← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 138

Sashe 51

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*024*
Kallon Aseem yayi kafin ya ce masa. "Ka fice min da ita ko kuma na had'a da kai." Haka ya saka Reshmah a gaba ya wuce da ita wani gidan da aka ware domin hukunta duk wanda ya ja da Yazid, gidan kamar gidan yari yake, sannan a cikin gidan akwai masu kula da kowa kawai ba zaka fita ba,ba zaka iya kome ba kana zaune a daki guda ga kome amma kuma takure kake.
Ya kaita can wani daki da yafi kowanne kyau, "Aseem don Allah ka roke shi."
"In sha Allah." Ya fada, yana me barin dakin, kuka ta fashe da shi a ranta tana kara shan alwashi sai ta wulakanta Zahrah matukar ta fito.
----- Tun da nake a rayuwata ban taɓa cin karo da irin wannan abin ba, domin kuwa ban zaci mangyad'a mai zafi zata watsa min ba, dafe goshina nayi ina mamakin kishinta. Ina zaune har su Addah suka dawo. Muna zaune ana cin abinci kawai muka ga mutanen Yallabai sun shigo cikin dakin, basu yi magana ba suka dauke ni. Zasu fita dani nace musu. "Ina da karamin goyo don Allah ku bar ni na dauke ta." Haka suka fita dani, dariya Addah takamayi tana cin abinci."Allah yasa su mata abinda ya wuce tunaninta."
"Kenan ke ce kika hada mata rigimar?" "Eh nice!" Ummi bata kuma magana ba, tana mamakin Addah.
Da suka wuce dani can wajen garin suka ajiye ni a gabanshi. "Kuje!" Kaina yana sunkuye. "Ke meye ya haɗa ki da Sultan?" Da sauri na d'ago kaina ina kallonshi, fuskarshi a rufe sai idanun shi kawai nake gani. Sake daka min tsawa yayi, na fashe da kuka, musamman da ya fidda wuka tsirararta. " Ban san shi ba." Na fada ina ja da baya, "Meye alakarki da Yazid?" Wani irin curewa yayan hanjina suka yi, jikina ya dauki wani bala'in rawa, na ja da baya ina girgiza kai. "Ba zaki gaya min ba kenan?" Ya kara daka min tsawa, kuka na saka mishi me karfi ina faɗin. "wallahi babu kome." "Ok tashi ki gudu" da sauri na mike tare da diba a guje, sai dai ko wurin ban bari ba, na ci birki sakamakon kartin mazan da na gani sun tare ko ina. hankali na a matukar tashe na waiga na ga sun zagaye ni. "Daga yau kada na kara jin labarin kin hadu da shi ko kin shiga gidan, idan kuma kika kara sakewa kuka hadu ko?" Ya fisgo ni tare da yaga min riga har kasa, kare kirjina nayi ya saka kafa ya tokare ni sai da na fadi. Ba a tab'a tozarta ni irin na yau ba, domin yana tsaye a kaina ya cire gabanshi ya shiga sakar min fitsari a kaina, sauran suka kwashe da dariya. "Wannan wasa ne, wanda zan miki ba fitsari ba ne, tsakanin cinyoyinki zan raba, nayi sukuwa a akanki yadda zaki ji rad'ad'in haka a ranki, naji labarin baki tab'a karo da namiji ba." Ya maida abin shi ya matsa a kaina, ya d'ago kaina ya dinga marina. Sai da naji kamar fuskar bata jikina, na karshe ne ya mare ni akan idanuna. "na tsane ki daga yadda Sultan yake zubar da kimarshi akanki." Suna gamawa suka watse daga wurin aka bar ni babu kowa. Haka na mike a hankali naji wani abu ya cika min zuciya na kasa kuka, har na kusa shiga gida, tun kafin na isa gidan nake jin Ihun Baby. Har na isa babu wanda ya kulata asalima a duhu suke. Banɗaki na Wuce ina ta kwara ruwa, ina wanke jikina sai da na wanke ko ina sannan na koma dakin.
Na dauke ta tare da rungumarta ina sheshekar kuka, daga Addah har Ummi babu wanda ya ce min, nayi shiru a hankali barci ya dauke ni, ga ciwon da idanuna suke domin ina ga da wani abu ya mare ni ba da hannu ba. Sai asuba na tashi nayi alola nayi sallah, ina idarwa na juya na kwanta sai dai kamar yadda nake saka raina zan yi barci, ashe abin ba haka ba ne,. Wasu kartin maza ne suka kuma zuwa suka tafi da ni wannan karon ina ganinsu na dauki Babyna muka tafi, tun daga ranar ban kuma zama ko na minti biyar ba tare ina aiki ba, wahalace ta karu min kamar na mutu na huta, haka nake fama da aiki babu dare babu rana, sannan abinci sau biyu ake bani sai yanzu na fahimci akwai iyakata akwai iyakar wasu, Yazid iyakar wasu ne, shi din duniyar wasu ne da zarar na sake wani abu ya kara had'a ni da shi tabbas zan iya fuskantar mutuwa. Haka yasa nake addu'a ba dare ba rana, ina gayawa Ubangiji ya kawo min mafita da karshen wannan halin da nake ciki.
-----
A bangaren Yazid babu ranar da ba zai tambaye su Zeehrah ba, an kai mata abinci Ya Baby take, babban burinshi ciwonshi ya warke ya tafi ya ganta, domin baya iya fita ko waje ne, yana cikin gida yana fama da ciwon.
Akwai wani abu da dayawanmu mata bamu gane ba, shine idan har namiji ya lakato batun dating da wata mace mafi alkhairi mu kyale shi, mu zuba mishi idanu. Idan kuwa muka ce zamu yi magana. Tow kuwa ya dinga abun da zai b'ata mana rai.

Gashi ko sati ba ayi ba, Aseem da Sharif suka saka dakyar ya fito Reshmah, amma abin da tayi ya tab'a zuciyarshi, sannan ba karamin hakuri da juriya yake da shi ba, domin da mace ce aka watsa mata mai da ba karamin jinya zata yi ba. Amma dake akwai kulawa kwanciyar hankali da nutsuwa kuma ana mishi kome ko wurin had'a magungunan shi baya fita anan ake mishi kome, tun ranar da abin ya faru Reshmah bata kwana a gidan da akai ta ba, amma kuma zaman babu dad'i. A wannan daren da sukayi abin da ya faru duk shirinsu ne. Ita da Yaranta shi Aseem yana tare da Yazid babu abin da ya sani.

***
Niamey.
Tunda farko da ace ta san matsalar nan na shi tabbas ko zata rasa rayuwarta ba zata tab'a barin shi da ciwon ba, "Hajiya!" Salamatu ta kira sunanta. "Na'am!" Ta amsa a sanyayye, "Shayin yayi sanyi." "Tow!" A hankali ta dauki kofin ta kurba kana ta d'ago kai tana kallon Salamatu. "Hmmm! Alhaji ya tashi ne?" "Eh yana dakin motsa jiki." Ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta ce mata. "Shi kenan jeki." Juyawa tayi zata fita Hajiya ta ce Mata. "Salamatu Aryan fa?" "Tun dazun ya shigo suna tare da bakon Marad'i." Murmushi tayi sannan ta ce mata. "Shi kenan na gode." Tana fita magani ta dauka ta sha, sannan ta dan kishingid'a tana kallon gefe guda. Wani irin sakaci tayi da rayuwar Majid ya lalace haka. Hawayen da ta gaza tare shi yake zuba mata, tana jin kamar tadau ciwon a jikinshi ta dorawa kanta, bata son ta ce bata yafewa Alhaji Mamman Ba'are ba, amma tabbas shi ya lalata mata nata rayuwar da har haka ya shafi na wanda bai ji ba bai gani ba.
Chapter 51 · 0% Book details