← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 138

Sashe 88

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuwan Aseem ya sani samun nutsuwa, sannan babu wanda ya kara min barazana, sai dai a wurin aikin ne babu sauki, ina zaune a za a tula min aiki kamar jaka. Tun ya Amaan yana zuwa ya bani hakuri, har ya daina nasan hana shi suka yi. A hankali na fara sabawa da aikinsu, ga shi ba hutu Asabar da Lahadi aiki. Don ko ban je ba, za'a kirani na je. A hankali na samu wata uku ni da Yarinyata mun nutsu, ana haka aka samu hutun ranar maaikata na duniya, muka wuce marad'i da Aseem, a can muka kwana uku, sannan muka dawo Niamey, ai a ranar da na dawo na sha masifar Mr Aryan kamar zai doke ni. Da na gaji ne na ce mishi. "Bafa aiki nake yi ba? Kune kuka gayyace ni nazo na san makaman aiki, akan me kuma za ahana ni rayuwata? Ban matsawa kowa ya zauna dani ba, kafin nazo nan ina raye don na bar nan ba ya nufin zan mutu ne. Tun kafin ayi uwar me sabulu balbale take da farinta." Na fada ina ajiye musu file dinsu na kamfani. Na juya zan fita Aryan din ya ce min. "Kina nufin kina da inda yafi nan ne? Ko kina da inda zaki zauna hankali kwance." "Kana mun barazana ne da rayuwata?" Na juya na kalle shi, "Zahrah ya isa haka." "A'a bai isa ba, bai isa ba barni na gaya mishi abin da yake ganin zai zame min kamar dole." "Ki ajiye aikin ki bar mana office ɗinmu." Naji Muryar shi kamar daga sama. Dariya suka bani. "Tow tunda na bar office dinku zan tafi lahira a kafa kenan ba." Na fada ina barin office din. Ko a jikina. A cikin wata uku na gyara musu kasuwancinsu ta hanyar d'aga darajar hannun jarinsu ta hanyar da ni kai na ban zata ba, sannan a cikin wannan yanayin, akwai mutanen da zasu zo domin saka hannun jarinsu don kawai rate na kamfanin GOLDEN EMPIRES yana tafiya, shine zasu min kinibibi. Na ajiye musu aikin. Ina fita na kira Aseem, na gaya mishi abinda ya faru. "Gani nan zuwa kin ji" ina tsaye a bakin kofar, Amaan ya iso da sauri. "Me yasa zaki min haka?" "Me yasa ba zan maka haka ba, halitta ta kuka yi da ba zan rayu ba sai da ku? Gaya min ko ce muku aka yi ina raye ne don ku? Ni fa bani da isasshen lokacin da zan na zama kuna juya ni kamar wata trouser dinku." "Amma kin san aikin da muka yi dake, yana bukatar taimakon ki. Da taimakonki muke kokarin bunkasa kamfaninmu ki ce zaki ajiye aikinki. Please ba don ni ba ba don halinmu ba, ki dawo." "Ba zan dawo ba." Daidai parking din Aseem, na shiga motar hankalina kwance. Daga can office ɗinshi yana kallon kome, yarinyar dan nutsuwa tana da shi, kawai ba xai yiwu tana abin da ranta yake so ba, idan har tana haka makiyan kamfanin zasu iya amfani da hakan. "Hamma anya Amaan ba son yarinyar yake ba?" "Shi ya sani idan ma sonta yake waye ya damu?" "Hmm! Tun ranar da aka kai mata harin nan, wannan mutumin ya bayyana kawai ban yarda da yarinyar bane." "Humm!" Ya faɗa yana kallon yadda Amaan ya dawo Office. Tun ranar da abin ya faru, ya fahimci wani abu, akwai wani abu a tattare da yarinyar na farko shine akwai wanda yake kare ta, sama da yadda take rayuwa. Don koda ya sa mutanen shi su bincika sun dai gano daga marad'i har zuwa Niamey akwai wanda suke bibiyarta, sannan kome na rayuwa bata bukatar shi daga wani, kome mata ake ana kawo mata. "Waye shi?" Ya furta da karfi, don ya zata a ranshi yake magana. "wa kenan?" "Idan baka manta ba, mutanen da suka bi bayan Amaan suka isa wurin an batar dasu. Sannan case din an kashe shi daga wurin yan sanda. Ba tare da sanin yarinyar ba, don an hana a bincike ta." "Eh Hamma haka ne." "Akwai wani babban inuwa a saman kanta,na rasa waye shi?" "Ka rasa waye shi?" "Eh na rasa, ina gudun alakarta da kamfanin yasa a cutar da ita." "Tabbas Hamma kowa na kamfanin nan aiki yake yi, ita kuma ta shiga jikin Amaan lokaci guda haka yana nufin ake bibiyar rayuwarta. Tow ya zamu yi?" "Kyale ta!" "A dawo da ita dai!" Don ya fahimci abin da yake son faɗa kenan. "A'a barta ta tafi tunda ita ta zab'a haka." "Bammmmm!" Aka bude kofar. "Munafukai algungumai, ba zata bar aikin nan ba kuma wani shegen ya kara mata rashin mutunci."tari ne ya turnike shi, har ya fadi a kasa, jini ta kunne da hancinsa, ta ko ina fita yake. "Kai Amaan!" Inji Majid yana me rungumar shi, da sauri ya ciccibe shi suka fita daga kamfanin, motar kamfanin na kai agajin gaggawa aka dauko, suka nufi asibiti. A can aka amshe shi, aka shiga bashi taimakon gaggawa. Har dare suna asibiti babu wanda yayi tunanin Hajiya. Sai da Jamilah ta kirata ta ce tazo asibitin, ganin halin da Amaan yake ciki yasata jin kamar zuciyarta ne zata buga. "Aliyu meke damunka?" Ta fada tana jin wani irin kuka, tabbas Amaan yana ganin jarabawa, haka ta fito tana kuka me ban tausayi. "Aryan me ya same shi!" "Hmm" ya ce kafin ya bata labarin abin da ya faru, kafin ya kai aya ta ce musu. "Anya yan adam ne ku? Don ta kara kwanaki uku sai ya zama kuskuren da za a Kore ta? Na zata ko makiyi Aliyu ya kawo ya ce zai zauna da shi , ku masu taya shi zama da shi ne ashe kanku kuka sani? Ni zan dawo da yarinyar." Ta juya tare da barin Asibitin, don ita Hajiya a tunaninta Amaan son Zahrah yake, don haka ta saka Aryan din a gaba har apartment din Zahra. Akwai wani abun da Allah shi kadai yake haɗawa, lokacin da Hajiya ta ga Zahra sakin baki tayi tana kallonta. "Ya sunanki?" "Fatimah Abubakar!" Murmushi Hajiya tayi duk hankalinta a tashe, amma sai tayi ƙoƙarin kwantar da hankalinta. "Amaan ya fadi bayan barinki aiki yana cen asibitin kwance sai abinda hali yayi." Rufe bakina nayi ina jin hawaye na zuba min. _Zahra guba ce a jikina nasan ba tsawon rai zan yi ba, idan na mutu ki tsaya a gefen ahalina_ "Yana wani asibitin?" Murmushi Hajiyar tayi tana faɗin. "Ko zamu tafi ne?" Kasa nayi da kaina, don ta cika min idanu, haka na dauko Amirah muka fita, ita a farko ta zata irin a wurin shiriritan shi ya tsinto ni, yake ta wannn hidimar dani, sai da take tambayata matakin karatu, da sauransu sannan ta fahimci ai ni ba watsatssiya ba ce, da kamun kaina sai dai gani na da yarinya yana dukar duk wanda yaji yarinya ta ce. Haka muka isa asibitin, a bakin kofar shiga asibitin muka hadu da Chairman, sai muzurai yake gashi bai da irin fuskar da zaka kawo mishi raini, don ko fadar da muka yi da Aryan muka yi, ba da shi ba shi ce min yayi na bar kamfanin. Kuma ban iya ja da shi ba, don kwarjinin shi kamar wanda ya tafi filin yaƙi. Allah sarki ko ina wannan sojan, na tuna shima dai duk da a duhu ne zai kai haka tsawo. Haɗe rai yayi a raina nace. *Wannan mutum da alamu zai yi mugun hali, ji yadda yake bata rai kamar ya ga kashi* Tuni muka wuce cikin asibitin har dakin Amaan din, hmm masu kudi suna jin daɗinsu, a lokacin da muka shiga wai ashe ya farka bayan fitar Hajiya. "Final ga ta nan!" Kunya ce ta kama ni. "Kyakyawar gaske kuwa, kai Aliyu don uwaka a ina ka samu kyakkyawar mace, wannan ai da Alhajin Allah ta dace, kun ga wata doguwar halitta kamar matar gidan Aljannah. Gaskiya Sa'adatu ki gayawa Aliyu ya nemi sa'ar shi wannan ai idan aka hada ta da Alhajin Allah zasu zama wata da zahara, don zasu haskaka alkhairi da duniya." Inji tsohuwar da na lura rigima ya gama cinye ranta. "Ban da zalama irinta Aliyu ai yarinyar nan da Alhajin Allah ta dace ba shi ba, don haka wallahi na gaya miki ki gaya mishi ya nime wata mace ba dai wannan ba." "Nana babu wata mace da zai nima, ita yace yana son gani ba wata ba. Babana ya jikinka?" "Da sauki Hajiya,amma Zahra ba budurwata ba ce, kanwata ce kamar su Jamilah." "Ban gane ba?" Mika min hannu yayi, na nufe shi. Murmushi yayi min sannan ya ce min. "idan har na tashi, ki gaya min me kike so na baki, domin na saka rayuwarki cikin hatsari." "Lafiyarka tafi min kome, Allah ya tashi kafadunka." Na faɗa mishi hawaye na zubo min. "Kina kuka ne don na gaza ko?" Girgza kai nayi ina share hawayen fuskata. "Kai ne mutum na biyu da ba zan manta da alkhairinshi ba. Ina zuwa ka amshi ni hannu bibbiyu. Taya ba zan yi kuka ba kowane mutum da ta shi ƙaddarar naka ƙaddarar iya boyewa ahalinka lalurar ka sai da yaci lakarka. Ya Amaan, kai mutumin kirki ne wanda yayi kokarin sadaukar da rayuwarshi domin ahalinshi. Duk da ban gaya maka kome a kaina ba, daga gani na kace kana min kallon wacce take cikin kaɗaici. " Kuka ya kwace min, "ina niman yafiyarka lokacin da na gaza fahimtar ka, ban san kai waliyi ba ne sai yanxu, ka gaya min me kake so nayi maka daga yau har zuwa karshen rayuwata." "Babu kome!" Ya faɗa min yana murmusa min, "Babu kome fatana ki rike min Hajiya kamar ke ta haifa bamu ba, ki kula min da Hajiya kamar ke ta haifa." Kukana ne ya tsananta domin a yau na samu dan uwa, na kara samun uwa wannan shine dadi kan dadi kunama ta harbi gyambo. Ga Uwa ga dan uwa, "A yau da ka kirani a matsayin yar uwa ka kara min da kyautar uwa, sai nake jin kamar nafi kowa dace a samun dan uwa irinka...... 300₦ 0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 07035133148 #Mai_Dambu ce [5/29, 07:47] Hlm: BHB246 "Kai mutumin kirki ne da duniya
Chapter 88 · 0% Book details