← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 138

Sashe 131

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dukkanmu munyi aure Ummi ce bata yi ba,sannan Nenne taji sauki har tana takawa Munaisah ta saya mata gida babba ta zuba yan haya da masu kula da ita, atow hidima takewa Mamanta kamar ba gobe sannan tana kashe mata kudi kamar me, Munaisah tana da kudi domin ko sarkokinta kawai masu yawan gaske ne, balle kuma tsabar garin kudi ga shagunanta A yola da Taraba,naji tana cewa wa ma zata bude wasu shaguna a abuja da Lagos, domin sun hada gwiwa da mijin Zuzu. Wanda yasa zuzun itama ta zuba kudi suka shiga juyawa. A lokacin na ce musu sun munafurce ni, budar bakin Mijin zuzu cewa yayi ko mutuwa Majid yayi ya bar abinda yarshi da ƴaƴanta zasu mora, balle ana maganar Chairwoman na Ba'are. Harararshi nayi lokacin, kuma zuwana ma Munaisah ta kara gaya min.

Bayan dawowarmu na nutsu wuri guda, na fara zuwa aikin kamfanin inda aka bani Office din Majid, sai dai abin da na fahimta kamar ana tab'a kayan Majid na Office din, wasu abubuwan an bincika su. Sannan yanayin dai ba yabo ba fallasa, ni da Aryan muka kara mike kafa da gaske muna aikin da ya dace.

Shekara daya ya wuce ranar Birthday din,Alfah ranar naji ya kara nisa ga zuciyata, lallai Majid yayi nisa a gare ni. Haka nayi ta fadi tashi muna aikin muna fama a lokacin aka sake tasa kamfanin a gaba, wannan karon mun yi nasara, an yi haka da sati daya, gobara ta kama a bangaren Hajiya Rabi da Yaranta. Domin ba iya mu kaɗai muka tashi ba, hatta a can Kamaru sun tashi tsaye, sai ga gobara ta lashe duk wani abin da Rabi ta tara ita da Yaranta, karshe basu tsira da kome ba, sai kayan barcin da yake jikinsu.

Bayan wannan babbar yayarsu Majid, tayi tafiya tana dawowa suka kwantsama wani mummunan hatsari, a shekarar ba a tab'a samun ribar da aka samu a wannan lokacin ba, sai gashi riba kamar hauka wanda yaja nasa aka yi karin albashi, a yadda abin yake faruwa yasa Hajiya kiran gida tana kuka ban san me ya faru ba amma hajiya ta kasa barci domin irin yanayin yana.bata tsoro ko Rayuwar Majid bata ji haka ba.
Ni kaina a yan kwanakin wasu miyagun mafarkai nake, wanda yasa ni fara tsoron na saka hakarkarina a katifa, domin take zan fara mugun mafarki, a ko ina idan na dan kwanta barci me dan ƙarfi ya dauke ni mafarkin wai ga wani mutum yana tona rami, sai kasa ta rubta ta rufe shi, can aka zo aka bude shi sai ga jini yana zuba da gwala-gwalai.
Mama na kira na gaya mata, ita ta gayawa Malamijo, shiru yayi kafin ya ce mata. Ta min nasiha nayi hakuri da duk abin da zai faru kada ta gaya min, haka na kwantar da hankalina, sai dai bayan kwana biyu na fara mafarkin Majid yana son zuwa gamu cikin tashin hankali. Majid yazo ya mika min hannu. Amma Aryan yana kuka kada na tafi na tsaya, har da rungume ni ta baya, kada na tafi na barshi. Ina ganin wani mutum ya kama Aryan ya danne shi, sai da ya daina motsi, yana nufo ni Majid yana isowa inda nake ya rungume ni. Anan na farka.

Da safe na gayawa Hajiya a saya min rago, a yanka a gyara ayi abinci a dafa a kai sadaka. Idan kuma abincin zai bata lokaci a saka namar a leda, da danyen abinci a saka jaka uku, a raba sadaka. Bayan na fito na ga Nana ta fito rike da sandarta. "Uwargida a wurin Abdulmajid da Abdul Majid Yaro." Yake ta min ta zuba min idanu kafin ta ce min. "Ina mafarki da Alhajin Allah yana tafe, sai dai kamar wata fitinar da take tafe a gabanshi. Na saka yau ayi min yanka zanyi sadaka"
"Na gayawa Mamana nima, ina wannan mafarkin nace ayi min saukar Alqur'ani, zan yi sadaka an jima za a kawo ragon!"
"Tow ayi ta saniya mana;"
"Kuyi magana da Hajiya kawai "
Ni da Nana muka yarda Majid yana raye, amma kowa gani yake mun zare wai abu kusan shekaru biyu amma muna da yakinin yana raye. Da sauri na tafi wurin Aryan na shiga motar ina gaishe shi.

"Lafiya Baban Amir." Na cigaba da danna wayata. "Fadime?" "Na'am" na amsa ban kalle shi ba. "Tunda shekara biyu kenan har da watanni me zai hana mu tattauna a tsakaninmu, sai na maye gurbin shi." A wani fusace na kalle shi, "sau nawa ina gaya maka kada ka sake min irin wannan maganar? Tow bari na gaya maka koda ace zan shekara dubu ne babu Majid wallahi na fi karfin na had'a makwanci da Yayanka sannan na hada da kai, ni babban gora ce sai magogin ƙarfe." Na juyar da kaina ban kuma kallon inda yake ba, Aryan tunda Majid ya samu shekara daya ya fara min wani irin abubuwa, tun bana kulawa har na fahimci so yake ya nuna min shi ɗan akuya ne. Allah na tuba ko mutuwa Majid yayi na ga gawarshi ai na shafawa kaina lafiya balle ban ga gawar Mijina ba zan kama zancen wani namiji tun da aka rasa shi ni maza ma kallon mata nake masu wallahi duk yadda Yazid yake sona amma fir naki, sannan abin da ya kara min kwarin gwiwa Majid zai dawo shine Yariman Baihak Crown Prince Maina da yazo kamfaninmu ya bani shawarar kada na damu da rayuwar wasu na gina tawa domin mijina, yasan jarumi ne a ta kowace fuskar kuma zai zo gare ni, sannan na ga yar karamar Matarshi wacce yake haukar so yarinya ce karama don bata wuce sa'arsu Barakatu ba, sai kinibibi take kamar zata shige jikinshi. Shi kuma shashasha sai rudewa yake, wato larabawa basu da kai akan matar da suke so sai bayan fitar shi ta nutsu tana rufe fuskarta. "Aunty Zahra ki bar min kallo haka!"
"Ba dole nayi miki ba, kin mai da magajin Baihak kwarkwar."
"Sirrin kwailantaka ce" sakin baki nayi ina kallon ta, ta sake murmushi da yanzun zance ya shiga gari ya nimo min dawo, kafin na rufe baki zai tafi, ai shi yasa bama daukar las a wurin miji, ita head girl tana can ta bamu wuri mu darji amarci"
"Ya isa haka.ban ce ki baro min magana ba!".....🤣 (Ni dai na san I dey take las, domin akwai wani sirri a jikin kwailayen mata don Allah me yasa Zahra ta hana kwaila baro zance 🙄🤣😂😏 Ni bana son hassada)
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce

[5/29, 07:48] Hlm: BHB275
Kai jama'a yarinya sai kace Radio, gata yar banza ba wasu shekaru ne da ita ba, yadda na had'e rai yasa ta nutsu daga ganinta yar kauye ce. Hankalina yana kan aiki ta ce min. "Mijinki yana raye?" A zabure na zuba mata idanu, bakina yana rawa. "Me yasa zaki d'aga min hankali?" Na fada kamar xan yi kuka. Ina ji a jikina yana raye amma ban san dalilin da yasa nake bin rinjayen abin da mutane suke fada ba.
"Wallahi mijinki yana raye, kuma bai yi nisa da nan da kike ba, sai dai a inda yake ne gaskiya ban sani ba, amma ke bakya jin motsinshi a ranki? Bakya jin kamar yana tare dake ?" Juyawa tayi ta kalli kofar shigowa, murmushi tayi ta nufo ni tana me mika min hannu.
"Idan har kin yarda da mutane masu baiwar gane-gane tow ki amshi wannan zoben. Duk me hannu a boye mijinki zai na gudunki. Ki dauke danginki daga Hajiya, Alfah Amaan, Jamilah da Anisah. Su tafi wani hutun Allah zai baki Sa'a amma Aryan ya xama yana gefenki, Aryan mutumin kirki ne bai miki maganar yana son maye gurbin dan uwanshi don ya tsani dan uwanshi ba, a'a yayi haka ne don rage miki kaɗaici da kewar Dan uwanshi. Yasa yake bayyana miki sakon zuciyarshi. Ba mutumin banza ba ne." Ta riko hannuna ta saka min zoben, sannan ta juya tana kallon kofar, shigowa tana murmushi ta ce.
"Alahan wassalan ya Habibi da'im!" Haɗiye yawu nayi ban tab'a ganin tashin hankali irin na yau ba, da sassarfa hade da kuruciya me haɗe da sakalci ta isa jikinshi, rungume shi tayi tana murmushi. "Sauran canji ne a jikina ba sai kin sace su ba." Dariya suka saka tare da min sallama. Raka su na fito nayi naga Aryan shima ya fito. "ina fatan baki mata sane ba?" "Kai haba ai abar tausayawa ce, munafukai suna dayawa a cikin kamfaninsu. Amma ita zata kawo karshen rikicin kamfanin ta hanyar fitar da bara gurbin kamfanin!"
Janye jiki tayi ta nufe ni. "Ki kama wancan dan iskan da yake leke ta window ki fara da shi." Da wutsiyar idanu na kalli Admin.
"Na gode haka suka shiga motarsu suka bar kamfanin."
"Shi abokin Hammayo ne sun yi course akan kasuwanci ne."
"Allah sarki! Ka shiryawa su Hajiya tafiya Umara ita da su Jamilah kowa da kowa. Har da matarka da Yaranka har da Amaan! Ka shirya musu kamar tafiya yawo ƙasashe uku!"
"Tow an gama yan mata!" Haɗe rai nayi, na juya zuwa cikin office ɗina. Ina shiga na dauki jakata na fito ina kallon Admin.
Chapter 131 · 0% Book details