← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 138

Sashe 100

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tare da hoton Zahrah, ya ce lallai ayi wani abu kafin ya iso dake mutum ne mai matsayi da kuma girmamawa sai gashi jakadar Algeria a nijar ya samu damar tura sako ga primemininester, kafin wani lokaci an kafa dokar bincike ko ina a fadainrgarin.
* Ana cikin Birthday party sai raba idanu Majid yake yasan tabbas zata zo, haka yasa shi sankankancewa. Shiru da yaji ne yasa shi damuwa yana kallon kowa, Umaima da suka zo nasu harkar lafiya, yau tana can tana kallonshi kamar a dame yake. Da sauri Amaan da Aryan suka shigo Aryan yana rike Amaan, yana kwacewa. Mika mishi tap din hannun shi yayi yana faɗin. "Sajjid ya sace Fadima." Shigowar Motar yan sanda gidan ne, yasa hankalin kowa ya koma kansu. Nan suka iso har gaban Majid, tare da mika mishi hannu. "Yallabai kana da labarin an sace sakatariyarka?" Zufa ne ya shiga yanko mishi, tare da kura musu idanu. Amsar tap din yayi ya ga hotonta da motar da aka sace ta. "Wannan motar mallakar Iyalin Mamman Ba'are ne ko?"
"Eh na gode sosai, kuyi iya ƙoƙarinku mu ma zamu tuntube ku idan wani abu ya taso."
Karfin hali ne yasa shi yin magana, amma ba wai yana da zuciyar magana ba ne, kallon Aryan yayi ya ce mishi. "Tunda wasu abubuwan ke faruwa baka tab'a gaya min kome akan motar da aka sace ba, Aryan me kake kokarin aikatawa?"
"Me zan aikata wanda zai tab'a kimar gidan nan, motar nan an sace ta kusan shekaru biyu kenan, yau nima nayi mamakin ganin shi."
"Aryan ka sayar da motar ne?" Haɗiye yawu yayi tare da sunkuyar da kai ƙasa. "Bani da zaɓi ne, na bawa Sajjid koyar."
"Me yasa ka bashi motar da ni kaina hukumar tsaro ne suka ba ni."
"Barazana suka min na daukar Abdul Majid shi yasa na basu motar."
"Me yasa baka gaya min ba?" Shiru yayi ya sunkuyar da kanshi. "Bana zarginka amma ka sake na zarge ka, garin nan sai yayi mana kaɗan."
Hankalin kowa ya tashi, kafin wani lokaci an fara ture-turen hoton Zahrah. Ita kan Hajiya kasa magana tayi, har suka shiga cikin gidan, Umaimah ta amshi wayar Jamilah tana kallon Zahrah duk da ta sauya amma ba zata mance fuskarta ba.
"Captain dama ka samo Zahrah Buba ce?" Cak ya tsaya da hawa Step. "Yes ita ce Yarinyar da kake nima, yarinyar da bata jininka, ita ce dai a tare da kai." Iska ne ya cika mishi huhun shi, ya kasa gaba balle baya, ya kasa motsin arziki. Akwai wani abu da yake ji na daya muryarta na biyu wani irin abu yake ji a jininshi a duk lokacin ya ganta bai tab'a zata jininshi da yake yawo a jikinta ne yake saka shi jin kamar ya santa da jimawa ba.
Kasa magana yayi ya kai minti ashirin a tsaye kafin ya wuce dakinshi, ya zube a saman gadon, wannan shine an bata goma daya bata gyaru ba. Zumbur ya mike tare da nufar kofar fita daga gidan. "Ina zaka Hamma akan wannan karuwar yarinyar zaka b'ata lokacinka ne?"
Juyawa yayi a fusace ya buga mata harara, tare da wani irin kallon tsana da takaici. " Kika sake kiranta karuwa sai na fasa miki baki, sakarya kawai." Yayi ficewar shi, gidan Tani ya shiga ya samu zata fita daga gidan kenan. Zuwa yayi ya bude motar ya zauna yana murmushi. "Da alamu ba ki ja kunnen d'anki ba?"
"Ban san kome akan satar Yarinyar ba."
"Ki kira shi a duk inda yake ya saki yarinyar, ko ya fadi inda zan dauke ta. Amma ki gaya mishi ya mika kanshi ga hukuma domin zai samu sassauci ni idan na same shi sai dai Raihana ta haifi wani."
Tani bata yi wasa da Kalaman Majid ba, a take ta kira Sajjid. "Don Allah ka sake mishi sakatariyarshi."
"Ni ina ruwa na, yaje ya samu wanda ya sace mishi ita." Wayar shi da yake hannun shi ya tura sako office din bincike, tuni aka gano inda Sajjid din yaƙe. "Ka dawo mishi da ita domin motar nan ta kace, ka dawo da ita kafin kome ya tonu."
"Sai kuyi!"
Fita Majid yayi a motar, ya nufi cikin gidan su yana waya. Ya nufi cikin gidan su ya samu ana ta nanata abu daya, haka yasa shi wucewa sai kuka Zaytoonah take tare da cewa. "Sai ka gaya min meye nayi maka baka sona?" Banza yayi da ita tare da bin shi da gudu, bai kulata ba don yasan cewa bai da lokacinta. "Wallahi sai ka gaya min."
Kura mata idanu yayi kafin ya ce mata. "Bana sonki,ban tab'a kaunarki ba. Ban tab'a jin ko dai-dai rana daya na so ki ba ni kanwa na dauke ki ai na gaya miki tuntuni zuciyata na wata ce. Tow akan me xan damu kaina na lallai sai na gaya miki karya ki je ki nemi wanda ya miki amma ni bani da lokacinki."
"Me yasa ka koya min sonka?"
"Munafuka an tab'a so dole ne yau naga danyen jaraba. Baya sonki sai me? Yau naga jaraba, hehehe Alhajin Allah don dai ka hana ni saka maka baki ne .maganar ka amma tun yaushe na gano Ariyan kasungurmin munafuki ne, dan iska idanu kamar matsatsaku."
Shi kan fita yayi tare da amsar wayar, "Alhamdulilahi" ya furta. "Nana an kama jikanki wanda ya bada motar da aka sace ta. Ina zuwa."
Bakiɗaya kwana zaune aka yi, Hajiya kallon Aryan take haka matarshi kuka take tana faɗin. "Me yasa ka rusa yardan da nayi maka. Aryan me yasa ka zubar min da kimana bayan ban maka kome ba. Yan uwanka sun yarda da kai amma ka lalata wannan yardan, idan har zaka iya munafuntar yan uwanka tabbas zaka iya kashe ni har da Yarana."
Ta fada tana kuka, Hajiya kuwa tasan waye Aryan ba zai tab'a yin haka ba tare da dalili ba. Ta jima da sanin yana boye mata wani abu, amma bata kawo a ranta cewa wannan abin ne ba. "Yanzu ka kyauta kenan." Mikewa yayi a fusace ya mari Amaan. Sai da falon yayi tsit ya kuma d'ago hannu zai kai marin Hajiya ta ce mishi. "Kyale shi haka."


Yazid .
A daren ya bar ƙasarshi don yasan babu nisa da nijar amma a haka sai asuba Suka shigo garin, koda ya iso abu daya ne shine basu agogon hannunshi da ya ce musu. "akwai agogo a hannunta matukar yana hannunta za a iya gano inda take." Wasa wasa sai gashi an samu inda take, suna hanyar Libya da Nijar. Haka yasa shi tashin jirgi. Tun tafiyar da yayi ya saya musu agogon iri daya, sannan aka sawa agogon tracking. Haka yasa shi gaya mata kada ta ajiye shi ya zama yana jikinta ko wani lokaci bacci ne kawai zai rabata da agogon. Ya kuma san zata yi hakan. Sannan da Nawwas yasan da agogon ba zai yarda ya bar kasar da ita ba.

Soji da yan sanda suka dauki hanyar, yayinda Majid da yan sanda suka bisu Yazid kan da yar ƙaramar jirgin sama aka dauke shi, ana bin inda suke. Da fari Nawwas yaso yayi lalata da Zahrah kawai ya sauya ra'ayinsa don kada a samu matsala, tuni ya tura hotonta akan manhajar su, yan iskan attajiran turawan nan na gani suka ce tayi musu aka fara saka kudi a kanta, haka yasa shi tattara kudi me yawa gara ya sayar da ita kowa ya huta, ya saka Yazid b'acin rai. Haka yasa shi nufar Libya daga can ya bi teku da ita dake akwai kayan safarar shi.

Cikin minti arba'in da wani abu aka same shi. Yana kan iyakar zai fita da ita, garin bincikar motar da suke fita ya tsaya bin layi, har Yazid suka iso. Lokacin da ya gansu ne ya san ba makawa sai sun kama shi.
"Waye ya tsaya miki?" Ya fada bayan ya damke gashin kaina. "Allah mana, ban da Allah waye zai tsaya min?" Murmushi yayi sannan ya ce min. "Idan na kashe ki ke daya, ban ci raba akan wancan dan iska ba amma idan na kashe ku dukkanku ku biyun fa?"
Chapter 100 · 0% Book details