← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 138

Sashe 98

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya bata ce mishi cikanka ba,amma ta zuba mishi idanu wannan abin da ya faru sai da Hajiya tayi ta fama da rashin lafiya,. musamman jininta yayi mugun hawa, bata magana balle a ce ta rage wani abu a ranta ranar da ya dame ta da tambayar meke damunta, sai da yayi danasanin tambayar, domin kifa hannunshi yayi a fuskarshi. Hajiya tayi mishi magana ɗaya."idan ka sake yarinyar nan ta subuce daga kamfanin nan, asarar da zamu tafka sai ka rasa inda zaka saka ranka. Mune masu kaso 90, tow ka je ka duba Baitul Malin kamfanin Yan uwanka sun kwashe kaso da rabin dukiyarsu don gudun kada Amaan ya faɗa kan nasu don ya gurguntan duniyarka. Idan har zata iya bada lokacinta domin aikinta ina ga baka bukatar ƙarin haske.."

Sajjid
"Goga kaji labarin Yazid yana nan kasar kuwa?"shaƙar hodar iblis yayi yana faɗin. "Koma meye sai na kashe dan iska."
Murmusa mishi Nawwas yayi ya ce mishi. "Akwai yarinyar da nake nima, ga hotonta nayi maka alkhairi me yawan gaske. Ina son ka biya ni da wannan alkhairin, ka nimo min ita."
Duba hoton yayi Zahrah ce sakatariyar Majid. "Amma kai dan iska ne, Ita yarinyar nan tana wurin Majid da muke Uba daya kuma nima na yake ruwa Ajallo, shi kuma Yazid kasan kanwar mu bata jike."
Nuna mishi hannun yayi dungulmi ya ce mishi.."idan har akwai gaskiya a abotar mu, ba zaka ji dadin ganina da wannan abin ba ko?" "Don Allah boye zan san yadda zan kawo maka. Amma me xaka mata?"
"Budurwa ce cikakkiya, ina son kafin wani ya fara saninta ni na shanye wannan romon farkon." Dariya Sajjid yayi yana faɗin. "Zaka bani bayan?""kai dai kazami ne, me zaka ji a wurin kazanta?"
"Koma me ina son a bani wannan damar."
"Zan shirya kome cikin nutsuwa."

Tunda muka shigo gidan, na fahimci lallai Yazid babban mutum ne, domin bakiɗaya unguwar security ne, kuma duk sun yayyame unguwar bakiɗaya baka isa wucewa ba sai da dalili. Cikin gidan muka shiga na sake wanka muka ci abinci, a daren ranar muka bar Niamey. Barci nayi ta yi a jirgi, Umara ya kai ni nayi ibada tsawon sati biyu ina ibada. Bayan mun gama muka wuce Dubai anan muka gama kwanakin mu, sannan muka wuce Nigeria inda muka tafi har Taraba, a Yola muka hadu da SK Lamido, dakyar Yazid ya bashi aron Amira mu kuma muka wuce taraba kwanan mu biyar bayan ya cika Yaya Babangida da alkhairi. Kai bawan nan akwai Alkhairi.
Gidan SK Lamido muka sauka aka mana tarban arziki, bayan sun cika mu da hidima. Mamar Sk Lamido har da kukanta don zamu tafi. "Idan tayi hutu xan kawo miki ita Umma." Inji Yazid nasan shi kaifi daya ne, idan ya fada ba zai sauya ba. Daga nan jirgin da muke tafiyar da ita na shine marad'i muka wuce.
[5/29, 07:47] Hlm: BHB252
Kwanan mu biyar a can muka dawo Niamey, nayi wani kiba har da kumatu, ni kaina na san na sauya.
Sai da yayi min sati biyu bayan yawon da muka yi, ya ce zai tafi ya zuba min idanu. "Zahra, akwai mafarkin da na fahimta baki cimma ba, shi yasa ba zan kawo bukatata gare ki ba. Amma idan har kin cimma ina jiranki, ni me kaunarki ne a kodayaushe. Aikin nan idan bai zama dole ba, ki hakura da shi amma ba zan tilasta miki lallai ki bari ba, don nasan kina da burinki akan aikin."abin da yasa ya fadi haka a tafiyar da muka yi yaga yadda nake sayayyar littafan da suka shafi kasuwanci, haka ya sa shi fahimtar ina son aikina.
"A'a..." Sumbatar goshina yayi yana faɗin. "Na sani wani cikin kamfanin ya nemi alfarma ba!" Kura mishi idanu nayi, "Jeki kwanta." Haka na mike na nufi dakin, har yanzu jin dumin bakinshi nake a goshina, murmushi nayi, washe gari da safe ya shirya na rakashi airport suka tafi kafin na dawo bakin aikina, ban san ya gaya musu zan dawo ba, ina shiga kamfanin naga an karbe ni da farinciki godiya nayi na wuce elevator, ina shiga Chairman shima yana zuwa komawa gefe nayi na makure bance kome ba. Har muka isa office ina baya yana gaba, "Oyoyo kawaciya!" Murmushi nayi don na lura dan larai dan iska ne sai ya ce zai rungume ni. Zama nayi a kujerar Office din na fara dube dube. Can aka kira layin office din
dan larai yadauka ya kalle ni. "Kiranki ne." Dauka nayi. "Shigo!" Ya faɗa, gabana ne ya fadi. _Kada Chairman dinku ya zame miki dodo babu abinda zai miki, ba zai kuma wahalar dake ba, ki nutsu ki daina rawar jiki akan kowa. Kinji ko* murmushi nayi na ciro hoton da muka yi a Dubai na saka a dest dina, na nufi Office din Chairman.
Ina shiga na gaishe shi, bai amsa ba bai kuma d'ago kai ba, *A duk lokacin da ya kiraki kika ga bai da lokacinki, to ki bar office din* kallon agogon hannuna nayi naga lokaci har naci minti biyar. Bance mishi cikanka ba sai jin sawun takalmina yayi zan fita. "Ni na sallame ki?" "Ina kiyaye rayuwata da lafiyata, idan na nakasa kamfaninka bata yi asara ba, Yata da mijina ne zasu yi asarata." Na saka kai zan fita ya ce min. "Ok kice wannan dan kwayar ya zuga ki kenan?" "Duk da shi dan kwaya ne, ya kula da ni kamar yar Adam, innocent kuwa suna kula ni ne kamar dabbobin da suke kiwo."
"Zahrah;" ya daka min tsawa, ko kaɗan ban razana ba, "kika ce me?" "Sir idan akwai takura sai na bar aikin ba zaka saka ni a gaba kamar baiwa ba." Na faɗa ina kallon shi don tsanar da na mishi ya gani ba tsoron shi nake ji ba.

Kome ya tuna ya ce. "Amma da kika yi tafiyar haka ake dawowa babu sanarwar kin san asarar da muka yi kuwa?"
"Dake ni baiwa ce shi yasa ba zan san.asarar da kuka yi ba, sannan ai ko baka sani ba naga staff sun yi welcome din dawowata." Na fada.. "Ki je wurin Aryan ya baki bayanai akwai baki daga lokacin, kamfaninmu yana dab da durkushewa."
"Allah ya kiyaye na gaba."
Na fada ina barin office ɗin, yayi hakuri tare da rarrashinkansa ne don Hajiya ta kafa mishi sharadi da sai ya kure mata hadda."
Koda yake dawowa ta, bai saka na samu hutu ba, amma kuma iskancin Mr Chairman ne bana dauka, duk yadda yaso na dauka naki yana min xan tsayar mishi ta hanyar zan bar aikin babu dole haka yasa shi rage zafin kai ba wai don ya daina ba, a'a sai dun kawai yana niman nasara da biyan buƙatar kamfaninsu.

Bani mantawa Hajiya ta bani wani aikin binciken da na gano Amaan yana fitar da makudan kudade a kamfanin duk wasu kwanaki, lokacin da na tura mata ta ga sakamakon sai da tayi kuka, haka yasa take ta bani hakuri ta email dina na dawo kamfanin. Alhamdulilahi daga cikin abin da ya faru Hajiya ta sayar da manyan kadarorinta, ta zuba kudin a kamfanin, haka yasa ni da kaina na bashi shawarar a saka kamfanin a tsarin manhajar play store. Kuma alhamdulillahi, take muka bayyana kudirinmu na duk inda kake a duniya zaka sayi gwal kuma yazo maka.

Sannan an rage ma'aikatan da basu da amfani, domin a farfaɗo da tattalin arzikin kamfanin, mun samu nasarar cire ma'aikatan bogi, sai gashi wannan karon manyan kamfanonin sun fara zuwa ana zuba hannun Jari, kai a cikin wata shida kacal ni kaina nasan nayi macen ƙoƙari. Wannan aikin da muka yi yasa shi bamu hutun sati daya. Muna dawowa hutu ya shirya mana tafiya india seminar. Kuskuren da nayi ban gayawa Yazid ba, har muka bar kasar nabar Amira wurin Siyamah da Baraka da tazo karatu.

Kwanan mu biyu, a Delhi na fito motsa jiki, don na je wurin ina fitowa na gansu zaune kowannensu sai muzurai yake. Mika min ruwa Yazid yayi cikin kulawa ya ce min. "Shine baki gaya min ba.""kayi hakuri kasan sha'anin aiki." Na fada ina kokarin zama,"idan kun gama seminar ku ina jiranki muje yawo!" "Ok" na fada ina tashi na wuce dakina, kallon juna suka yi, kowannensu yana jin haushi musamman Majid da yake ganin iskancin Mr Yazid ya fara wuce iyaka.
Bayan na shirya muka tafi seminar, bamu dawo ba sai karfe biyar, abinci naci da sallah,.muka shiga zaga India ba karamin fusata Majid yayi ba, amma haka yayi hakuri. Ya kira Hajiya ya gaya mata abin da ya faru. "Fisabilillahi Hajiya aiki muka zo yi ko yawo?"
"Mijinta ne don haka baka isa raba su ba."
Wannan korafin ya mata dad'i, ko babu kome zuwan Yazid zai saka shi hankali.
Mukan mun sha yawo, sannan ya kashe min kudi kamar hauka, sai dare muka dawo. Yana ganin kayan da ke jikina ba shi na futa da shi ba, ya biyo ni. Bayan na fito wanka ina goge kaina, ya buga kofar nace. "Shigo" don na saka kaya, kuma ina goge gashin kaina ne. Lokacin da ya shigo yaga ina ta goge gashin kura min idanu yayi.
"Ba zan hana ki bin shi ba, amma don Allah kada ki zubar min da mutunci." Ya fada yana kallon yadda nake ta goge gashin. "Idan mijinki ne,.ku fadawa duniya amma haka."
"Ban gane ba?" Rufe kofar yayi yana dafe goshinsa, ya kwafsa.
Yana fita abun ya bani dariya, na kwanta abuna nayi barci Bayan nayi waya da Siyamah da Baraka da Amirah, kashe wutar dakin nayi muka fara waya da Yazid. Ina dariya, akwai abubuwan da ba zan manta ba, yau nayi su kallo a cinema, na tafi wuraren tarihi,
Chapter 98 · 0% Book details