboda wacce take da bukatar ta ne ta dauke ta. Ya kamata ki cire wadannan mutanen a rayuwarki, domin basu kaunarki kuma basu son wani abu da zasu saka miki don farinciki sai bakinciki." Ya faɗa, "Yazid" "meye? Iya gaskiya kike so na gaya miki ko me?" Shigowar Majid yasa shi dauke kai. "Zahrah an samu wacce ta dauke ta." Da sauri na ce mishi. "Wacece?" Nuna min hoton yayi a kan tap din shi. "Ji nayi kamar xan fado, ban san lokacin da numfashina yake hawa da sauka kamar me asthma. Allura ya dauka ya ja ruwan tare da haɗawa da sauri ya danna min, kowa nayi xan fadi Yazid ya tare ni. "Sam baka da lissafi, gaka kamar me tausayi da hankali taya zaka nuna mata irin wannan abin ?" "Malam babu ruwanka da ni." Tsaki Yazid yayi yana faɗin. "A wannan lokacin kowa ya zama mahaukacin karfi da yaji, ita yarinyar da aka dauka kasan wace ce ta dauke ta?" Kallon Yazid yayi da alamun son karin bayani. "tsuk" ya ja tsaki sannan ya mike ya kwantar da Zahrah. Yana faɗin. "Duk son gwaninta, ba ta haka zaka gaya mata ba." "Kada ka gaya min magana!" Inji Majid, "A'a gaskiya xan gaya maka, daga da su baku da banbanci. Na san abin da nake yi, tun da naso na samu Uwar yarinyar ce ta dauke ta, amma ba ta hanyar da ya dace ba kana da abin da zaka iya ne? Wannan matsalar Zahra ce zata iya magance shi, mu yan taya ta ne ba yan kashe mata gwiwa ba." Daga haka ya saka kai ya fita, haka suka cigaba da bin duk inda zasu samu Amirah, sai dare aka samu wani suitcase a kofar asibiti. Aka rubuta a saman akwatin. Zuwa ga Zahra ke daya zaki bude akwatin. Hukumar asibitin da yan sanda ne suna taru. Babu wanda yayi yunkurin budewa,Har masu bincikar bom sai da aka kawo, ina zaune Yazid ta shigo dakin. Cire min ruwan yayi, sannan ya mika min hijab muka fita, yana rike da hannuna. Don tun da na farka bana hmm-hmm bana yi, ina cikin d'imuwa. Gaban jakar ya ajiye ni, ina gani na fahimci sakon Zuzu ce. Jikina ne ya dauki rawa, na kalle shi kamar xan yi kuka na girgiza mishi kai. "Babu abinda zai faru." Inji Majid, sai na kai hannuna zan maida baya, daga karshe dukkansu biyu suka rike hannuna na bude jakar, Amirah ce kwance a cikin shi, rungume da Bunny Bunny, da sauri na d'ago ta tana barci me nauyi. A jikin rigar ta aka saka. *Am sorry na bata maganin barci ne, amma na gode Yarinya ta girma. Yawwa akwai daya suitcase din a kofar gidanki* ciro yarinyar nayi Nurse suka amsheta. *Don Allah kada ki ni footage dina, idan kika yi haka zan ji babu dad'i. Kuma zan amshe Y'ata wallahi" " A kashe case din anan." Dariya Yazid yayi yana faɗin. "Tow kun ji me kara ta janye." "Amma Zahra criminal case ne." Inji Majid, "And so what? Duk abinda nawa yayi min ina iya rufa masa asiri, koda kuwa tawa rayuwar yake bukata, ina hakura na bashi akwai wani abu ne?" Wannan maganar ya mishi zafi, a binka da tsohon soja tuni ya daka zuciya ya bar wurin. Yazid dariya abin ya bashi, haka ya sa shi riko