Sashe 66
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sakin baki yayi yana kallonta kafin ya tattaro nutsuwarshi da abin da zai gaya mata Hajiya ta bar dakin bakiɗaya yanzu shi me zai cewa Hajiya? fisabilillahi Hajiya bata mishi gentle ba, shi fa auren familyn Ba'are gani yake kamar shiga lahira ne babu guziri, yo da guzirin ma ya aka kare balle ka shiga babu abin da zaka kare kanka. Yasan wani tarko ne ba wani abu ba ne,uban waye zai kashe ta a wannan lokacin da kowa yake ibada. Gyara kwanciyarshi yayi kamar ba zai tashi ba, can kuma ya mike tare da sauka ya saka takalman ya nufi hanyar waje. A falo ya samu Hajiya tana waya. Fita yayi yana kallon yadda garin yake, hannunshi sakale a cikin aljuhun wandonshi. A hanyar shi ta shiga gidan ya had'u da Aryan da yake dawowa daga rakiyarta. "Ina zaka Hammayo?" Sosa wuyar shi yayi yana kallon Aryan ɗin. "A irin wannan yanayin me yasa baka wuce gidanka ba?"
"Na raka maisarah gida ne, domin wurin ya cika duhu kuma mace ce ta dauki kasadar fita a wannan lokacin. Tana bukatar wanda zai rakata gida." "Hmm!" Ya faɗa suka wuce zuwa gida, zama suka yi a harabar gidan. "Hamma kamar akwai abinda yake damunka?" Girgiza kai yayi, yana kallon sama. "Ban san me yasa hajiya take jan wasu abubuwan ba? Nafi Hajiya son nayi aure, amma kuma a haka na lura kamar bata yarda bani da lafiya ba ne, idan na auri Maisarah me zan mata? Sannan abin da nake boyewa zata iya cutuwa idan tasan halin da nake ciki." Ya fadi haka a hankali, shi kanshi Aryan sai yake ganin kamar sa'a yayi da Hamman shi yake gaya mishi irin wannan al'amarin, wanda kowa yasan halinshi da boye abinda yake ranshi.
"Wayyo Allah taimako!" Suka ji Ihun Maman Maisarah, kallon juna suka yi, kafin su shiga Mamarta suka samu tana ihu. Shiga cikin gidan suka yi har da ita, dakin yarinyar ta nuna musu. Kur suka mata, aka rasa me bakin magana. "Don Allah ku taimaka min, kada ta mutu." Da sauri Aryan ya wuce kitchen dinsu, ya dauko wuka ya yanke igiyar da ta daure wuyarta da shi. Fita da ita aka yi, a lokacin su Nana sun iso. "Lafiya?" Yanzu Aryan ya rakota muka gaisa, da yake taje gaida Hajiya Sa'adatu, shine bayan tafiyarshi, naga an kirata a wayarta, ta dauka ban san me aka gaya mata ba, amma naga ta fita zuwa tsakar gida, daga nan ban bi ta kanta ba, ashe igiyar shanya ta dauko ta rataye kanta."
"Kun yi ja'ira yar banza, waye ya gaya mata mutuwa shine mafita, me ma aka mata da zata kashe kanta, bayan ni ban mutu ba, ku kaita asibiti." Kallon Aryan Majid yayi, cikin wani irin yanayi da baya son ya zarge shi. Amma sai ya dauke kai kamar bai damu ba, haka suka tafi asibiti suna zuwa aka karbesu kusan kwana suka yi akanta, kafin wurin karfe biyar na Asuba likitocin suka fito daga cikin dakin da take. "Ya take ciki?" "Alhamdulillahi zamu ce, sai dai bakiɗaya ko zata rayu bai zama dole ta mori kanta ba."
"Akan me?"
"Saboda kashin da yake haɗe da bayanta, da spinal code dinta ya karye." "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un, me yasa na kiraki? Kin rayu cikin firgici da tsoron kada a kashe ki, yau gashi ke baki mutu ba. Ke baki rayu ba." Mamanta ta faɗa cikin kuka da danasanin abinda ya faru, domin da tasan haka zai faru ba zata so Maisarah tazo ba, haka yasa ta cigaba da kukanta har gari ya waye, wannan faruwar lamarin ya kara saka tashin hankali a zuciyar mutane, musamman yan cikin gidan. Abin da yafi hurting ran mutane, shi ne a daren Aryan ne ya kaita gida, haka yasa baki daya ya shiga yanayin zargi da tuhuma. Karfin imani da tawali'u yasa Aryan bai haukace ba, amma sai da ta kai ya zauna yana kuka kamar karamin yaro a gaban Hajiya. Shi kanshi Majid tausayin Aryan din yaƙe ji amma baya son maganar gaskiya shi daya ne abin zargi a cikin gidan. Domin shine ya ganta na karshe kafin faruwar lamarin. Amma kuma maganar gaskiya bazasu ce shi ya aikata ba, sannan ba zasu ce bashi ba ne. Dole bincike ne zai tabbatar da haka.
Ba karamar girgiza Alhaji Kamilu yayi ba, domin bai tab'a kawowa hakan zai faru ba. Sai dai da Hajiya tayi mishi maganar binciken abin da ya faru. "Wani bincike kuma? Babu wani binciken da za'a yi, domin nasan ƙarshe a cikin gidan nan aka samu wanda yayi wannan aika-aikan."
"Ai gara a bincikan hakan zai saka mu daina zargin Aryan domin kowa yaji ta hadu da Aryan abin da yake ayyanawa a ranshi akwai wani kudiri ko wani abu na daban."
"Na sani, sai dai hakan ba zai haifar mana da d'a mai ido ba, Allah ya bata lafiya kawai." Ya fada yana kara jin wani irin d'aci a ranshi domin Allah ya gani yaji zafin al'amarin, sannan duk wanda yayi wannan aika-aikan yasan abinda yake yi, shi yasa yayi amfani da rakota da Aryan yayi da zuwanta gidan Hajiya.
Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke, sannan ta ce mishi. "Shi kenan, tunda baka son binciken Allah ya bata lafiya. " Ta fada tana mikewa, tare da leka dakin Maisarah da take cikin Unconscious. *Idan wani abu ya fito bayan kawo miki wannan Cameran tow tabbas abin da yake ciki babban al'amari.*
Wani irin zufa ne yake zubowa Hajiya, duk abinda yarinyar nan ta gani ba karamin al'amari ba ne, haka yasa ta nufi gida zuciyarta na wani irin zillo.
***
Zahra
A matukar gajiye na dawo, dake Allah ya taimake ni Amirah sugrah tana wurinsu, ina shigowa aka kawo ta, yarinyar nan taki zama, "kuje da ita kawai, na gaji gajiya zata kara min." "Tow Tante!" Suka fita da ita, ina kwance a wurin har wurin biyar, tashi nayi na nufi kitchen. Dama tun safe na surfa wake tare da dafa kwai, wanke-wanke na shiga yi, ina gamawa na zuba mishi kayan miya. Na zauna na markad'a shi. Ina tsaye har yayi laushi na juye ina nazarin nayi ta manja ko mangyad'a. Karshe haka nayi ta mangyad'a, na zuba kwai da kifi. Sannan na duba geron da na bawa Barakatu ta surfa min, na dauka na wanke shi tass. Sannan na zuba ruwa na watsa gefen. Bude frij nayi, na dauko yogot na ciro na ajiye. Na gyara alala ta na ɗora bisa wuta, sannan na koma daki nayi wanka. Na saka kayan shan iska, na fito nazo na dama kunun garin kunun da ruwan tsamiya na.
Har kunun yayi min yadda nake so, na ajiye shi na daura shinkafa jallof, na cigaba da aiki. Ina haɗawa na dawo na kunna tv, na fara kallon tafsirin Malam Awwal Albani Zaria. Gyara kwanciya nayi ina kallon, sai da naji kamshin alalen ya cika min hanci naje na sauke, kusan uku suka fashe. Haka na ajiye na gama haɗa kome na fito dashi a faranti. Ina ajiyewa ana kiran sallah, komawa daki nayi na dauko jakata na tuna akwai fruit da na sayo. Haka na fito da dabino naci, na sha ruwa. Ban tashi a wurin ba, suka dawo min da Amirah, tayi barci kwantar da ita nayi na mika musu nasu abincin. Ina faɗin, "ku gaida min Mamanku."
"Mun gode sosai!"
.... Bayan nayi sallar Magariba da Isha da su tarawee,, na kwanta a falon. Har na fara barci sama sama, naji kukan Amirah dakin nashiga na cire mata kayan jikinta, na mata wanka na sauya mata na barci. Sannan na dawo dakin bayan nayi wanka da alola, na kwanta barci me nauyi ya ɗauke ni. Washe gari na tashi da wuri da yake Muna da test. Da wuri na wuce ban dawo ba, sai karfe biyu a gida nayi sallah.
Haka aka azumi yayi ta tafiya, rayuwar da dadi babu dad'i, ban rasa ci ko sha ba. Amma sai nake ganin kamar daular tayi min yawa, ina matuƙar son da ko wani ne a cikin dangina na gansu, su dandani dadin da nake ciki sai dai.nasan kamar yadda Allah ya halicci wuta da ruwa basu gamuwa, haka nasan matukar muka hadu sai mun yi abin kunya, haka yasa ta wani bangaren nake ganin kamar nauyi aka sauke min akan Addah, gefe guda kuma ina jin kamar ban kyauta ba, ba dadi mutuwar mutanen da kasani. Amma kuma mutuwar Addah shine samun sukuni na da Amirah.
Kwanciyar hankali da nutsuwa ya shige ni, sannan wani abin da ya kara bani mamaki ashe tun fil azal ina da kalar fata mai kyau, domin kuwa nayi fesh kamar bani ba. A makaranta ma gani na da Amirah yasa mutane dayawa sun shafa min lafiya, domin daga malamai har dalibai farkon zuwana sun fara matsa min da gaisuwa. Ni kuma na iya dauke kai bana kula kowa harkar gabana ta ishe ni.
Saura kwanaki uku mu samu hutu, wani malami ba a department ɗinmu yake ba, amma bakiɗaya idanunshi yana kaina duk da bana son kula shi. Amma haka yake saka a kirani, Ni kuwa idan naje bana magana sai na tsaya mishi a kai.