Sashe 126
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Kwanan mu biyu muka koma Marwa domin itama ta ajiye aiki, tana yar business din nan na zamani, kuma ta ce bata ga wani abun da take nima ba don ta samu, ina yawan jin haka daga gare ta.
Sai da muka yi sati biyu me kyau kafin muka fara samun shi a waya, ranar da ya kira ni, nayi kuka kamar zan bi shi ta wayar. Daga nan kuma yayi ta bani baki, kafin nayi shiru. "Yawwa ko ke fa, ina baby na?" "Lafiyanta lau!" "Mace ce aka gaya miki?" "Naga kafi karkata akan namiji ne."
"Duk wanda Allah ya bani ina so." "Hm!" Ya faɗa yana cigaba da niman fitina ta, a sati biyun nan ji nake kamar nayi hauka. "yauwa yaushe xaka dawo?" "Da sauran lokaci."
"Gaskiya ka dawo na haihu a gabanka!"
"Naji zan zo ki haihu a gabana."
"Shi kenan zan zo na haihu a gabanki yayi!"ya faɗa yana murmushi. Sai da yaji alamar zan yi barci ya kashe wayar, haka washe gari ya kira sai da ta kai kullum zai kira yaji ya muke, Alhamdulillahi duk wata damuwata ta kau, Aryan yaƙe rike da kamfaninsu,wanda Hajiya take bayan shi tana nuna mishi kome, sannan ganin yadda yake tafiyar da kome yasa Hajiya kara tabbatar da cewa Aryan zai rike kamfanin sama da Majid, don haka masu kawo musu matsala, sai suka ja da baya. Sannan dayawansu gani suke kamar Majid yana bibiyarsu.
***
Ina Kamaru sai ga Zuzu da Ummi, sai da suka huta na zuba mata idanu ina shafa kan Amirah da take wasa da wayata. "Ina kika bar min Aaddah?" Murmushi tayi tana faɗin. "Tana gida, tare da masu kula da lafiyarta." "Allah sarki Aaddah na." "Tana nan tana fade-fade mun so zuwa da Munaisah Mahdi ya hanata zuwa." "Wai tun ba a shiga daga cikin ba ma kenan."
"Wallahi kuwa!" Kiranta muka yi na ce mata. "Munafika cewa kika yi ya cika tsawo siriri ne, ke kin hadu da samudawan maza ko?" Dariya ta saka tana faɗin. "Eh sai me?" "Sai na gaya miki kin zama munafuka."
"Eh tunda fir'auna zai danne ni a kasar wuta, Zahra zan dura miki Ashar." "Na nawa kuma, bayan kin zage ni sai ga Ummi da Zuzu da fatan lafiya suka baro ku?"
"Lau Zahrah sun zo ganin Baby ne!" Haka muka gaisa, sannan muka yi sallama. Ni kaina nasan naji dadin zuwansu satinsu biyu suka koma bayan zuzu ta ajiye min kayan da ta sayo min. Nayi ta murna, Hajiya ma satin da ya wuce ta aiko min da kayan Baby Jamilah ma haka, Aryan kudi yake turo min a cikin wata guda da tafiyarshi.
Amaan duk sati daya zai tura min kudi shima, duk da nasan bai da shi sosai amma yana kokari. A hankali muka share wata biyu, a lokacin cikina ya shiga wata bakwai, a lokacin ba karamar buƙatarshi nake ba. Haka zan ta kuka ina jin tsanar aikin soja, ban san yadda matan suke handling wasu damuwar ba, amma ni tabbas na shiga matsanancin damuwa.
Tun muna samun shi awaya, har ta kai bamu samunshi, sai ya kusan sati biyu bai kira ba, ko na kira baya shiga. Ashe a lokacin sun hau teku ne. Wannan abin ya d'aga min hankali domin ban saba ba, ban tab'a shiga irin wannan yanayin ba, sai gashi jini na hawa yaƙe kamar hauka, domin na saka damuwa a raina, dalilin da yasa Hajiya tazo ta ganni har take bani labarin abubuwan da suka faru a baya, sai naga babu amfanin d'aga hankalina domin itama kamar bata son zuwan shi amma babu yadda ta iya tunda abin ita suka fara tuntub'a.
Abin da ya faru kuwa kamar yadda ta gaya min, yan fashin teku ne suka sace wasu turawan biritania, sannan anyi anyi su sake su sun ki, karshe shugaban yan fashin ya ce matukar ana son ya sake mutanen dole a nemo Majid, domin Majid ya mishi sanadin da ba zai manta ba, sannan a yadda Hajiya ta faɗa ko a wurin aikin Majid yana da tarin makiya da masu jin haushinsa, haka yasa ni jin kamar abu zai fito daga cikina,. Nace mata."Hajiya me yasa kika bar shi ya tafi? Idan da na sani wallahi ba zan tab'a yarda ba, wannan ai ba inda zai je ba ne."
Muryar Mama ne ya katse min kukan da zan yi. "Tow ayu, so miji." Tura baki nayi ina faɗin. "fisabilillahi an san mutanen nan ba son shi suke ba, a tura min dan uwa salon su kashe min shi ko su nakasa shi wallahi ba zan yarda ba."
"Ba yarda zakiyi ba? Tow sai ki bishi karshen rashin yarda." Inji Yafendo, "Ni dai Yafendo ki daina shiga maganata, ke ba ga mijinki a tare dake ba, ko an tura shi wani wurin ne?"
"Zahra ban san rashin kunya, yaushe kika fara son Majid ɗin da kike mana rashin mutunci akan shi " ai kuwa na fashe da kuka, cike da takaici domin dai akan gaskiya ta nake magana kuma dole nayi magana akan me za a tura min miji wata uwa duniya da sunan ceto basu da sojoji ne da sai shi, don an maida min miji iliya dan mai karfi.
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB271
Ita kan Yafendo sai dariya take tana faɗin. "Eh Malamijo yana tare dani, idan kin ji haushi ki bi shi mana mara kunya." Ai kuwa na kara cika kamar balloon nace mata. "da shi shugaban sojojin da shugaban Najeriyar wallahi wani abu ya samu mijina sai na ja musu Allah ya isa " na tashi ina tafiya da kyar domin daurewa da marata tayi, ina faɗin. "duk me hannu cikin raba ni da mijina, shima Allah ka kashe shi kowa ya huta don yana ceto rayuwar waɗancan mutane za a takurawa rayuwar mu, kuma ban yafe ba haka kawai mutum yana raka ni awo anyi min bakincikin zuwa awo da shi don wulakanci babu maza ne a Nijeriya sai an zo nijar. tow ban yafe ba." Tashi Mama zata yi Hajiya ta rike ta. "Barta tayi abinta da zafi, bana fatan tayi yadda nayi bana fatan ta ji zafin rabuwa da shi, in sha Allah zai dawo gare ta " haka kawai sun dauke min mijina Allah ya isa, na fada a raina domin ban yafe ba,
Haka Hajiya tayi ta rarrashina, Mama kuwa kamar bakinciki ya kashe ta, domin gani take da gayya nake wasu abubuwan. Idan ma da gayya ce ai ina da gaskiya Allah ya isa min na fada ban yafe ba, kullum idan naji kewar shi sai na musu Allah ya isa min ban yafe ba, kullum sai na musu.
Hajiya sai da tayi wata guda na shiga na takwas, sannan ta bar Kamaru. Kafin na haihu ta ce min zata dawo, da kuka muka rabu, idan Mama ta kalle ni kamar ta zane ni. Ni kuwa ko a jikina. Wani lokacin sai ta kyale ni nayi ta rigima da Goggo Sume, ba zata iya min ba, haka nayi ta turawa ga cikin ya kara girma, har tsoron cikin nake domin idan yafi haka girma, ban san ta inda zai fito ba. Shi yasa kullum sai na yiwa Mama mita. "Ayya Mama ni cikin nan tsoro yake bani duba fa, idan yana motsi har fitsari nake yi!"
"Haka kowa yake yi, ayi hakuri ayi ta lallabawa shima ibada ne."
Haka yasa nayi shiru ban kuma cewa kome ba, tunda ta gaya min ibada ne na rungume kaina da rayuwata.