← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 138

Sashe 29

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wannan takin Amaryar Alhaji Mamman Ba'are ita ce mace mara yara dayawa, amma daga Rabi har Fauziya, a ƙalla suna da yara kowaccen su shida zuwa bakwai , domin gidan gasar haihuwa ake kamar yadda suke hango iyakar kokarin mijinsu.
Sannan Nana ta kara musu zafin kishinsu, ta hanyar gasa musu magana da cewa "Ni duk macen da bata haifa min jika namiji ba, ai tayi a banza tunda mace bata gadon arziki." Wannan ya kara musu kwarin gwiwa daukar ciki suna haihuwar yara rututu, don ma Uban yana tsaye akan Yaran. A gefe guda ga kannenshi da suke hararar dukiyar, wanda ya sani sarai kawai dauke kai yake akan su, fatanshi kada ya bar duniya bai samu wanda zai rike kamfanin ba.
Haka ya tawo Niamey da Sa'adatu. Asalin Bafulatana, kana ganinta kasan Bafulatana ce kasancewarta doguwa sirirya. Ga kyau ga farar fata gata da wata irin kunya da kamun kai. Haka yasa Alhaji Mamman Ba'are, kware mata daga yan kwanakin da suka yi a hanya, ya fahimci yarinyar mace ce guda, haka yasa yayi ta nan nan da ita har suka iso gida.

Sannan itama bata takura kanta ba, tunda tasan ba zata iya sauya ƙaddarar da ta same ta ba. Haka suka isa kantamemen gidan alfarma. Wanda ya gaji da haduwa kamar ba gobe, suka shiga cikin gidan motar tayi parking ya fito itama ta fito. Cikin gidan ya nufa da ita, tana baya yana gaba duk inda ya wuce gaisuwa ake mika mishi har ya nufi falon Nana, zama yayi a saman daya daga cikin kujerun falorn, ita kuma Sa'aden ta zauna a kasa, kanta a kasa. "Ka dawo Mai Babban suna, ya hanya ya kasuwar?"
"Alhamdulillahi! Kasuwa tayi albarka tunda har da mata na samu." Ya fada yana dauke kai yana kallon Sa'adatu. Kalman Alhaji Abubakar Abzin yana dawowa mishi. "Don Allah kada ka zubar mata da mutunci ta hanyar gayawa mutanen gidanka a caca ka samo ta."
"Ban gane ba?" Ta tambaye shi.da alamar bata ganen ba, gyara zama yayi ya gaya mata kome amma ya roketa da don Allah kada sauran matanshi su sani, Sa'adatu a caca ya samota. Kuskuren shi kenan bayan Alhaji Abubakar Abzin ya roke shi, shi kuma yana tunanin Nana Uwa ce da zata iya rufa mishi asiri, sai dai yayi kuskuren domin Nana bata cikin irin wadannan iyayen.
Kiri-kiri ta shafawa idanunta toka, ta shiga bala'i da hayagagga. Akan me zai auro mata mugun iri, maza ya fice mata da ita daga gida, kada bala'i ya fado musu cikin dukiyarshi mai tsafta.
Fadar Nana da ihunta yasa matan gidan sanin Alhaji Mamman Ba'are ya karo aure kuma matar Nana bata yi na'am da ita ba. Haka sukayi ta bala'i a gidan, ya wuce da Sa'adatu bangarenshi, ya zuba mata idanu.
"Kiyi hakuri laifina ne, da ban gaya mata ba da haka bai faru ba." Dake tana da hakuri haka ta sunkuyar da kai ta ce mishi. "Ba kome Uwa ce bata laifi." Wannan abin da tayi ya kara mishi kaunarta da bai san lokacin da ya faɗa ba,
Haka zaman gidan ya kasance, idan ta fita tsakar gida, Hajiya Rabi da Yaranta su rufeta da duka, koda kasheta zasu yi idan Nana ta fito cewa take. "shegiya jinin matsiyata, Ubanta da tsiya ya masa katutu a caca ya sakata. Ku kashe banza da haihuwar su gara mutuwarsu."

Harirah wacce ta kasance itama yar babban gida ce, sannan Yayanta babban lauya ne, yasa take iya shiga fadar Sa'adatu, sau biyu tana kwatarta a hannun Hajiya Rabi da Yaranta. Sun mata dukar kawo wuka, ta suma ta ce musu. "Wallahi idan yarinyar nan ta mutu sai na gayawa Yayana ya nima mata hakkinta kuma daurin rai da rai za a muku kun san dokar Nijar ai." Jin haka yasa suka rage dukanta, aMma hantara da wulakanci ayi abinci a hanata. Karshe ma sai wanda yaran suka jagwalgwala shi za su bata, ga bakar magana idan ta bukaci wani abu.

Shi Alhaji Mamman Ba'are bai san me ke faruwa ba, domin bata tab'a gaya mishi halin da take ciki ba, amma kuma tana matukar cutuwa, sai Harirah ce ta gaya mishi abin da suke mata, ta ce mishi. "Idan baka yarda ba, ka tafi ka dawo idanunka ya gane maka, nima don ina gidan ne aka rage dukanta amma matukar bana gidan tow sai abin da ya karu "
Haka ya kwana cikin mamaki, domin koda ya tambaye ta, shiru tayi mishi kanta sunkuye tana wasa da yatsunta. Washe gari da safe, suka fita daga shi har Harirah.

Lokacin har Sa'adatu ta fito tana share gidan, Yar Hajiya Rabi Babban wacce bata wuce shekaru goma ba, ta zo wucewa ita Sa'adatu bata sani ba, ta zuba mata shara. Ai kuwa yarinyar ta daddage ta zuba mata dundu a baya, tana ihu. ""Mama Mama kin ga wannan matsiyaciyar da aka auro a caca ta zuba min shara ta b'ata min safa ta." Dama Hajiya rabi tana cike da ita Harirah ta hana a casata, sai gata ta fito da wani murtikekken bulala. Ta rufe Sa'adatu da duka, tana yi yaranta suna yi. Fitowa Hajiya Fauziya tayi tana faɗin. "Shegiya sai kace Mayya idan an gama dukarki wanke -wanke na yana jiranki." Tasan ana dukarta ne babu halin amsa mata, haka ta shige kitchen ta dibo ruwan zafi zata watsa mata sai ga Alhaji Mamman Ba'are da Harirah. "Ka gani ba? Ruwan zafi zata watsa mata bayan sun gama dukarta. Alhaji kaji tsoron Allah Ubangiji ba zai barka ba, kasan zaka kawo ta cikin masifa ka auro ta ka mai da ita wurin danginta."
"Rabi da Fauziya. Na baku nan da minti ashirin ku bar min gidana, idan kuwa na dawo na.same ku wallahi sai na sake ku.". Ya nufi Sa'adatu ya dauketa suka nufi ciki. Goge mata fuska yayi yana son yayi Magana amma ya kasa magana. "Shirya mu bar ƙasar."
"Ina zaka kai ni? Wurin Abbati? Ko wurin Baffana?" Ta tambaye shi cikin kuka. "Wani wuri da zaki rayu babu faɗa babu tsangwama."
"Tow."
Haka ta shirya kayanta sannan suka fito a lokacin Nana ta fito tana kallonshi. "Ban gane ba, ina zaka kaita?"
"Idan Uwar da ta haife ni, ta gaza taimaka min waye zai taimaka min? Nana ke kika basu damar cutar min da Mata? Nana gani na da kika yi a raye yasa kike cutar da abinda nake so? Nana zan nisantatta da ku ne domin Harirah ta gayawa dan uwanta na auro mace na kawo Matana suna son kashe ta, kotu zata turo min sammaci sai ki san abin da zaki ce musu."daga haka ya riko hannun Sa'adatu suka bar gidan, Marad'i ya wuce da ita suka kwana biyu, a wannan kwana biyun ne, ya mai da ita cikakkiyar mace, cikin alfahari da samun mace irinta, dama an gama.mata kome na makarantar, da shi da Alhaji Abubakar Abzin suka tawo da lta garin kano, inda ya tsaya sai da yaga ta fara karatu. Don kusan watan shi biyu
kafin ya fara shirin dawowa nijar ya rike hannunta.
"Kinsan dalili na na kawo ki nan, kin san kudirina na kawo ki nan. Don Allah kiyi karatu sosai, kiyi abin da ya kawo ki zan na zuwa lokaci zuwa lokaci ina duba ki."
Gyada kai tayi, Washi gari motar shi tazo ta dauke shi, haka ya barta cikin kewa da rashin sabo, ta fara karatu a BUK, a tsangayar tattalin arzikin kasa da kasuwanci. Yarinya me kwazo da hazaka.
Wata ukun farko da fara karatun, kaf tsangayar suka san tana ja,. Ai kuwa shima Alhaji Mamman Ba'are da suka zo da Alhaji Abubakar Abzin, ya ga sakamakon da ta fara samu ya fahimci yarinyar guruwa ce, domin samun irinta a cikin Yaranka ba karamin arziki ba ne.
Haka yayi ta dora Alhaji Mamman Ba'are a kan hanya, yadda zai na kyautatta mata. Har ta samu shekara daya a lokacin ne ta samu cikin Abdul Majid. Cikin tsananin zafin laulayi haka ta haɗa karatu da laulayi tana tsoron kada ta samu matsala ya ce tana wasa, a lokacin ta shiga aji biyu. Haka yazo ya samu tana fama da laulayi ga shi suna tsakiyar semester, kanta yayi zafi duk da wannan yanayin bai gaza gaya mata kudirinshi ba, har ya gama kwanakinshi zai tafi ya ce mata. "Idan mace kika haife zan barki ki kara haifar daya, su zama biyu kema ki samu abokan hira, don Allah ya azurtani da Yara mata sun kai goma sha bakwai ga na cikinki ga na cikin Rabi da Fauziya. Don haka kina haifan biyu zan kai ki a cire mahaifar ki huta kinji."

Gyada mishi kai tayi tana jin duk abinda ya ce, domin ita ba zata tab'a bijire mishi ba, shi din kamar waliyi ne a gare ta, haka yasa ta ke daukar duk wani abin da ya ce da muhimmanci. A hankali ya shafa kanta yana rungumeta. Abu daya yasa yake sonta, ilimi da kokarinta. Kuma yaranta zasu banbanta da Yaransu rabi haka yasa yake kara jin dadin ganinta tana kara mishi biyayya.
**
Ya dawo da su Hajiya Rabi, suka nime saka Harirah gaba, danginta suka ce basu san da zancen ba, kada su fara saka yarsu a gaba ba yarda zasu yi ba. Haka ba karamin ja mata mutunci yayi ba. Bayan shekara daya ne Alhaji Nasiru Wodabbe da Mahaifin ta suka zo mata da kayan aurenta, kayan alfarma na yar gata, da wasu daga cikin yan uwan Mamanta,. Dake Alhaji Mamman Ba'are har kasarsu ya tafi ya je suka ganshi ya tabbatar musu tana lafiya, sai gashi sun kawo mata kayan aurenta da duk abinda ake na al'adar kasar nijar. Shima ganin ya auri yar babban gida, basu bar kasar ba, sai da ya ajiye musu kayan auren da ake a cikin kayan har da zinari babba tukwaicin budurcinta.....
#past
#entangled
#revals
#lovers
#Dambuje😹
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*

{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu

_🙄 Wai page biyu kuke so, Yasin kuyi maneji mana😿 masoyan Addaririya_
Chapter 29 · 0% Book details