Sashe 3
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Operation Anaconda
***
A daidai lokacin da nake tsammanin mutuwata, ta zo gare ni domin nasan abubuwa dayawa sun faru a cikinsu har da rashin ganawa da mahaifiyata, wanda tana raye amma bamu san a wata duniyar take ba, iya hakan idan aka barshi a rayuwata na azabtu da rashin Uwa, nasan duk laifin na Baffa ne da Addah at least ya dace a gaya min inda mahaifiyata take. Soka min wukar a gefen cikina, yayi dai-dai da dawowata daga duniyar tunani da mafarkin zahirin da nake bayan na ga mutuwa. Sake caka min wukar yayi cikin tashin hankali ina kara jin abin da yake fada.
"Sai na kashe ka, idan ka kuma tab'a min Mamana!" Ya kara d'aga wukar zai soka min kamar wanda aka mishi wani abu, haka ya zube a jikina. Azaba da rad'ad'i yasa na kasa aikata kome, ina kwance kasarshi da alamun suma yayi domin ina jin dan bugun zuciyarshi. A hankali na tattara karfin da yaymin saura na tunkud'e shi gefe can, ina jin yadda jinin yake zuba. Ga zafi gashi yana zuwa da sauri da dumi, a hankali na fara sauka daga bisa gadon sai dai na kasa, komawa nayi ina jin wata iriyar azaba ga zufa da gajiya me haɗe da jiri kamar xan yi aman kayan cikina. Haka na koma tare da kame wurin ina kwance, nayi ta kokarin niman wani abu na rufe ciwon. Na rasa a wurin lalube na tabo fuskarshi. "Tashi ka taimaka min kada na mutu,ka tashi don Allah zan mutu ka ji." Na fada ina jijjiga kafadarshi. Kamar a mafarki yayi ta jin muryata, haka yasa shi bude manya idanunshi da suke cike da barci, "Tashi ka taimaki rayuwata mutuwa zan yi." Na fada da asalin karamar muryata.
Ina jin wani uban tsallen da ya buga, yasa ni ƙara ware idanuna, ina nishi idanuna a rufe naga kamar an haska fuskata. Bude idanuwan da zan yi hasken wuta ya gauraya dakin, sai dai abin mamaki shine bana gani sai dishi-dishi. Lumshe idanu nayi a hankali naji kamar barci ne ko wani abu ne yake faruwa da ni, na dai san ban kuma fahimtar duniyar da nake ba. Wani irin rikicewa yayi wanda yasa shi gaba-daya rud'ewa, wayarshi da yake gefen gadonshi ya dauka, tare da duba lokaci. "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un!" Ya iya furtawa domin kuwa yasan yayi abinda ya dame shi, ya kuma rasa wanda zai kira ya gaya mishi halin da yake ciki. Sake wucewa yayi ban daki ya kalli wandon shi bai ga alamar manhood ɗinsa tayi wani abu ba, amma kuma hannunshi kaca-kaca da jini. *Doctor Umaima!* Abin da zuciyarshi ta ambato kenan, da sauri ya fito tare da ɗaukar wayarshi. Jikinshi na rawa ya kirata.
"Assalamu alaikum!" Ya faɗa ta d'aya bangarenta. Ina bai samu arzikin amsa mata ba ya jifa mata tambayar. "Kina asibiti ne?"
"Yes ina Night ne!"
"Alhamdulillahi! Umamai don Allah ina cikin tashin hankali ne, na yi attempt kisan kai. Please ki taimaka min gani nan."
"Ya Rahaman,tayah hakan ta faru?"
"Ba lokaci gani nan." Ya faɗa mata, sannan ya koma kan gadon ya dauki wani towel ya daure inda jinin yake zuba, sannan ya dauko zanin gado ya nad'e ta da shi, kafin ya kuma ɗaukar bargo ya dunkule ta a cikin, sannan ya dauke ta, ya nufi hanyar waje, ta falonshi ya shiga gareji.
Ya ajiye ta bayan motar, ya koma ya dauko key, yana zuwa ya bude a cikin motar ya sakata, ya koma ya gyara dakin shi tas, yana jin zuciyarshi kamar zata buga, yasan halin Commodore Magaji Abba Chindo, yana samun labarin ya kashe yarinyar kwanar shi ya ƙare. Haka yasa shi kara rud'ewa domin wannan aikin shi ne farincikin shi, shine kome na shi idan ya sake ya rasa shi tabbas sai yayi matukar danasani. Haka ya gama goge dakin ya saka kome a wancan dakin duhu, sannan ya nufi gareji a lokacin Dr Umaima ta kira shi ya kai sau uku, yana shiga motar ya kirata. "On my way!" Ya kashe ya kunna motar sannan ya fito ya bude get din, ya koma ya fitar da motar, sannan ya sake dawowa ya rufe get din ta ciki ya koma ta fito ta kofar gidan.
Har ga Allah ya tsani kanshi, wannan lokacin ya dace ya rabu da wannan laluran, amma ina kamar kara cusa mishi abin ake, kara ji yayi ya tsani ahalin shi idan aka cire Hajiya. Itace har abada ba zai tsaneta ba, tunanin shi ne ya katse lokacin da ya iso bakin get din fita. Ya nuna ID card ɗinshi, haska motar suka yi, sannan suna ga normal bargo ne. "Oga ina zaka?"
"Zan shiga clinic ne an kira ni."
"Ok Oga kayan cikin motar nan fa?" "Idan na gama aiki xan kwanta ne, bargo na ne."
"Ok ku bude mishi kofar!" Haka suka bude mishi kofar, ya fita yana sauke ajiyar zuciya. Da gudu ya nufi titi tare da ɗaukar hanyar asalin cikin barrack din, yadda yake gudu kadai zai tabbatar maka, yana biyayya ne ga zuciyarshi da take bugawa.
Koda ya isa asibitin dake d'an tafiya ne ya raba su, yana isa bakin get din aka tsare shi, mika musu ID card ɗinshi yayi, suka bude mishi domin sun san likita ne, kuma babba, yadda yake tukin har ya isa bakin Asibitin zai saka ka gane Allah kaɗai ya kawo bawan Allah nan asibitin. Yana shiga harabar asibitin Dr Umaima da wasu Nurse biyu suka fito, zasu amshi mara lafiyar, suka ga ya bude motar ya dauko ƙunshin bargo. "Jeed Ina mara lafiyar?"
"Ba lokaci mu wuce ciki " ya dauki bargon suka wuce cikin asibitin. Kai tsaye emergency room ya wuce da ita. Ya kwantr da ita a saman gadonsu na marasa lafiya. Sannan aka shiga bude ta, har aka bude ta gaba-daya. Har lokacin jini yake zuba.
"Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Tana zubda jini" Doctor Umaima ta faɗa da sauri tana danne wurin. "Ki taimaka min kada ta mutu."
"Kayi wani abu, a tsayar da jinin nan, a shiga da ita tiyata."
Cikin abinda bai wuce minti ashirin ba,suka nemi yin tiyatar . "We need blood?"
"Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un!;babu a bank ne?"
"Ban sani ba!"
Da sauri Nurse Biodun ta bude blood bank, ta ce musu ."Daya ne ba zai wadatar ba."
"Za a samu mutane a lab?"
"Bana tunanin sun tashi,saboda aikin su ba dare ba rana ne." Da sassarfa ya fita ya nufi can wurin lab din, ko minti talatin ba ayi ba, ya isa sun rufe da kyar aka samu wanda yake kwana a wurin. "Duba jini na, group O+ ne" Ciro wayarshi yayi ya kira Doctor Umaima. "Leda nawa ake so?" "Ina ga hudu zai yi, don yanzu na samu an tsayar da jinin."
"Ok ki kokarta gani nan zuwa." Ya faɗa, kallon mutumin yayi, bai mishi magana ba, ya dauki duk wani abun bukata, ya fara aikinshi, cikin ikon Allah dake mutumin yasan shi, kuma yana tambayar shi, sannan yana duba medical records dinshi a computer ɗinshi, sai gashi Allah ya takaita da sai anyi ta tests. Aka dibi leda daya, can aka kuma diban na biyu, a lokacin aka barshi ya huta. Kiran Doctor Umaima ya shigo mishi lokacin ana diban na uku. Cikin tsananin gajiya ya ɗauka. "Saura leda daya, a zo a karbi sauran"
" Captain!"
"I'm okay!" Ya faɗa cikin karfin hali, can kuwa sai ga nurse da wani soja, aka zo aka amsa. Yana isa wurinta ta ce mishi. "Baka saka hannu ba a Matsayin."
"Umaima rayuwar yarinyar ne mai muhimmanci, ba saka hannuna ba."
"Ok"
Haka suka shiga da ita aiki, yana kwance ana diban jinin karshen.
Wurin karfe biyar na Asuba ya fito a hankali yana jin jiri na dibanshi. Dakyar ya isa emergency room. Zama yayi a kujerar da ke cikin dakin, jin kiran Sallah yasa shi nufar masallaci, yana sallah a nan ya kwanta domin wani irin jiri da zazzaɓi yaje ji.
Karfe shida na safe Doctor Umaima ta fito, a matukar gajiye domin babu inda baya ciwo a jikinta. Sannan aka turo yarinyar a gadon marasa lafiya. Aka kaita ward, wucewa daki tayi ta gabatar da sallar asuba, sannan ta shiga hada kayanta. Tana kokarin kiran wayarshi amma ba a dauka ba. Sai da ta cire kayan jikinta sannan ta wuce dakin da aka kwantar da yarinyar, bata ga wani fuskarta sosai ba, ta juya ta fita wurin seven ta bar asibitin. Yana barci a cikin asibitin yaji kiran da wayarshi keyi, kamar a tsakiyar kanshi. Bude idanu yayi da suka yi wani irin fari da ja. Yasa a kunne. "Sir kana ina ne? Za atafi teku."
Wani irin jiri ne ya kwashi Idanunshi ya ce. "Ok gani nan" kashe wayar yayi ya sauke ajiyar zuciya, kafin ya hada karfinshi wuri guda, ya tashi tare da ɗaukar kome na shi ya fita daga Masallacin domin yasan team lead ɗinsu Commodore Magaji Abba ne, haka yasa ya boye ciwonshi domin ya san halinshi sarai, and yaso ya kuma ganin yarinyar nan, haka ya kwashi motarshi a guje. Sai community dinsu na sojoji. Yana isa a daddafe ya shigar da motarshi, sannan ya wuce kitchen ya haɗa tea me kauri ya sha, kafin wani lokaci ya fara zufa kamar me. Wanka ya shiga yayi sannan ya kimtsa ya fito daga gidan ya turawa Doctor Umamai kudi tare da short Note.
*Yarinyar nan idan ta farka please ki bata wannan! Thank you da abinda kika min!*
Daga haka ya fita bayan ya dauki duk wani object na aikinsu.
Operation Anaconda plan.