Sashe 8
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ina Zahrah take?" Jin murya Shamsiyah yasata fitowa daga cikin ɗakinta tana kallonsu. "Tana asibiti ba lafiya." Daga haka ta nuna musu kome da kome da ta sayo, sannan ta wuce ɗakinta ta kwashe kayan. Wurin karfe daya na rana Zulaihah ta kirata. "Wai Addah ba za a kawo mana abinci ba ne?" Runtse idanuwan ta tayi kafin ta lailayo wata uwar ashar ta maka mata, "babban.....,,, ubannki! Ba za a kawo ba kina da abinda zaki fada ne? Shegiya mara mutunci."
"Addah dubu dari aka baƙi, idan ba zaki d'aga kafa ba, ki dawo min da kudin mu maza, dawo da saba'in xan baki talatin din."
Kamar ta fasa ihu tayi shiru, kafin ta ce mata. "Bana son iskanci, nace ba za a kawo muku ba ne? An jima za a kawo muku." Ta fada a fusace, "Adda ihu kike mana fa?" Inji Zulaihah. "Yanzu don Allah na ce muku ba zan kawo ba ne, ku yi hakuri me da me kuke bukata?"
"Yawwa a hada mana da kofi biyu, kayan tea flask da kuma special abinci dare da rana. A kula da mu kamar baki Hajiya Addah."
"Shi kenan za a kawo muku." Wannan shine asalin dole kanwar naki. Haka suka kashe wayar, kowa najin babu dad'i ita Addah tana ganin kamar Zulaihah bata kyauta mata, ita kuma Zulaihah tana haka ne domin huce takaicin Mahaifiyarta.
***
*Zahrah*
Ruwa aka sanya min, bayan an kara duba min ciwon, shi ne aka fito dani, yanzu dai sun saka min ruwa da wasu allurai. Ina jin wayar Zulaihah da Addah, a hankali barci yayi gaba da ni. Ban farka ba, sai wurin karfe uku, na samu Munaisah da Ummi suna hira sama-sama. Zulaihah bata dakin, kallonsu nayi kafin na ce musu. "Kunzo ne?" Domin ban kawo a raina zasu zo ba. Kallona suka yi kafin suka ce min. "Eh amma ke taya aka yi ana yin abun arziki ta kasa ke taya kika kare da gefen cikinki?" Shiru nayi ban ce musu kome ba, shigowar Zulaihah da Dr Umaima yasa ni kallonsu ina kakaro murmushi. Ganin su Ummi da Munaisah sai Dr ta kara yarda wani lokaci halittar kyau da hasken fata bala'i ne, domin kuwa Munaisah hancinta da huji, kunnenta kuwa har saman kunnen a makale suke da barima har da na gwal.
Sannan ta kara kallonsu ganin yadda suke wani, iyayi yasa ta sha jinin jikinta waɗannan yan matan sun fini wayewa da gogewa a bariki, ni din kamar sabuwar yankar rake ce, shi yasa har nake gadon asibiti tow ko da ta koma gida ta ji kaninta yana bata labarin ai gida gida, Magaji Abba Chindo ya sa aka yi ta niman wata yarinya da ya dauko daga cikin gari. Kallona tayi tana mamakin anya ba ni ba ce? Duba min ciwon tayi tana faɗin. "Kin yi sallah kuwa?" Girgiza kai nayi. "me yasa kike wasa da sallah.". Kura mata idanu nayi kafin na bude baki ta daura da cewa. "Sallah tana kare mutum daga aikata alfasha, idan har kika kiyayye sallah, a duniyar nan babu wanda ya isa ya cutar da ke, sai dai abin da Allah ya rubuta xai same ki."
"Na gode zan kula, bana wasa da sallah amma daga faruwar wannan al'amarin nayi wasa da sallah har subhi da zuhur sun wuce ni"
Murmushi tayi sannan ta juya tana kallon Zulaihah. "Idan kika hada mata tea, tayi sallah ko a zaune ne sai ta sha rabin kofi."
"Abinci fa, domin gashi an kawo." "Sai jibi saboda tumbin ta ya tabu, tasha tea din idan babu abinda ya faru, zata iya cin abincin."
"Shi kenan" ta faɗa tana hada tea din, sannan ta fita daga cikin ɗakin, haka Zulaihah ta rike ni har ban daki ta taimaka min nayi alola, sannan na dawo dakin na gabatar da subhi da zuhur, ina idarwa na amshi tea na sha, ciwon ciki ne ya sako ni gaba, kamar zan mutu kiranta Zuzu tayi suka shigo dakin. Wuce dani wurin scanning aka yi, aka min anan suka ga ɗinkin cikin bai yi da kyau ba, akwai buƙatar a sake min wani aikin yau. Alluran rage zafi tayi min, sannan suka wuce aka fara shirin, a lokacin Adda ta kira su Ummi tana faɗa akan me basu dawo ba, suka gaya mata ai aikin aka kuma shiga dani, babu shiri Addah ta nufo asibitin, domin abin ya bata tsoro kada garin niman duniyarta, na rasa rayuwata. Bata san amsar da zata bawa Shad'ari ba.
Haka kuwa ta iso a gigice, tana tsaye har aka fito dani. A galabaice jikinta yayi matukar sanyi, ita tsoro take ji kada na mutu, haka suka bi ni har dakina, "Likita ya aikin?" "In sha Allah an dace, dama na farko munyi shi tare da bin raunin ne, amma na yanzu mun yi shi ne da bin duk inda yake ciwon."
"Hmm! Kuma nawa ake bukata? Domin akwai kudi a hannunsu." Kura mata idanu Umaima tayi kafin ta ce mata. "Allah sarki, ai Captain ya biya kome babu abinda ake bukata duk kudin da za a cire a insurance ɗinshi za a cira."
"Kai madalla."
Murmushi Addah ta sake tana faɗin. "Don Allah ko zaki taya ni amsar kudin hannunsu, ki ce musu akwai wani abu da za a saya." "Hajiya anya kece kika haifi yaran nan?" "Kai haba daya Kyakyawar me dogon hanci da dogon gashi, ita ce na haifa. Ita kuma mara lafiyar da wancan me doguwar riga ruwan toka ubansu daya kanina ya haife su, ita kuma daya fara tas din can itama yar Kani nace, Zahrah ce ta dauki duhun fatar Uwarta ai kin gansu nan." Gaba Doctor Umaima tayi ta barta a nan tana surutu, haka kawai take jin Addah bata mata ba, Indai zaka kawo Yara ka daura su kan wani yanayi mara daɗi, meye ribarta? Itama Adda dakin da aka kwantar dani ta shigo, tana tsaye sai yamutsa fuska take tana faɗin. "Ita dai wannan shegiyar ta san hanyar b'adda kudi loko-loko, ban da iskanci da wulakancin taya zaki kare a gadon asibiti akan ciwon da bai taka kara ya karya ba, mtsew." Ta ja tsaki tana isa bakin gadon yarinyar nan yar bala'i, a ranta domin kuwa ta ga yadda ran kowa yake a b'ace idan ta cika mita kan yanayin da ake ciki.
"Tow ai ku muje ko, tunda an yi aikin a sa'a" ta fada tana barin dakin, haka suka bi bayanta ban da Zulaihah da take zaune, ta saka ni a gaba tana kuka. "Ya Allah kai ka jarabce mu Ubangiji ka tashi kafadar Zahrah." Ta cigaba da kukanta, har aka yi sallar la'asar tayi sannan ta koma ta zauna. Shigowa Dr Umaima tayi tana faɗin. "Kuka ya isa haka, ki ci abinci."
"Ba zan iya ci ba, bayan Zahrah tana kwance."
Shiru suka yi, sannan Dr ta ce mata. "Matar nan Mamarki ce?" Rintse idanunta tayi tana jin kamar an watsa mata ruwan zafi a jikinta, don dai Allah ya ƙaddara zata zo a tsagin addah ne amma da ba zata tab'a yarda a ce Addah mahaifiyarta ce ba.
"Eh Mamata ce."
"Allah sarki naga kuna kama sosai."
"Eh haka mutane ke faɗa muna kama da Adda, shi yasa duk lokacin da wani ya ganni sai ya tambayeta ko ya tambaye ni."
Daga haka tayi shiru itama Dr Umaima bata zake sai ta san kome akanta ba, amma zucuyarta ta kwadaitu da son sanin wacece Ni?
★★
Tarkon makiya
Bayan an yi sallar Isha, da ya jagorance su, yayi musu addu'a. Sannan ya mike tare da kallon sauran abokan shi da suke su bakwai ne, sauran kaso masu girman suna tare da Commodore Magaji Abba Chindo, murmushi yayi sannan ya dauko kayan aiki, yana kuma da kayan da zasu saka idan zasu faɗa cikin ruwa. "John ko zaka zauna anan ne naji kace matarka ta kusan haihuwa."
Daukar kayanshi yayi yana sakawa, "Cab ai nayi Imani da Allah, amma gara na mutu a filin yaki da ace ina nan, ina jiran dawowarku." Ya fada yana saka rigar ruwanshi domin ana iska don har tana kad'a jirgin ruwansu.
"Ammar kai ma ko zaka zauna ne, kace rabonka da Misau tun haihuwar Anam, saboda inda zamu mutanen suna dauke da miyagun makamai."
"Hmm! Fatana kada Kasata ta mance da 'ya ta."
"Kana nufin zaka bi ni kenan!" Haka yayi ta rokonsu da su hakura da bin shi, amma ina baki daya suka nace, sai sun bishi anan ne suke ta hira da zasu tafi wurin karfe tara na dare, ya dauke su zuwa wurin Commodore. "Zamu tafi Sir! Dayawa sun daura hakkin kula da rayuwarsu akanka da kuma ni, Sir sun yarda da kai ne suka gwammaci su zauna da kai, Sir hakkin mu ne mu kare kasarmu da mutanen da suke karkashin kulawarmu. Please Sir gasu nan"
Har ya gama maganar Magaji Abba Chindo,bai ce mishi cikanka ba domin kuwa baya fatan ya bude baki yayi magana, Babban burin shi Captain yana barin jirginsu yan tada kayar baya su yi musu daga-daga da namar su, shi yasa da ya ce ya tafi,ya fara bin sauran yana gaya musu ai fa Captain da suke ganin zasu bi, bai da lafiya da zaran an fara harbe-harbe cutarshi zata motsa. Muna cikin zamani ne da son kai yayi mana katutu, kowa son ranshi yake haka yasa baki daya suka janye bin bayan Captain.