← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 138

Sashe 30

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Assalamu alaikum barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya, karku manta da wannan Kamfani mai albarka mai kawo muku kayan bukata cikin sauki da Aminci da Inganci.
Wato TA RASULU MULTIPURPOSE. YA SAKE DAWO MUKU DA KAYAN NAN MASU ARMASHI DA DANDANON KOWACCE MACE TAURARUWA CE.
_______________________
MARKADADDIYAR GYAD'A
HADADDEN KAYAN SHAYI
GARIN KOSAI NA TAFI DA GIDANKA.
GARIN TUWO
GARIN KUNU YAR ASALI
CURRY ME DADI
SPICES
TYME
YAJIN DADDAWA ME KYAU
GARIN DAN WAKE
JAN YAJI MAI DAD'I...
_____________________
BUGU DA KARI MUN TANADAR MUKU DA KAYAN FITAR SALLAH DA NA SHAGALIN SUNA DA BUKUKUWA.
ATAMFOFI, LESHINA, MATERIAL, SHADODDI, YADUDDUKA NA MAZA DA NA MATA, JAKKUNA DA TAKALMA.
WANI ABIN SAI KUN ZO TA RASULU MULTIPURPOSE DOMIN KASHE KWARKWATAN IDANU.
ZAKU IYA TUNTUƁARMU A WADANNAN NUMBOBIN.. 08086639163 - 09030168590.... MUNA DAKON SAYAN DAI-DAI KO SARI.....

*015*
A bangaren Nana ta dai sassauta kiyayyar ta ne don, iyayen Sa'adatu babu wanda ya isa ya kawo musu raini sannan daga mazan dangin har matan kana ganinsu kaga wadanda suka san ciwon kansu, ga wanka da matan suka yi na arziki zaka fahimci sun tashi cikin arziki da wadata domin gwala-gwalan da sukayi kwalliya da su, bayan tafiyarsu ne ya fara ginin part din Sa'adatu ya zuba mata kome nata, da zai tafi wurinta ya dauko mata yan kunnenta babban set da karami ya kai mata,
A lokacin da laulayi nata yayi sauki kenan, haka ta rike shi da daraja, bai gayawa kowa Sa'adatu tana da ciki ba, amma yadda yake lissafin zata haihu bayan sun gama jarabawa zai kaita wurin danginta ta zauna sai tayi arba'in ya dawo da ita. Haka kuwa aka yi domin suna gama jarabawa, ya zo ya zauna ko zata haihu amma ina shiru haka.yasa shi daukarta suka tafi kasar Iyayenta. Lokacin da ta ganta a cikin danginta. Ranar kwana tayi tana kuka tana jin wani irin son danginta..ga iyayenta ga Abbati sai shiga da fita yake yana kawo mata abinci da ta ce tana so.

Shi kanshi Alhaji Mamman Ba'are sai da yaji wani iri domin kuwa yarinyar ba tsarar shi ba ce, don Abbati ya nuna mishi wanda aka so ta aura, yaro ne Matashi amma haka ƙaddara da rabo ya shiga tsakani. Ranar da suka isa a daren ranar ta haifi d'anta namiji, babu wanda yasan tana nakuda, tsabar kunya da wauta.
Yafendo mahaifiyarta tana dakin Mallam mahaifinsu, suna sallar nafilla da mallam wanda suke kiran shi Babaji, taji kukan jariri, bata yarda kunnenta ya jiyo mata ba, sai can ta kara jin kukan. Ai sallama tayi ta nufi dakin ta, anan ta samu Sa'adatu da Kanwarta Kabo, an rasa wanda zai yi wani abu, sun saka Baby a gaba. Dariya abin ya bata ta ce. "Danejo jaririn kuka kasa a gaba. Keda kabo shine baku fita kun kira Sumai ba?" Tana jingine da gadon, tana sauke ajiyar zuciya. Bata ce kome ba, itama Yafendo fita tayi ta kira Sumai, Uwargidanta kenan, ita tazo ta gyara Babyn tsaf, ta wanke Sa'adatu a lokacin, sannan suka saka turaren wuta, domin ita Sumai fulanin chad ce, tana harkar turaren wuta. Kafin wani lokaci gidan ya cika da kamshi, Sa'adatu ana kiranta danejo, Babaji yana kiranta da Hajiya. Kasancewar sunan Mahaifiyarshi ce kuma Hajiyar ce da gasken gaske.

Da asuba aka gayawa Alhaji Mamman Ba'are, Hajiya ta haihu.don da fari bai fahimci wacece Hajiya ba, sai da Alhaji Nasiru Wodabbe ya zauna ya mishi bayani, sai ya gane ya kuma ce musu. "In sha Allah Hajiyarta za a kirata.". Haka ya fita Masallaci, ya shiga gidan don ance mishi ta haihu amma basu gaya mishi me ta haifa ba, sai da ya shiga Sumai take murmushin farinciki ta ce mishi. "An samu da namiji, ango ba cefane." Zubewa yayi a kasa ya zuba sujudul shukur, kafin ya fashe da kuka, aka mika mishi Yaron, jikinshi yana rawa ya fito da yaron har gaban Babaji, ya ce mishi."ka saka mishi sunanka." Murmushi Babaji yayi ya amshi yaron ya mishi huɗuba, a madadin yasaka mishi Aliyu, sai ya saka mishi Abdul Majid. Ya mika mishi. "Gashi nan Abdul Majid, kukan ya isa haka. In sha Allah zai zame maka fitila a duk wani Mabudin alkhairinka." "Mallam baka saka sunanka ba?" Ya faɗa hawaye na zuba mishi. "Suna na ba shine mai muhimmanci ba, sunan da zai zame mishi alkhairi ake bukata."
Malam yaji dadin wannan kara da Alhaji Mamman Ba'are ya mishi, shi kan kuka yake tayi, don gani yake kamar ba dan shi bane, har asibiti aka kai Yaron aka duba lafiyarshi. Sannan suka dawo kwanan shi biyar ya dawo Nijar ya gayawa Nana ai Sa'adatu ta haihu, bata wani damu can ba, sai da ya ce mata namiji ta haifa shine bayan suna suka je ita da Hadiza da Harirah. Ba karamar hidima aka musu ba, duk iskancin Nana da wulakanci sai da ta rena kanta, domin tazo inda ake magana ta arziki wato kudi kumbar susa. Domin su suka je Barka, sai gashi sun dawo da kayan arziki niki-niki. Madadin haka ya janyowa Sa'adatu farinjini sai tsanarta ya kara cika zuciyar Hadiza da Nana, ita kan Harirah tun farkon ganin Sa'adatu da hakorin hajji jikinta ya bata daga babban gida ta fito, shi yasa bata wani takurawa kanta wurin kishi me zafi ba.

Watansu guda suka dawo kano da kaya niki -niki, suka cigaba da zuwa makaranta. Da dattijuwar da tazo da ita daga garinsu me suna Inno, ita tayi ta renon Abdul Majid har suka yi arba'in da wasu satika sannan Inno ta koma ita kuma ta cigaba da karatunta, sai da suka yi wata hudu sannan suka tafi marad'i, kwanansu uku suka wuce Niamey. Wayyo rawar kai a gurin Alhaji Mamman Ba'are ba acewa kome, haka tayi musu sati Uku. Don zasu koma makaranta kuma har cikin azumi suna karatu. Haka da zata dawo Alhaji Mamman Ba'are yayi ta mata hidima.
Har suka dawo, kaunar da yake nuna musu ya janyo mata bakin jini, haka suka yi ta jigilar karatu ga danginta daga garinsu ana yawan mata aike, lokacin da Abdul Majid ya cika shekaru biyu, suka tafi Umara da shi, Abbati ya biya mata da Abdul Majid. Lokacin sun samu hutu koda suka dawo, Nijar suka sauka a can ta huta domin lokacin zata shiga aji hudu ne, ga zata tafi IT, wannan zuwan ta fahimci kamar bayan son ganinta har ta gama hutun zata koma, ya zo domin sau biyu suka hadu, da zata koma ya mata kome, ya ce kada ta kuma zuwa Nijar.
Tunda ta dawo bai kuma waiwayonta ba, Allah ya so Abbati baya wasa da zuwa ganinta duk bayan wata uku, bata taɓa gaya mishi tana cikin matsi ba, ba kayan abinci shima Abbati idan yace zai zo Mahaifinta zai cika mota da kayan abinci akawo mata . Sannan Yafendo tana turo mata da kayan sayarwa turaren wuta da wasu abubuwan da babu anan, haka yasa ta samu damar tsayawa da kafarta.
A can Nijar kuwa, Alhaji Mamman ne ya hadu da wata mata sun haɗu tun a lokacin zuwan shi Mali, sun dan tab'a soyayya sai gashi ta kuma dawowa rayuwarshi,. Bayan da ta fahimci ta kare mata, tun da suka hadu ta kara jan ra'ayinshi suka fara soyayyar bariki, kuma dama can yar barikin ce shima ba zai ce ba yar barikin bace domin bai san.yadda aka yi ya fada tarkonta ba.

Tunda ta dawo rayuwarsa tayi bincike a cikin matansa wacece yafi so, a binciken ta gano Sa'adatu da danta. Anan ta fara shige da fice, sai da ta cire mishi su a ranshi, sannan ta aza mishi kiyayyar Abdul Majid, idan ya ga yaron kamar zai kashe shi. Don haka yace kada ta kuma zuwa gare shi, don yaron.
----- Bayan ta gama IT, ta koma makaranta Allah ya taimaka akwai kudi a hannunta dasu ta biya kudin makaranta, ta cigaba da karatu, suna cikin karshen zangon da zasu gama makaranta, yazo a lokacin Abdul Majid bai wuce shakara biyu da rabi ba. Da murnar yaron ya tawo gare shi, Alhaji Mamman yasa kafa yayi kwallo da Yaron, tana wanka ta ji ihun Abdul Majid, da sauri ta fito daga ban daki, ganin Alhaji Mamman Ba'are ya rufe yaron da duka, yasa ta isa wurin ta dauke shi, tana faɗin. "Yaron da babu ruwanshi me yayi da zafi?" Kame gashin kanta yayi ya rufeta da duka, har da kwallo da ita, wulakancin da yayi mata Allah kaɗai ya sani, ya kuma jan ta har cikin ɗakin, haka Abdul Majid ya tafi bakin kofar yana buga kofar yana kiran sunanta "Hajiya!" Yana buga kofar, Alhaji Mamman Ba'are kuwa, ya kwana biyu bai tab'ata ba, haka yayi ta sukuwa akanta kamar ya samu jaka. Yana gamawa ya tashi yayi wanka ya gyara jikinshi, ya saka aka sauke musu abincin yayi tafiyarshi,

Bai kara waiwayarta ba, sai bayan sun gama exam ana batun zuwa bautar ƙasa, ya samu tana fama da laulayi, lissafi yayi kafin ya sakata gaba suka je asibiti aka duba lafiyarta, sannan suka dawo ya kuma rufe Majid da duka, ya kara saka mata doka. Tana gama bautar ƙasa Masters zata wuce. Haka yasa suka zama kamar bayi, a wannan zuwan da yayi har da Hajiya Tani da ya mai da ita yar gida. Amma idanuna Harirah yana kanta, domin bata yarda da ita ba, koda tayi magana akan hakan sai da suka kwashi yan kallo. Tana ji tana gani Tani ta samu damar k'amk'ame kome a cikin gidan.

Wato tani wata irin Shaidaniyar mace ce, da ta gallabi kanta da duk wanda yake kusa da ita. Musamman ta kananaye kowa har da kannenshi da Nana, babu wanda ya isa ya d'aga mata murya. Domin idan kayi magana Alhaji Mamman Ba'are zai ce ka fita ka bar mishi gida, haka yasa kowa ya sha jinin jikinshi. Kowa ya rufawa kansa asiri, kuma ai wargi wuri yake samu. Akwai wani lokaci da Hajiya Rabi ta rufe ta da duka, ai kuwa Alhaji Mamman Ba'are yana shigowa ya samu Tani a inda Hajiya Rabi ta dake ta, babu bin ba'asi ya rufe Hajiya Rabi da duka, sannan ya kwaso mata kaya ya watsa a waje, da guzirin sakinta.
Chapter 30 · 0% Book details