Sashe 113
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Sake wayar yayi kamar wani gaula, ya bita da idanun zata fita daga airport din, da wani irin azama yayi kanta da sassarfa. "Zulaihah!" Ya fada da dan ƙarfi. Juyawa tayi tana kallonshi, jikinta ne ya dauki rawa. Ta rufe bakinta tana jin wani irin hawaye na zuba mata, karasowa yayi yana haki, abin ka da jiki duk madara. "Ina kika shiga?" Kallon shi tayi tana ƙara tuna abin da ya kawota, juyawa tayi ta cigaba da tafiyarta. "Zuzu!" Kamar zata tsaya sai kuma ta cigaba da tafiyarta. Biyo ta yayi tare da riko hannunta, cikin wani irin fushi ta fisge hannunshi. "Kada ka sake tab'a ni, na gaya maka."
"Ina abin da kika haifa?" Ya tambaye ta, cikin wani irin yanayi. "Ka bani ajiyar ciki ne? Malam ban sanka ba, bani hanya na wuce."
"Ki saurare ni!"
"Sai kayi kuma!"
Fitar da ya fasa kenan, kallonta yayi gata da wani irin shiga kamar irin yan iskan yan matan nan, hujin kunnenta kusan biyar. Ga hanci, wuyarta kuwa wani dan iskar abin wuya ne baki. "Muje na kai ki Taraba."
"Ka ga nayi maka kama da yarinyar arziki ne?"
"Haka na same ta, a shekarun baya nasan haka nasota, haka na raba dare da ita muka raya dareraki masu yawan gaske. Nasan kina sona!"
"Karya ne, bana sonka kada ka sake damuna."
Rungume ta yayi ta baya, "kiyi hakuri Uwar Yarana." Wani irin kuka ne ya kwace mata. Riko hannunta yayi suka tafi wurin Motarshi, bude mata aka yi ya sakata. Ta cigaba da kuka wiwi. Haka yayi ta rarrashinta, a ranar tafiyar shi zuwa China ne amma haka ya hakura, ya nufi Taraba da ita. Lokacin da suka isa ya samu gidan ana ta rikici. Tsakanin Addah da Matan Babangida wani irin kunya ya rufe Zuzu.
"Yaushe zaki girma? Yaushe zaki daina abin Kunya?" Ta fada da karfi, rikota yayi yana faɗin. " Ki kula Soulmate!" Cikin wani irin kuka ta ce. "Gaya min meye addah take so?" Ta janyo jakarta ta tura mishi. "Aiki na ne da nayi da jikina da rayuwata." Cikin wani irin kuka ta ce. "Sayar dani kika yi fa? Sayar da yar cikinki, saboda hassada da kyashin. Yau ga Zahra tana cikin farinciki da dangin Mamanta. Zahra tana rike da yar da kika raba ni da ita, ina son naga Y'ata abu ya gagara." Ta durkusa a wurin tana kuka. "Zamana a U.s ban da wulakantacen rayuwa me nayi? Nice rawa a gidan rawa tsirara, Ni ce gamsar da wani tsoho...."
"Kome kika yi a duniya, ina sonki a haka ya isa haka. Ina sonki a haka ko da kuwa kece Magajiyar karuwai, Lamido yana sonki yana kallonki a matsayin Uwar Aamirah!" Indai Zahra da take rike da Amirah ita ce Zahrah da take fada....
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB261
"Zahra ta Nijar ce Yarinyar take wurinta?" Ya kuma tambayarta domin ya tabbatar. Cikin kuka ta gyada mishi kai, cikin shashekar kuka ta ce masa. "Taya zaka ji idan mahaifiyarka ta kasance kamar Addah ya zaka ji? Tsananin son kudi da abin duniya ya zaka ji?" Cikin wani irin kuka ta zauna dabas ta ce mishi. "Ita ta haife ni, ita tace na bi namiji, na kwana da maza na kawo mata kudi a hakan na hadu da kai." Takasa tsayar da kukanta tana kallonshi. "Still kana nan akan bakanka, kana son tarayya da Ni haka?" Murmusa mata yayi yana faɗin. "Ina sonki!" "Tow mutuwa xan yi!? Mutuwa zan yi da bakincikinta da halin da nake ciki, wannan matar gara na mutu na bar mata duniyar bakiɗaya na gaji da halinta. Wayyo Allah na."
Ta fada tana ihu da birgima, hauka da rikici babu wanda bata yi ba, haka tayi ta rigima da rikici. "Idan kudi ne gashi nan tayi ta ci har ta mutu, amma ta bar min rayuwata na samu taslima na gaji na gaji da azabar Adda da masifarta."
Idanun Adda kirmisisi tana kyallara daya tana kallon Zuzu, ina ruwanta ta ce mata. "Ina ruwana jan kudina zan yi ke kika ji wurin" haka ta ja a kwatin duniya sabuwa, shi kuma Sk Lamido ya fitar da zuzu daga gidan da take ta Ajiyar zuciya.
A tow abun kunya bai dame Addah ba, a gidan ma hada husuma tayi tare da gulma wai Amaryar Babangida tana yin asiri tana zubawa a cikin abinci, ta gayawa Uwargidan, shine Ita uwar gidan ta samu Amaryar da fada, da habaici da Ummi ta ga haka ta fahimci Addah ce ta haɗa husumar shine ta saka su a gaba aka mai da magana anan suka kira Addah aka fara tone-tone. Kai Addah masifa ce.
•
Yazid ya tafi ya barni da kunci da b'acin rai. Wanda ya ja min na tsani kowa da kome. Hajiya tayi juyin duniyar nan na dawo jikinta amma naki, domin idan na tuna abin da ya faru sai naji bana son shiga harkar kowa kuma bana son ganin kowa.
Satinsu daya suka bar Marwa, ni kuma na bi Mamana Duola, a nan na ƙara samun wata irin nutsuwa da saukin warware wasu abubuwan. A hankali Mama take jana a jiki tare da nuna min kome, kai Uwa na da dadi. Wayyo Allah na wannan abin da take min ne yasa na ji lallai zuwa yanzu tafi ni gaskiya, kuma maganar zuzu xan kirata na bata yarta.
Haka na nimo Ya Babangida na kira shi. "Yaya Babangida ina son zuwa amma a Yola please!" "Tow in sha Allah." "Zan turo maka kudin abin hawa." "Kada ki damu, amma gaskiya Addah ta dame ni." "Hmmm!" Na fada ina jin wani irin zafi a raina, kafin na ce mishi. "Ba zaka gane wacece ita ba, sai gaba kaɗan." Na fada mishi sannan muka yi sallama. Tun daga lokacin na fara hada mata kayanta. Dakin Mama na shiga na zauna. "Ya dai Batul?" "Mama zan iya rabuwa da Amira kuwa?" "Me zai hana kuwa? Zaki iya mana." Haɗiye kukan da ya taso min nayi. "Ina son yarinyar domin na...." Sai na kasa fada mata kome, "kin shayar da ita ko?" Gyada kai nayi, "halin Babanku ya miki yawa." Ta fada tana miko min wasu dogayen riguna. "Duba sun miki kyau?" Tashi nayi ina gwadawa. "Ya miki kyau sosai, akwai takalmi da jaka a cikin wardrobe ki duba kalar da kike so." Haka na bude na dauki kalar da suka min na rufe mata, "me zaki kaiwa babangidan?" "Babu don xan tura mishi kuɗi" "Idan kina da wani abin bukata ki gaya min." "Babu Mama!" A cikin kwanaki goma, bayan na turawa yaya Babangida kudin ya tafi na nufi Nigeria.
•
A Yola kuwa Sk Lamido ya gayawa Mahaifiyarshi abin da ya faru, sai da tayi kuka don farinciki. Sannan ta tsaya mishi tsayin daka sai ya auri muradin shi, haka yan uwanshi kamar su tafi Cameroon su dauko Amirah kowa sonta yake.