Sashe 92
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk yadda taso cire lamarin, abin ya ci tura don ta saka a ranta sai ta mu'amalanci Abdul Majid Mamman Ba'are, don ya mata kuma ko yana da mata ko bai da mata sai ta saka ya aure ta, ta kware a yaudara da iya bibiyar namiji, sai dai har yau idan ta tuna da Zahrah tana jin kamar bata mata adalci ba, sannan itama Zahrar tayi mata laifi da ta bata amana bata cika mata ba, sai dai ita ta koma koda yake ta ji labarin abin da ya faru na tasar sansanin da wani yayi, tasan inda Zuzu take amma bata jin zata iya taimaka mata, domin ta rama abin da Addah tayi masu na lalata musu rayuwa da tayi.
***
Baya bata kaɗan, ashe tunda na daina zuwa, Hajiya da Aryan sun yi ta nima na domin har marad'i suka je, aka ce na turo a sauya min wuri amma bana nan, naji labarin ne a bakin Aseem. Bakiɗaya rayuwata ne ta sauya domin kome zan yi ina da masu tsaya min, shi yasa ban wani ji zafin rabuwa da su Ya Amaan ba.
Ranar juma'a mun taso aiki, na dawo gida na ji gidan shiru.
"Siyamah ina Amirah."
"Wai an zo an dauke ta." Ban san lokacin da na mike ba.
Kai ban san na fito waje ba, sai da ta biyo ni, bakiɗaya na manta Amaan shi ya sakata a makarantar, kuma da can yana daukota. Ai kuwa kafin wani lokaci na birkice na birkitawa kaina lissafi. Nida Aseem muka tafi makarantar, Allah da ikon shi, muna zuwa aka fara bincike da shigarsu da fitarsu sai ga shi nan, lokacin da yazo ɗaukarta. Wani irin sanyi naji.
"Kun gane shi? Sannan shine ya fara kawota ai makarantar shi yasa ba a hana shi daukarta ba."
"Kuyi hakuri." Inji Aseem har da yan matan hawaye, haka muka nufi gidansu. Koda muka isa a harabar gidan muka ga yara sun cika, alamun ana wani hidima ne. Shiga cikin gidan nayi, har falon Hajiya. Yarinyar tana gefe can da alamu tayi kuka har ta gaji. "sugrah!" Na ambaci sunanta. Da sauri ta mike tare da nufo ni da gudu, bude mata hannu nayi ta faɗa kirjina. Dariya yaran suka yi, da suke falon daidai fitowar yarinyar asibitin. "Mami muje gida."ta faɗa tana kuka har da shashekar kuka, alamar tayi kukan sosai tun kafin nazo. "Waye ya tab'aki?" A hankali ta bude cinyarta, ja fatar wurin yayi tana me faɗin. "Muje Mami."
"Waye ya kona ki!" Na fada da karfin tsiya, ina son Amirah, bana kaunar wani abu ya same ta. Runtsa idanunta tayi taki budewa. "Ni ce wani abu zaki iya?"
Na d'ago kai tare da binta da idanu. Bakina ya kasa furta kome, nufarta nayi na kifeta da mari, tare da riko jelar gashinta. "Wallahi kinci albarkacin Amaan, idan ba haka ba da sai na koya miki hankali." Na hankade ta, na wuce.
Tare da ɗaukar Yarinyata,muka bar gidan.
"Akan me zaki kona mata yarinya?"
Inji Aryan da yake saukowa daga wurin Majid."akan me ba zan konata ba, tunda tazo birthday din Mimi ta kwace kawayen Mimi."
"Mimin da bata wuce shekaru biyu ba, har tasan kawaye ne? Ke munafuka me bin namiji ya sota, ai wallahi keda Alhajin Allah sai dai ki ga ni daga nesa, munafuka algunguma, ina ke kika ce Aliyu ya dauko miki yarta zaku yi kafircinku shine bari ki toya mata Y'a algunguma idan ma kina haka ne don kada ta samu matsuguni tow annamimiya ta samu domin fadima bata da miji sai Alhajin Allah, doguwar mace ba."
"Ni kam Nana me na tsare miki ne?"
"Au zagina zaki yi? Waye bai san kaso aurenki kika yi ba, sakarya me kama da gwanki me rangwangwan."
Cin mutuncin da Nana tayi mata Allah kadai ya sani, Hajiya ma ta gaji da halinta, haka yasa taki kula su, ai kuwa tayi kuka sosai ita kuwa Nana ta sako Aryan a gaba ya kaita gidan Zahrah.
...
Mu daga nan asibiti muka kaita, aka saka mata magani, sanan muka koma gida, a kofar gidan na ga Aryan din da tsohuwar nan. "Zahra'u kiyi hakuri kin ji, wallahi ban ji dadi ba ban san abinda ya faru ba kenan, ai in sha Allah ita da Alhajin Allah sai dai taga ana yi. Me yasa kika daina zuwa wurin Yayanki bayan kinsan ba lafiya ne da shi? Dalilin da yasa ya biya makaranta ya dauko yar jikalle kenan, kiyi hakuri ina baki hakuri da abinda aka miki."
"Hajiya ba kome ya wuce ai, don Allah ki ce kada ya kuma.daukarta ba tare da izini na ba, hankalina ya tashi."
"Haka ba zai kuma faruwa ba, kin ji."
"Fadime me yasa kika bar kamfani "
"Ya kake so nayi? IT nazo yi, tunda members na kamfani sunce basu bukata na me zan.yi?"
"Shi kuma asibitin fa?"
Murmushin takaici nayi, sannan nace mishi. "CEO Aryan Mamman Ba'are, akan idanunka Chairman yasa aka duba abincin da na kawo ko? Sannan akan idanunka sisters dinka sukayi ta bullshit dina, me kake son nayi? Nazo asibitin sun ce kada a kuma barina na shiga gaya min dole ne ni a gare ku."
Hawaye ne ya zubo min, "Ni na iya manejin rayuwa, ko babu Ya Amaan ina iya rayuwa na gode."
"Su waye suka saka hana ki shiga kamfanin gaya min naje naci kundugurin ubansu."
"A'a Hajiya ya wuce wallahi."
Haka na shige na barsu a wurin, ai da suka koma gida Nana tayi ta bala'i kamar zata yi dambe.
Haka lokaci yayi ta tafiya har na gama IT na, na koma makaranta muka doshi Final year , tunda muka dawo babu abinda ya kuma faruwa sai alkhairi.
•
Wannan shine karo na biyu da taso ganin shi babu hali, a cikin wata shida. Amma yau da alamu har ta samu shiga. Tana zaune ya shigo, sanye take da doguwar rigar abaya, lokacin da ya shiga office din ya zuba mata idanu, shi kanshi ya shiga wani irin rud'ani don ya zata Zaytoonah ce.
"Barka dai Mr Mamman Ba'are, ina farin cikin samun ganawa da kai."
"Hmm!"
Ya zauna yana jin wani abu yana yawo akanshi. "A cikin wata shida yau Allah ya bani damar ganinka," zama yayi a table dinsa yana kallonta. "Nazo ne akan abinda zamu iya cimma idan ka amince." "Hmm!"
"Ina sonka da aure."
"Zan gaya miki gaskiya, ni ba zan aure ki ba."
"Akan me yasa?"
"Don my heart belong to somebody else."
"Kada ka saka nayi kisan kai."
"Ba zaki iya kome ba, domin Allah yana kare ta a duk inda take "
"Kana ja da ni kenan."
"Munaisah Abubakar Takum, na jahar taraba da yake Nigeria. Kina da kasuwancinki a Poland bayan kin shiga ta haramtacciyar hanya, sannan kina zaman dadiro da Paul wanda yake son aurenki. "
Tafi ta kama tana faɗin. "Lallai na yarda kai na musamman ne."
"A haka ba xan auri macen da ta kasa rike kimarta da rayuwarta ba. Kada na kara ganinki a kasar nan."
"Sai na binciko yarinyar nan da kake so na aikata lahira."
"Ina miki fatan alkhairi."
"Kana wasa dani."
Wayar Office din ya dauka yayi magana sai ga security suka yi waje da ita. Mikewa yayi yana kallon yadda take masifa.
_"Tashi ka taimaka min kada na mutu,ka tashi don Allah zan mutu ka ji._ "yummmy" yaji wani abu yana yawo a jikinshi. A ina zai ganta? Ya ganta shin tana raye ne ko ta mutu.
Amma me yasa yake jin wani irin abu akan Fadima? Shafa kanshi yayi idan har wancan yarinyar da a wancan daren tayi faffutukar kare mutuncinta, zata amince tabbas zai aure ta, domin yadda tayi ta gudun ceton mutuncinta ba wai don ta rasa yadda za tayi ba ne, a'a irinsu ƙalilan ne acikin mutane, da duniyar nan akan yarinyar da bata wuce shekaru sha tara ba, ya amma a yanzu yasan zata bawa ashirin da wani abu baya, murmushi yayi yana shafa kanshi lokacin da ya kwanta da ita a asibiti, murmushi yayi yana ji a ranshi tabbas ita ce zata. Iya hakuri da shi ba zai tab'a give up. Zai nemeta ba zai hakura ba.
Wayar shi ya ciro ya gwada kiran Umaimah. "Hmmm!" Ya ce mata yana ahafa kanshi. "Ka kira ni ne ka ce min hummmm?" "Dr yarinyar nan fa?" Ya tambaye ta, yana murmushi. "Ka kira ni ka gaya min bakar magana ne?"
"Idan na gaya miki fara ci zaki yi?"
"Ok sai an jima."
"Kin ga labarin yarinyan nake nima?"
"Ka je garinsu mana."
"Akwai tazarar da yake tsakaninmu ba zai hana ni nimanta ba."
"Hmmm, sai ka nimeta ai."
"Shugaba."
Kashe wyaar yayi don ya fahimci haushinsa take ji, kuma ba zata tab'a tsayawa ta saurare shi ba...
A hankali ya wuce waje hannun shi a cikin aljanuh wandonshi, duk inda ya wuce gaida shi ake har ya fito inda motarshi take ya shiga....
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
07035133148 or 08130269641
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB248
A hankali ya malala hancin motar har ya fita waje, yana fita kuwa ya ga motar Munaisah tana bin bayanshi har ya bar area din kamfanin bata daina bin shi ba, don haka yana isa gidansu kafin ta shiga ya saka kada a bari wani ya shigo gidan, haka yasa koda ya shiga tazo babu wanda ya kulata, dake tana ganin kamar kowa mayen kudi ne, har da fito da kudi ko zasu. Barta ta shiga amma suka bawa banza ajiyarta, ganin haka ta tsaya ko wani zai zo fita ta samu damar shiga gidan, amma babu hali.