← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 138

Sashe 40

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Zulaihah kenan, idan na gayawa Zahra ce kin ta bata maganin zubar ruwan nono ya zaku kwashe? Ko na gaya mata cewa da bariki zaki shiga niman kudi ya zata ɗauka?" Wani irin rawa jikin Zulaihah ya ɗauka, tana kallon addah hawaye na zuba mata. "Addah me yasa zaki min haka? Me yasa karfi da yaji kike son lalata rayuwar Zahrah? Meye tayi miki? Na zata idan wani zai dauko wuka domin ya kashe zahran ke me kare ta ne ashe ke ce kike dab'a mata wuka ta baya me yasa sai ita? Gaskiya Allah ba zai barki ba, hakkin mu ya ishe ki duniya da lahira." "Yarki zaki bani!" "Har abada ba zan baki Y'ata ba, Zahra ce zata riketa. Na san Ummi zata gaya mata gaskiya amma na fi son koda zata tsane ni ke ta fara tsanarki na har abada."
"Ai kuwa zata bani ita domin na sayar da ita, kamar yadda na sayar da ke har mahaifanki domin kada ki sake haihuwa."
"Addaaaah" ta kira sunan da karfi, "me na miki?" "Baki min kome ba, Yarki zaki bani."
"Kin dauki kasonki Yarinya ko bayan raina ne diyar Zahra ce, don haka duk abinda zaki yi kiyi." Tafa hannunta tayi, sai ga wasu kartin maza sun shigo, haka suka kama Zuzu suka mata allura sannan suka kyaleta. A hankali ta kalli Addah, "da ke da Ummi kun sayar da Munaisah, bayan kun kashe Nenne. Yau ni kika sayar Addah matukar na rayu wallahi sai na farauce ki kamar yadda mafarauci ke farautar dabba." Harshen ta ne yayi mata nauyi daga nan bata kara magana ba, tana kallo suka rufa mata farin mayafi.
---
Lokacin da na isa tantin mu, dauke da Babyn sai da Ummi ta mike tana leka yarinyar. "Yarinya tafi Zuzu kyau!"
"Wallahi kuwa!" Na fada, ina mika mata babyn. "Ummi Khair!" D'ago kai tayi tana kallona. Idanunmu ya haɗe da juna. "Me kuke aikatawa da Addah?" Murmushi tayi a hankali ta juya min baya, tana fadin. "Addah dai ni ina yi ne domin kare rayuwar mahaifiyata, duk lokacin da zata dauka zan so ta rayu koda ba zata yi magana ba, ba zata motsa ba ina son mahaifiyata."
"Ina kuka kai Munaisah?"
"Munaisah ta fiki gata, ta tafi inda zata samu nutsuwa ne, matukar tana tare da ke zata iya daukar zugar Addah ta kashe ki."
"Ummi ban gane ba?"
"Ba zaki gane ba, amma anan inda muke rayuwa ba zata yiwu ba sai da cin amana, sai da zalunci, sai da cutarwa ko ita Zuzu ai ta cutar dake ta hanyar da ba zaki tab'a yafe mata ba. Shi yasa don ki yafe mata idan kika samu labarin ta baki yarta ba zaki ji labarin nan kusa ba, kina da sauran lokaci ki je ki ji daga bakinta me ta aikata miki, Mother Teresa!" Ta fada tana mika min babyn, sake rungumar Babyn nayi zan fita. "Zuciyarki tana da kyau sosai Zahrah, kina da adalci sosai shi yasa ba zan iya cutar dake ba, amma kowa kika ga baki ganshi ba adalci yayiwa kanshi domin akan kuɗi zasu aikata kome infact har dani zan iya kome abu daya yasa na kasa cutar dake Yakumbo", ta kalleta tana murmushi. "Amma idan ta nice yadda ake bani kudi domin na sayar da kowa kina nufin ba zan iya ba ne? Yakumbo ta yarda da cewa wata rana ke haske ce ga rayuwata."
Kunsan me ake kira da gudun ceton rai? Shi nake son nayi ko zan cimma manufarsu a kaina, don haka na sa kai na fita da gudu domin titsiye Zuzu ta gaya min wacce irin cutarwa tayi min, gabana faduwa yake ina ji kamar ana mai dani baya, duk yunkurin gudun da nake hakan amma ina kome ya lalace daga lokacin da na bar Zuzu. Koda na isa na samu an fito da gawarta ne. Haki nake ina kallon Addah kafin na kalli gawar zuzu. Da sauri na nufi kan gawar, rike ni Addah tayi tare da faɗin. "Mutane nawa ne kike son su mutu domin ki? Me yasa lallai sai kowa ya sadaukar da rayuwarshi domin ki? Me yasa lallai sai kowa ya rasa ranshi dominki? Zahra'u na rasa Y'ata dominki don haka ki bani jikata."
Kasa magana nayi ina jin jikina yana rawa.

"Ad.....!" "Dan uwana ya rasa rayuwarshi domin ke? Na rasa zuri'ata domin ke? Na rasa kowa don ke. Anya Zahrah ke mutum ce? Yanzu ma na rasa Zulaihah saboda ke." Kai na ne ya fara sarawa a hankali na isa gaban Zulaihah. "Ki tashi ki gaya mata ba don ni kika mutu ba, gaya mata ban san kome akan kowa ba. Me yasa?" Na fada da karfi, "Me yasa na zama masifa ga ahalina?" Na fada da karfi ban san yadda aka yi ba, kuka ne ya kwace min kuka nake wanda tunda nake a rayuwata ban tab'a jin shi ba. Kuka nake cikin tsannanin takaici da b'acin rai. Kiri-kiri Addah ta daura min alhakin mutuwar Zulaihah.
"Taso muje!" Uwar mugu ta riko hannuna, ina tafiya ina kuka har tantinta. Murmushi tayi tana zaune tana kallon yadda nake kuka. "Da Alamu kukanki ba yau kika tara shi ba. Don haka kiyi abinki, kiyi ko zaki samu nutsuwa."
Nayi kuka har sai da Babyn ta fara kukan niman abinci, nan hankalina ya dawo jikina. Na dauke ta cikin rawan jiki zan fita ta ce min. "Ga madarar jarirai nan ki bata!" Ta ajiye min formula na yara, karba nayi xan fita ta ce min. "Ki daina kukan haka, zab'an rayuwar suka yi, ke kuma kina da sa'a shi yasa ba zaki gane ba." A fusace na ce mata. "Shi yasa kuke bibiyarmu kuna hada mu faɗa da tsanar juna? Me muka yi muku haka?" Na tambaye ta hawaye na zubo min, "ba fa haka ba ne?" "Haka ne mana, haka ne mana me yasa tun fil azal baku gaya mana cewa nan sansanin mutuwa ce ba ta yan gudun hijira ba? Ki sani kunyi kuskure in sha Allah karshen ku yazo wallahi azim sai Allah ya wargaza wannan wurin ki saka idanu ki kalli yadda kome zai zama tarihi." Na juya na fita ko madarar ban dauka ba, muna zuwa tantin na samu Ummi tana barci. Zama nayi bayan nayi sallama da disasshen muryata, na zauna ina son nayi magana amma bakinciki ya hanani, bamu kara jin duriyar Addah ba. Zama nayi na fashe da kuka yarinyar ma kuka take.
"Ki bata nono idan ta ja ruwa zai sauka." Na kalli Ummi a mamakance. "Kin tuna kunun da Zulaihah take baki?" Kafin ta karasa na dakatar da ita. "Ba sai kin gaya min ba, zuciyata ciwo take." A hankali na bude nonon zan saka mata ta ce min."dakata!" Tashi tayi ta dauko wani garin magani ta zuba a wani bojuwa ta wanke nonon dashi, sannan ta ce min. "Bata." A hankali na saka mata nonon a baki, sai da tayi ta niman bakin nonon kafin ta fara alamar tana jan ruwa. Kuka ne ya kara kwace min ina ji kamar xan mutu kafin rana ta sake bud'ewa. Wani irin ciwo nake ji mai zafi a kirjina. Ban san yaushe xan daina kuka ba. Haka na rungumeta har ta fara jan ruwan.
Chapter 40 · 0% Book details