← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 138

Sashe 37

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Watan su daya da rabi suka dawo an gama gyaran gidan har an zuba kome na gidan, daga cikin gidan zaka shiga asalin cikin gidan baki daya, shi dai Majid ya ware layinsu baki ɗaya don abin da yake faruwa babu wanda ya shiga musu. Bai bar kasar ba sai da aka yi bikin kannenshi, sannan ya saka Aryan ya dawo da Matarshi kusa da Hajiya inda shima ya cire flat me kyau aka mata, suka zauna lokacin tana goyan d'anta Abdul.
Tunda ya bar kasar bai kuma waiwayonta ba, tsawon shekaru shida. A wannan shekarun babu ranar da Hajiya ba zata tafi niman shi ba, ko tasa a nima mata shi ba, sai gashi wannan karon Aryan ya dauko mata shi a kai.
Wannan shine labarin Hajiya da Yaranta.
-------------
Mu dawo labari.
-------------
Sansanin Yan gudun hijira..

Wato kun san meke faruwa a cikin sansanin gudun hijirar da muke kuwa? Hmmm wato wani murdadden al'amari ne, adamawan Kamaru tana iyaka da Nijeriya da nijar ta yamma, sannan ana smuggling na kwayoyi safara da yara da mata, wasu ana tura su cikin kamarun, wasu kuma a tura kasashen Afrika da turai.

Sannan babban wani abun mamaki ta hannun Uwar mugu ake wannan aikin, sannan asalin miyagun kwayoyi da makamai, ana shigowa da sune ta nan ana shiga da shi Nijeriya da nijar.

---- Kwana muka yi muna hira da Zuzu da Ummi Addah bata dawo ba, sai wurin asuba ta dawo tana kuka wiwi. "Addah lafiya!"shigowa da Munaisah aka ayi dakin kamar bata da lafiya ko taci duka. "Allah yayiwa Nenne rasuwa?" Tashi zaune mukayi. Murmushi Ummi tayi ta ce mata. "Hankalinku ya kwanta "
"Me kike nufi? Babu kowa a wurinta sai Munaisah naje domin na tayata zama ne!"
"Ya isa Addah" inji Zuzu, wallahi duk sun saka ni cikin duhu. "ina gawar?" "Tana can ana mata sutura" nida Zuzu muka fita, Ummi ta kalli Munaisah ta ce mata. "Daga nan karatun daya ce har birnin lantsandaal, kin biyewa Addah kun kashe Mahaifiyarki, ki rubuta ki ajiye. Addah sai ta ci amanarki wallahi kuwa sai ta saka ki kuka lokacin babu Zahra da zuzu, matukar zata sayar da Yarta ke din banza ce ba zata iya miki butulci ba. Na tausaya miki matuka gayya."
Tun bayan an yi jana'izar aka kaita makwancinta, da zamu koma Balali ya kirani ya ce min."don Allah ina son magana dake."
"Ok me ya faru?"
"Ki saka idanu akan matar da take dakinku da ita wancan me cikin." Hadiye yawu nayi, na ce mishi. "Lafiya kace haka?"
"Kiyi hakuri anan sansanin tunda wancan gayen yazo tow wallahi numfashin ki ma da zai saya tow tabbas zai saya ya samu kuɗi."
"Me zan iya yi?" D'ago kai yayi ya ce min. "Jeki zan baki sako!"
Haka na juya na tafi sai lokacin na lura ashe Uwar mugu ya gani. A hankali muka hadu da ita ta ce min. " Me yake gaya miki?" Murmushi nayi nace mata. "Ta'aziya yake min."
"Bayan nan bai ce wani abu?" Girgiza kai nayi nace mata. "Haba bai ce kome ba!" "Zahra'u kenan! Mu shiga ki karya." Girgiza mata kai nayi ina faɗin. "A'a na koshi."
"Muje mana, ko an gaya miki wani abu ne?" Ganin tana son daura zarginta akan Balali yasa ni binta har dakinta, muka zauna ta shiga zuba min abinci da kayan ciye-ciye. Duk abinda ta zuba min sai da na raba biyu tana kallona, tana gamawa na ce mata. "Muci tare."
"Kin xata zan saka miki guba ce?" Girgiza kai nayi nace mata."ko daya kawai muci tare wannan zan kaiwa Zuzuna."
"Tow muci" haka muka ci tare da ita, sannan na mike ta kara min abincin. "Kina da wani irin kyau, kiyi amfani da kyan nan mana." Girgiza kai nayi nace mata. "ai kyauwa na muni ne ga wancan abin"
"Kina son zuzu ko????????? "
🤔🙄Me ya kawo irin wannan tambayar... Jama'a me uwar Mugu take nufi.
#Thedambuje
[2/19, 12:21 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*

{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu

Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci.
Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE.
_______________________
MARKADADDIYAR GYAD'A
HADADDEN KAYAN SHAYI
GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA.
GARIN TUWO
GARIN KUNU YAR ASALI
CURRY ME DADI
SPICES
TYME
YAJIN DADDAWA ME KYAU
GARIN DAN WAKE
JAN YAJI MAI DAD'I...
_____________________
BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA.
ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA.
WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU.
ZAKU IYA TUNTUƁARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590.... MUNA DAKON SAYAN DAI-DAI KO SARI.....

*018*
"Na'am me kike ce?" Na kalleta cikin son fahimtar me take nufi, murmushi tayi tana kallona. "Kawai naga yadda kike damuwa da ita ce ko mahaifiyarta bata damu da ita haka ba, kin ga wannan wuri da kike kowa ta kanshi yake, ki ajiye wata Zuzu ki kama Harkar gabanki yafi miki."
"Ban damu da ko waye bai damu da zuzu ba, amma ni a raina na damu da zuzu. Sannan ba zan dauki wani ya dora ni akan hanyar da ba zata bulle min ba,, idan Addah ta gadama ta kula da rayuwar Yarta idan bata gadama ba, ta barta tai yadda take so. Ke da ita baku isa tilasta ni yin abin da ban shirya ba, idan kuma kina ganin zaki iya Bismillah. Har karshen rayuwata ba zan daina tsayawa a bayan zuzu ba kin ji na gaya miki sai ki san nayi." Daga haka na juya tare da barin mata dakin ko abincin ban dauka ba.
"Abincin da kika bar min fa?" Ban juyo ba, na ce mata. "Kece idan baki ci ba zaki mutu, ni kuwa ko banci ba zan rayu matukar Allah shine rayayyen nan da baya mutuwa."
Sannan na sa kai zan fita, ta kuma ce min. "Kada ki d'aga kafarki domin zan iya aikata kome." Juyawa nayi na kalle ta dariya nayi nace mata. "Ni ban san tsoro ba, ki gaya min taya zan san tsoro bayan akan idona aka kashe min dangina? Gaya min tsawarki bai wuce haushin dan kwaikwayo ba. Ni gurnanin fitar rai naji kin ga kenan babu abin da zai bani tsoro bayan nasan ina raye ne ko na mutu don Allah, ko a kashe ni don niman duniya." Daga haka na bar mata gidan, Yana kwance yana jin duk abinda suke fada, a ina aka samu yarinya me zuciya haka, Aina'u ya kalla da take ta sharar bacci, ya mike zaune yana mika, kirjinshi cike da gargasa ya dauki dogon wandonshi ya saka. Ya fito inda Uwar mugu take zaune tana mamakin maganganun Zahrah. " A ina kika samo jar wuya haka?" "Yan gudun hijira ne da suka taso daga Nijeriya, za akai su sansanin gudun hijirar hadin gwiwa da na Nijeriya yaranmu suka karkato mana da su nan, Yaran jiya da ka gani duk daga can suke."
Shafa kanshi yayi yana faɗin. "Yarinyar ta iya jefa citta a bakin mutane, ban tab'a jin yarinyar da ta gaya miki gaskiya haka ba." Sosa kanta tayi tana murmushi ta ce mishi. "Eh ai bata da kunya ko kaɗan. Haka yar Ubanta take fama da ita, taurin kai ne da ita kamar arnan dutse."
"Nawa aka samu domin ina son wucewa da shi kafin lokaci ya kure min." Sunkuyar da kai tayi tana faɗin. "Ba a wani samu dayawa ba, amma zaka iya zuwa wurin ajiyar zaka ga iya wanda muka samu." Gyada kai yayi yana faɗin. "Duk bayan wata shida nake zuwa amma ace iya wanda na samu kenan? Babu waɗanda suke jinya ne?" Kasa tayi da murya tana faɗin. "Allah ya baka hakuri, akwai Aina'u anan!" Shiru yayi kafin ya ce mata. "A nemo min nan da sati xan wuce na gaya miki."
"In sha Allah, amma akwai yaron nan Balali da Dilla ya kawo mana shi, yana son ballo mana ruwa."
"Ki saka a kawo min shi naji hujjarshi na lalata min dagiya ta."
"Yarinyar da ta fita suna tare."
"Nace a dauko min shi, ita kuma a tadata tabar min daki kafin fushina ya sauka har kanta." Da sauri ta nufi dakin ta tada ta, suka fito domin idan ya fadi haka rashin Imanin shi ya motsa kenan. Tana fita ta nufi kofar da su Balali suke aiki, ta ce. "Ku rufe kofar nan." " Tow!" A take suka rufe ta ce musu."ku kama min dan iskan cen ku kaiwa yallabai."
Bai gudu ba, ya tsaya suka kama shi har gidanta, ajiye shi aka yi gaban shi. Kanshi a sunkuye. "Kai me ya haɗaka da yan matan da suke wannan sansanin?"
"Ayi hakuri yallabai ba zan sake ba." "Hmmmm ba zaka sake kula su ba ko ba zaka sake wani abu ya fita daga bakin ka ba." "Dukka biyu yallabai." Gyada kai yayi yana faɗin. "Idanuna yana kanka, nan da sati biyu zan bar nan ka sake wani abu ya faru." Wata ƙatuwar wuka ya ciro, yana wasa da ita kafin ya ce mishi. "Da shi zan kashe ka."
"In sha Allah, ba zaka kara kama ni da wani laifi ba."
Haka ya bada hakuri sannan aka kyale shi, wani abin mamaki murmushi mutumin yayi bayan ya fita. "Me yasa baka kashe shi ba?" "Akwai abin da na karanta shi me dabi'ar Dilla ne bada hakuri akan kuskure wanda ya aikata da wanda bai aikata ba, wannan yaron dila ne. Kin san dai wannan wurin an gina shine da ra'ayin mutane mabanbanta, shi kin san aikinshi da abinda yake so, ni kin san aikina da abinda nake so, idan na ce zan kashe shi. Zan lalata goma daya bata gyaru ba, madadin na kama shi sai nayi rashin sa'a.
Chapter 37 · 0% Book details