Sashe 16
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A hankali wurin yayi ta cika, kuma a wannan zaman babu bare amma kuma wani abin mamaki shine zuwan wasu daga cikin turawa da yan siyasar da Sajjid Mamman Ba'are ya gayyato, ya tashi ya taro su. Har wurin Nana suka gaishe ta. Kafin suka gaida kowa sannan suka koma wurin zamansu, Abdul Majid dan Hadiza Abdul Majid ba'are, ya mike tare da nufar wurin Hajiya suka gaisa. "Hajiya Abdul Jeed ba zai zo bane?" Idanunta da suka cika da kwalla ta ce mishi. "Ban sani ba, na dai tura Aryan bai ce min kome ba."
"Lallai Jeed dole ya bayyana anan. Domin an shirya makirci na bala'in fitar hankali."
Duk wahala da ta sha, da iya azabar da ta sha, wai karshe abin da ta samu shine ya tsonewa kowa ido. Suna da nasu amma ita nata da na Yaranta ya tsone musu ido. Hajiya Hadiza Ba'are watsawa danta Abdul Majid harara tayi, ita kan bata san wani irin d'a ta haifa ba, ko a gidan Ubansu haka yake makalewa ya'yan kishiyoyinta yana basu kulawa kamar wani son shi suke.
Komawa wurin zamanshi yayi yaki yarda ya kalli Hajiyarsu, da Nanah kakarsu kenan. Kanshi yana can bakin kofar aka fara taron tare da zab'en ra'ayi akan matsayin BA'ARE GOLDEN EMPIRES. Abin dai ba a cewa kome.
Haka aka fara voting, jikin Yaran Hajiya yayi sanyi ban da Amaan Mamman Ba'are, dan shi dama yasan haka zata faru, kuma shi yana tare da su, babu me kaso mafi girma da yawa a kamfanonin kamar Majid, don haka gara ayi uwar watsi kowa ya rasa, Aryan Mamman Ba'are kuwa ko a jikinshi domin bai tashi ya kada kuri'ar shi ba, kallon shi Alkalin yayi ya ce mishi. "Malam Aryan Mamman Ba'are, shin baka ga kowa ya kada kuri'a ba ne?" D'ago kai yayi yana yak'e ya ce mishi. "Alkali kayi shiru yanzu zan kundume wasar domin uban gayya ya bayyana." Ya cigaba da danna wayarshi alamar game yake yi, "Malam Aryan kuri'arka ake jira fa." "Ba iya nawa ba, har da na wancan da yake tsaye a bakin kofar." Ya nuna musu Majid Mamman Ba'are sanye da kayan turang. Shadda ce skyblue, yasha babban riga da takalmi halfcover, kanshi sanye da rawani ya rufe fuskarshi da ita, yadda yake tafiya kasan cikakken jarumi ne. Mikewa Aryan Mamman Ba'are yayi ya tafi can bayan kujerar da aka ware babba kuma an lullube shi da mayafi, Hajiya ya dace ta zauna a wurin amma saboda fitina ta hakura, sai gashi Aryan ya janye lulluben da aka mata, sannan ya jata baya, Majid Mamman Ba'are ya isa wurin y zauna, dukkansu sai da suka mike tsaye. Yadda ya zauna sai da ya jingina da kujerar sannan ya aza kafa d'aya kan ɗaya, ya janye mayafin da yake fuskarshi. Yana bin ilahirin mutanen wurin da rikitaccen Idanuwan shi me dauke da wutar takaici da b'acin rai. "Amma taya dan iskan Yaron nan ya dawo?" Cikin kwafa Hajiya Tani tayi magana tana kallon Majid da ya daura daya kan ɗaya, yana sakin wani murmushi yana kallon Aryan da ya koma wurinshi da zama. "Alkali Bismillah!" Inji Aryan ya faɗa yana murmushi. "Tow Malam Aryan kuri'arka da ta Abdul Majid Mamman Ba'are ya rage, akan sikeli" hannu ya kai aljuhun rigar shi ya Ciro wasu zinarai manya guda uku, sai na shi daya yana zuwa ya saka nashi, yana kallon kowa a wurin sannan ya saka daya na Majid Mamman Ba'are, tuni hannun ya rinjayi daya hannun cikin tsokana da niman magana ya ce. "Alkali idan na saka sauran biyu ina cewa Ba zaku ce nayi son kai ba?"
"Baka da matsala Malam Aryan" cikin wani irin juyi ya ajiye dayan, sai ga shi bakidaya ya rinjaye gefen. Kafin d'aga dayan sama ya ce musu. "Kun ganshi nan kuri'ar Majid Mamman Ba'are na karshe kenan!" Ya ajiye . Shiru wurin ya ɗauka. Babu wanda ya kawo Majid zai bayyana, balle a kawo zancen kuri'arshi, sannan babu wanda ya kawo wannan al'amarin haka shi daya kuri'arshi daya ta mutane goma ce ukun baki daya ta mutane talatin ne, domin kuwa asalin zinarin na Alhaji Mamman Ba'are ne, da kanshi ya ajiye wasiyya har kotu aka kai banki aka ajiye, asalima ba a kasar ya ajiye ba. Sai aka zo rabon gado aka gani. Ya narka ta zuwa na Majid Mamman Ba'are kuma ya saka sunanshi a jikin zinarin.
"Kuri'ar Hajiya Sa'adatu da Yaranta sune masu rinjaye, sannan suna da damar fadin yadda suke so ayi da BA'ARE GOLDEN EMPIRES."
A hankali Aryan ya mike ya ce. "Alkali dama ai idan aka yi rinjaye a kan mu gwanjon kamfanin za ayi ko?" Kallon Alhaji Haladu Ba'are da Sajjid Mamman Ba'are alkali yayi, suma kura mishi idanu suka yi.
"Alkali ni nake magana ba Sajjid tani ba, ba Haladu Ba'are ba, Aryan Mamman Ba'are yake magana."
"Eh Malam Aryan."
"Kawai a saka a kasuwa!" Ya fada yana me komawa wurin zamanshi ya daura daya bisa ɗaya.
Ajiyar zuciya Alkali yayi ya fara karanto ka'idodin sayar da kayan.
"Doka ta farko waɗanda suka fadi basu da hurumi akan kamfanin dole suyi hakuri da duk abin da zasu ji ko zasu gani. Doka ta biyu idan aka sayar ga duk wanda ya saya hurumin shine cire sunayen wasu da baya ra'ayi a board meeting, doka ta uku iya waɗanda suka saya suke da ikon tafiyar da kamfanonin baki ɗaya."
Wannan shine shirinsu idan Majid Mamman Ba'are bai zo ba,tow abin da za ayi kenan. Mikewa Aryan Mamman Ba'are yayi ya mikawa alkali kudin da aka sakawa kamfanonin. Hajiya tasan ba wayonta bane, ba Kuma iyawarta ba ne kawai wata falala ce daga rabbul alamin, ya bata yara maza biyu masu matuƙar zuciya da son cigaban juna. D'aga takardar kudin alkali yayi, nokewa kowa yayi babu wanda yayi kuskuren tashi domin kuwa basu da kwatar kudin da aka nima balle rabi. Haka yasa Majid Mamman Ba'are mika hannu. "Na saya!" Shine dama me hannun jarin da ya wuce misali. Yana fadar haka ya mike, tare da barin taron. "Alkali kaji ya saya, ko akwai wanda zai ja ne?"
"Babu Malam Aryan!" A hankali ya taka gaban kujerar Hajiya Tani ya zuba mata ido. "kun shirya wasa, ba tare da kun san waye dan wasan ba, ya dawo har na tsawon lokacin da ya dibawa kanshi."
Daga nan ya nufi wurin Hajiya ya daukar mata jaka, suka nufi hanya Jamilah da Aneesah suna biye da su. Lokacin da Amaan ya isa wurin Nanah kasa magana yayi. "Munafiki ba kace mana Aryan bai same shi ba? Ko dama munafurci ne yasa kazo don kasan sirrinmu!"
"Nana!" Alhaji Haladu ya kira sunanta, "shima bai san kome ba, babu babban shaidanin kamar Aryan yaron nan "
"Wai ku yaushe zaku daina faɗa akan abin da ba naku ba? Dukiyar nan da bakin Ya Mamman ya mallakawa Sa'adatu da Yaranta, musamman Majid don Allah ku kyale su mana."
"Ai kai ban san wani irin haihuwa nayi ba, baki daya baka da kishi da kishin yan uwanka, ban da jaraba irin ta Mamman ai shi kenan."
Hajiya Tani bata ce kome ba, domin dama ba zata tab'a cewa ba, amma zuwan Abdul Majid Mamman Ba'are ya kashe mata kasuwa, domin duk burinta ya lalace. Juyawa tayi ta futa bata musu magana ba, ta nufi hanyar waje ita da d'anta. "Hajiya!" Hannu ta d'aga mishi. A waje suka same su, musamman Aryan."Hajjaju! Ki kara shiri da kyau."
"Kana wasa da rayuwarka." Inji Sajjid Mamman Ba'are. Ai kamar jira ake Sajjid ya fadi haka sai ga Press sun shiga daukar hotonshi a bakin kofar kamfanin. "Taron da aka shirya domin ruguza kamfanonin BA'ARE, ya tashi cikin wani irin juyin juya halin, domin kuwa ana cigaba da taron Majid Mamman Ba'are ya bayyana sannan ya saye kamfanin da kaso daya na cikin dukiyar shi, abin da ba a saba gani ba domin duk taron da ake Majid bai tab'a halartar taron ba, amma wannan karon ya tawo cikin ban mamaki " can wani dan jaridar ya amsa da cewa. "A wani abin da ba a san mafarin shi ba, Sajjid Dan wurin Hajiya Tani da ta likawa Marigayi Mamman Ba'are, yayiwa Aryan Mamman Ba'are barazana da rayuwarshi."
Jikin Hajiya Tani ne ya dauki rawa, ta juya tana kallon Sajjid da ake ta daukar shi, da sauri ta fada cikin Motarsu, suna shiga ta juya a fusace . "Ina ruwanka da shi? Idan ma wani abu ya maka sai ka yi shiru meye na tanka mishi? Ga ka nan kato amma tunaninka na Yara ne, bakasan ka girme shi ba ne? Amma ya iya nutsuwa ya shirya kome cikin dadin rai. Ka koya daga gare shi."
Rintsa idanun yayi yana jin kamar ya fita ta rufe su da duka. "Kai mishi barazana da rayuwarshi? Kasan ko ciwon kai yayi kai ne, idan mun koma gida kayi gaggawar kiran yan jarida ka wanke kanka."
"In sha Allah "
"Na gaya maka, hatta tari idan kayi duniya zata fassara shi da wata manufa ce, baka gane ba, kana kokarin lalata min shiri na."