Sashe 24
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
"Shi mutumin da ya kwanta dake a dakin asibiti fa?" Kura mata idanu nayi, baki daya sai naji abincin ya fita kaina. Na rufe a hankali nace mata. "Ki raya duk abinda yake ranki haka shine daidai." Na fada mata ina murmushin takaici. Mikewa nayi ina karkade hannuna. "Zahra'u kina boye min abubuwa dayawa, sai dai nice uwar baki uwar magana, nayi ta gaya miki sirrina." "Me kike so nayi miki? Ni nasan ban boye miki kome ba, kuma iya gaskiyar kenan na gaya miki me kike so bayan haka?" Shiru tayi tana kallona, kafin tayi kasa da murya ta ce min. "Ina wannan lokacin da muka hadu da wani dan Yola ya zo seminar?" Gyad'a mata kai nayi, a ranar da ya zo cin tuwo ya roke ni na bishi, koda muka je bai yarda mun wuce masaukinshi ba, tambaya ta yayi asibiti muka je, a daren ya kai ni wurin likita aka duba lafiyata, da nashi domin yace baya son yayi mu'amala da macen da take dauke da wata lalura shi asalima Haihuwa yake nima, Allah ya bai bashi ba. Kuma yana da mata huɗu babu wacce Allah ya nufeta da haihuwa. Bayan an gama mana ne muka wuce masauki, kusan dukkan kwanakin da muka yi da shi. Ba zan iya mantawa ba, duk da sabon Allah ne amma kuma abubuwan da suka faru ba masu mantawa bane, bayan ya gama kwanakin shi zai tafi ne ya bani number shi akan idan wani abu ya taso na gaya mishi sannan ya roke ni da cewa kada na bi wani namiji na tsawon wata uku. Ban tab'a haduwa da wanda yake zuba min kuɗi kamar hauka irinshi ba, haka nayi ta bawa Addah kudi ina tafiya na kwana a hotel gudun kada tace na bi wani namijin, wata biyu da tafiyarshi ne na fahimci ina da ciki, na tura mishi sakon da kwanaki da test da aka min, kin san wani ikon Allah sakon ya same shi dai-dai zai bar kasa ne, amma a ranar ya turo min kuɗi da duk wani abun bikata, ya kuma roke ni naje gida na gayawa Baffa zai zo niman aurena. Tun lokacin na rasa yadda zan gayawa Addah, har cikin ya shiga wata hudu,ina boye mata kwatsam sai ga abin da ya faru nan muka tawo jenuwa, ashe Allah bai nufa zamu sake ganawa da shi ba ne." Ta fada cikin wani irin kuka, kasa magana nayi ina kallonta, kafin na d'ago kai....
#Thedambuje
[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*
{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*012*
Wani lokaci kana iya ganin abu amma don a zauna lafiya zaka iya makancesa sai a zauna lafiya, ba tare da an cutar da juna ba. Kusan hakan ne ya faru idan da ace na d'ago kai na kalli abinda Addah take min sai nace hakkina ya kama Zuzu amma idan na duba yadda itama zuzun Addah ba kyaleta tayi ba, sai naga ashe ba kome bane don tayi min wani abin, tunda 'yar da ta haifa ma bata kyale ba. Irinsu Addah a cikin al'umma masifa ce matukar zaka nemo kudi tow bata da matsala da kai, kaunarta da kudi yasa bata jin ko dar, zata iya aikata kome matukar zata samu kuɗi, babu abinda ya dame ta. "Kin yi shiru!" Ta faɗa tana share kwallar da yake zubo mata. "Tow Zully me zance? Ina ga a gayawa Addah maganar cikin ki, domin bana son na samu matsala da Addah."
Mikewa tayi kamar maganar da nayi ya bata haushi, ta juya zata bar wurin na sha gabanta."Ban fadi haka saboda na b'ata miki rai ba, amma idan kin ji haushi kiyi hakuri kin ji " hawaye ne ya zubo mata, tana min wani irin kallo me cike da tausayi, tsarguwa nayi na juya baya. "Zan mutu ne?"
"Ki min alƙawarin ba zaki barshi yayi maraici ba." Rufe mata baki nayi ina faɗin. "Kina saka zuciyata wani irin bugawa, don Allah ki rufa min asiri, bani da kowa sai ke." Cire hannuna tayi ta daura bisa cikin ta ce min. "Sai wannan kina da wannan, in sha Allah zan zauna a gefenki." Komawa muka yi wurin zaman muka zauna. "Me yasa ranar da Baffa zai baki addu'a baki gaya mishi ba?" Hawaye ya zubo mata, ta share tana faɗin. "idan na gaya mishi zai tsani yar uwarshi a tsarina bana son a tsane ta da wuri, na fison sai na mutu za a tsane..." Rufe mata baki nayi ina faɗin. "Duk lalacewarta mahaifiyarki ce, kada don abin da take yasa zaki so duniya ta zage ta, kiyi hakuri wata rana sai labari."
Kamar zata ce wani abu sai kuma tayi shiru, "kin ci abinci ma kuwa?" "Na koshi!" "A'a Maman Unborn zauna kici idan bai isheki ba, a karo miki." "Ni fruit nake so." Shafa fuskata nayi, sannan na juya na fita kasancewar gari ne masu yalwar ya'yan itace, ban sha wuya ba asalima ina zuwa wurin na samu Doctor Andrew zai saya sai ya biya mana kudin, duk da ban so ba, amma haka na amsa ina mishi godiya, na kawo mata, yadda take yasa na zuba mata idanu. Da alamu ranta yana son ya'yan itacen domin yadda take ci kamar tana ci da wani. Murmushi nayi nace mata. "My heart yana son abincin da kike ci." Girgza kai tayi tana faɗin. "Mace ce!" "Are you sure?" Gyad'a kai tayi tana faɗin. "Na rasa ma me zance, ke bakya tsoron wani abu ya faru ne?" Dariya nayi tare da mika na ce mata. "Bana tsoron kome, yaushe Munaisah zata zo, barci nake ji bakidaya jikina ciwo yaƙe."