← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 138

Sashe 89

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

bata dadaka da kasa ba, kowane mutum da ƙaddarar sa. Ka tashi don Allah." Na faɗa mishi ina hawaye. Dariya ya fara yana tari. "Hajiya nifa ko yau na mutu bani da haufi." "Shiiii! Cuta ba mutuwa ba ce, haka zalika wuya bata kisa, da tana kisa da yau bana nan a zaune. Zakarar da Allah ya nufa da cara." Fuuuu tsohuwar nan ta fita, ban damu ba na goge hawayen fuskata. -- "Alhajin Allah, yarinyar nan waye Ubanta? Ni dai da kai ta dace ba da wancan karuwin ba." Ware idanu yayi yana faɗin. "Nana ni kuma?" Girgza kai yayi yana faɗin. "Never," "Kai ni ban san neba ba, da kai dai ta dace domin nasan...." Bai saurare ta ba, ya wuce dakin. "Allah ya baka..." Damkar hannuna aka yi na juya, ina shakar kamshin turaren shi. Sauvage doir, sarawa kaina yayi ina jin wani abu kamar an jona min wutar lantarki. "Tashi!" Kamar wanda ya bani rufe baki, haka na mike tare da bin shi kamar raƙumi da amale "Ka sake ka fitar da ita daga dakin nan, furucin da zai fito bakina zai iya shafar rayuwarka." Ba iya shi ba, hatta ni taka burki nayi tare da juyawa na zuba mishi idanu. Ina jin kaina kamar zai rabe biyu, numfashi na ne ya shiga hawa da sauka. Na fara niman shi da kyar da kyar, domin ji nake kamar numfashina zai bar jikina, ko Hajiyar ta fahimci haka ne ta zo ta rungume ni ta baya."Hajiya!" Ya kira sunanta a raunane, "Na gaya maka daga kalamai na." Tsit wurin yayi, "koma ki zauna ki dauka nan cikin yan uwanki kike raye, babu me miki ko kallon banza ne." Ta cire hannunshi cikin nawa. "Amma Hajiya." Ruwa ta bani na sha. Ina tari. "A'a Baffayo, kana son yarinyar nan a kusa da kai. Taya zan nisanta ka da ita? Ni kuma ina son ko ba zaka tashi ba naji kana magana kamar kowa, shima arziki ne zauna Yarinya ya ma sunanki." "Fatimah Abubakar." Murmushi Hajiya tayi hawaye na zubo mata. Daga yadda take daurewa kawai ya sa ni tuno labarin da ya bani irin wahalar da Hajiya tasha da mutane, tausayin ahalin ta yakara ninkuwa a rai. "Zahrah ki bi Hajiya ku je gida ku kwana." Girgiza kai nayi ina faɗin. "Zan kwana a tare da kai, sai dai a tafi da Amirah." "Akwai sauro kuma kin ga kuma..." "Allah na gode maka da babu dodo ko?" Dariya yayi, sannan na ce mishi. "Ya kamata ka rage nauyin da yake ranka, kayi barci ka huta." Daukar Amirah Aryan yayi da ta fara barci. Ni da hajiya muka zauna a asibitin can sai ga Chairman da bargo, matashin kai. Da sauran abin bukata. Mikewa nayi zan amsa ya wuce ya ajiye. "Hajiya xan kwana a waje." "Tow!" Haka muka kwana muna hira sama-sama, kafin barci ya dauke mu. Ina zaune a kujerar dakin nayi barci Bayan na lullube kafata da bargo. ...... Wani irin duhu garin yayi gani cikin sahara, na rasa inda xan dosa. Ji nayi an rike hannuna ana ja na da sauri. Haka na bi wannan hannun, har muka shiga haske. "Yazid!" Na furta lokacin da na ganshi. Murmushi yayi min sannan ya riko hannuna muka ci gaba da tafiya, bamu yi nisa ba, muka hadu da Chairman da wasu mata har da Hajiya tare da su Addah da Munaisah. Da sauri na nufe su suka juya min baya, na ƙara sauri zan nufe su. Wani farin dattijo ya rike ni. Ya nufi daki da ni. "Idan kika yi hakuri zasu biyo ki, kada ki bisu domin zasu sake nasarar raba ki da kome da kike da shi." Buga kofar dakin aka yi Chairman da Yazid suka shigo kamar wasu zakuna. "Duk wanda kika zab'a, Allah yana tare dake, amma shi wannan idan kika zab'e shi tsugune bata kare ba..." Bude idanu nayi daidai lokacin da xan kalli inda ya nuna min. Hakin da nake yi ne ya sa dole ya shigo dakin, yana kallona. Cilla min goran ruwa yayi ya fita, a hankali na bude ruwan na sha, na shiga ban daki nayi alola. Dakyar na samo abin sallah. Na tada sallar dare.
Chapter 89 · 0% Book details