← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 138

Sashe 17

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Hajiya da Yaranta baki daya wucewa gida suka yi, Majid da daman ya rigasu barin wurin taron, sun same shi a dakin shi na Asali , yana kwance. Dakin duhu kamar kullum. "me yasa kake son zama cikin duhu?" Tashi yayi zaune yana kunna wutar da yake gefen gadonshi. "Hajiya ina jin dadin haka ne, domin yana tuno min da wasu abubuwan da suka wuce."
Murmushi tayi tana kallonshi ya kara girma, ya nutsu ba kamar lokacin baya ba. Ya zama cikakken namiji me cikar halitta, sadauki da duk inda ake nimanshi ya kai. "Abdul Majid maganar aure fa?" Gabanshi ne ya fadi, ya kurawa ƙasa idanu. Akwai wani abu da yake rufewa a zuciyarshi baya jin zai iya aure. "Hajiya!" Ya kira sunanta muryar shi tana rawa. "Hajiya auren nan dole ne?"
"Dole ne Majid! Dole kayi aure domin haka ne zai saka ka kara zama cikakken mutum ka zama magidanci."
"Hajiya."
"Akwai yar kawata babanta abokin cinikin mu ne, kaje an jima da yamma ka ganta."
"Hajiya!" "Bana son musu, ai na maka adalci rabonka da kasar nan." Mikewa tayi tare da fita daga dakin. Sai da ta isa bakin kofar ta juya ta ce mishi. "Ka fahimci gatar da zan maka amma ban maka dole ba." Gyada kai yayi yana jin kamar ya fasa ihu.

Hajiya tana fita falon ta Salamatu me aikinta tace "Hajiya akwai baki a falon kasa ." Kura mata idanuwa tayi ta ce mata. "Su waye?" Cikin girmamawa ta ce mata. Hajiya Nana da Hajiya Hadiza!" "Muje!" Tsayawa Salamatu tayi Hajiya ta shiga gaba, har falon kasa suna zuwa suka same su a hakimce. Niman wuri tayi ta zauna tana gaishe su. "Ina Abdul din yake?" Inji Hajiya Nana. "Yana sama!" Kwafa tayi ta ce mata. "Wato har ya kai da ya mai da mutane yan iska ko? Sai yazo gari ya ki zuwa gaishe da Hajiya." Murmushi Hajiya tay ta ce musu. "Na ga dai Abdul Majid Mamman Ba'are, d'ana ne kin manta ne Hajiya Hadiza? Da kika ce Yaransu Hajiya Rabi da Fauziya sune Yaranki, Yaran da suka fito daga jikina Yayan bariki ne, yanzu kuma da wacce kuke tafe?"
Kurawa Hajiya idanu suka yi, Nana ta ce. "Bana son munafurci, kiyiwa jikana magana yazo har gida ya..."
"Tunda kika kasa hakuri kika zo takalata da faɗa, kin san dai baki isa na zo har gidanki ba." Ya fada yana gyara hannun rigarshi. Kallonshi tayi wannan yaro yana bata tsoro har cikin ruhinta. Hadiye yawu tayi tana kauda kanta domin tana matuƙar tsoronshi. Zama yayi ya kalli Hajiya Hadiza ya ce mata Mama Barka dai."
Tab'e baki tayi ta ce mishi. "Barka."
"Yanzu Alhaji sai kazo garin nan baka zo ka duba ni ba.? Fisabilillahi." Ta fada kamar zata fashe da kuka.....

#thedambuje
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*

{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*009*
Tamke fuska yayi yana kallonta, domin ba zai tab'a mantawa da izayar da matar nan ta bashi ba, cikin muryar shi mara daɗi ya ce mata. "Nana kin ajiye ni ne da zan zo na duba ki?" Shiru tayi tana kallonshi kamar zata mutu, idan ta ga yana nuna mata kiyayya haka. "Alhaji ina laifin Nana don ta damu da kai?" Mikewa yayi bai basu amsa ba, musamman ita Hajiya Hadiza da ya tsani ta mishi magana.
"Kyale shi ai Uwarshi tana gani yake wulakantani." Murmushi Hajiya tayi tana faɗin. "kin sha gaya min idan kina magana da ahalinki na daina shiga cikin maganar, kuskure ne don na zab'i yin shiru akan na magantu?"
Cikin borin kunya ta ce mata. "Hmmm! Haka dai kika ce, amma ni yaushe na ce ki daina shiga cikin ahalina. Yanzu dai nazo ne maganar kamfanonin nan, da fatan dai ba za a cire min hannun jarina ba ko?"
"Ni babu ruwana ki same shi." "Tow ta nan kika bullo min Sa'adatu?" A gajiye da halin Nana Hajiya ta ce mata. "Nana meye nawa a cikin wannan lamarin? Yaran nan jikokin ki ne, sannan kuma."
"Kawai dai ki ce mana Yaranki sun fi karfinki, amma taya akan wannan yar maganar zaki ce wai babu ruwanki salon munafurci da nunawa kamar ba ruwanki." Inji Hadiza Abdul Majid ba'are, "Hadiza kin ga babu ruwanki da sha'aninmu, tsakanin Nana da Jikokin ta gata ga su ina ruwana?"
Chapter 17 · 0% Book details