← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 138

Sashe 44

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Haka muka cigaba da tafiya har sai da muka ji babu dad'i, domin wasu sun tafi, bamu tsaya ba sai da rana ta faɗi, a wani ƙaramin gari, tun kafin mu shiga garin na fahimci mutanen garin suna maraba da zuwanshi, garin dauke yake da kabilu biyu, hausa da fulani, domin ga alamu sune suka kafa garin. Sannan kowa ka gani yana da abin yi, ma'ana Babu wanda zaka gani yana zaune haka. Gaishe shi ake yana amsawa har muka bar cikin kauyen muka kara nausa daji, anan ne na fa kara yarda Allah daya gari Banban. Dajin da muka nufa gona ce ni nace lambu, babu irin shukar da babu a cikinshi, sannan akwai cigaban zamani. Lokacin da muka isa wucewa damu aka yi wasu gidajen da suke zagaye da wani gida can, gaba da gidanshi. Yanayin gidan kamar irin dakunan kwanan dalibai ne, gado da katifa har da bargo. Kwanciya muka yi barci yayi gaba damu.
***
Niamey.
Suna kwance wuri guda, hannunsu sarkafe da juna. Kana ganinsu kasan lovers ne na gayawa yan gari. "My heart meke damunka?" "Hmmm! Kudi naje hajiya ta bani ta hanani, raina a b'aci na zo nan." Shafa kanshi Sajjid yayi yana faɗin. "Kamar nawa?" Mikewa yayi yana faɗin. "A'a ka barshi zan tafi na sayar da motata." "Kana dani kace zaka sayar da motarka, baka yarda ina sonka ba ne? Kasan yadda iyayenmu suke gaba da juna amma kake tsammanin zan iya rayuwa babu kai? Ko wancan mutumin gidanku ba zan tab'a yafe mishi ba."
"Idan na yafewa kowa, Majid ba zan yafe mishi ba, sai na saka shi biyan abinda ya aikata." Sai da Sajjid ya gama hasala Amaan Mamman Ba'are, sannan ya dauki kudi masu yawan gaske, ya bashi ya kai hannu fuskarshi. "Kayi hakuri nasan Aryan da Majid yan uwanka ne, amma ina matuƙar jin haushinsu, ina ta kokarin koyawa kaina dauke kai akansu amma na kasa. Ka gafarce ni." Sajjid ya faɗa kamar zaiyi kuka, a rikice Amaan ya rungume shi. "Zan taya ka lallubar hanyar da zamu ga bayansu."
"Allah!"
"Da gaske zan iya kome matukar zaka yi farinciki." Murmushi Sajjid yayi yana faɗin. "Ban yarda ba, don na baka kudi kake fadar haka." Mai da mishi kudin yayi yana faɗin. "Bana bukatar kuɗinka, lokaci zai nuna maka ina sonka ne don Allah ko kudinka."
Murmushi Sajjid yayi yana juya idanu ya ce mishi. "Dauka ka tafi nasan kana sona ne don Allah, wasa nake maka." Ya fada yana cusa mishi kudin tare da mishi chakulkuli. Dariya suka saka bakiɗayansu. Sai da suka yi wanka sannan Sajjid ya raka Amaan har wurin Motarshi ya bar gidan, kiran Mahaifiyarshi yayi yana faɗin. "Jakin yaron nan ya faɗa fa!" Ajiyar zuciya Tani tayi ta ce mishi. "Ban yarda zai iya mana wani aiki ba, ka dawo haka ina son ganinka."
"An gama!" Ya fada yana shafa ciwon da yake goshinsa. "Kada ka dauki lokaci." "Tow." Ajiye wayar yayi yana hararar shi, tabbas idan ya samu hali sai Hajiya Tani ta biya abinda ta aikata, ba ita ta haife shi ba ko ita ta halicce shi sai ya mata abinda ba zata manta da shi ba, kuma yanzu ma zai cigaba da mata biyayya. Tun yana Yaro take azabtar da rayuwarshi har girmanshi bai huta ba, yanzu ma don yana da abu me muhimmanci ne ya barta take raye. Yasan duk wannan fadi tashin da yake ba don kanshi yake ba, iya ita kanta yake mata, sannan shu'umar mace ce ta gaske da ba zata iya daukar rainin hankali ba, yasan ita ce ta haife shi, amma baya tunanin zata iya d'aga mishi kafa, idan ya mata kuskure shi yasa a duk lokacin da yayi kuskure da girman shi sai ta illata shi.
Shi kuma a nashi tunanin yayi girman da dole ta daina dukarshi, domin yau da gobe ya wuce wasa, sannan ba zai cigaba da zuba mata idanu tana dukar shi ba.
Chapter 44 · 0% Book details