Sashe 83
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
zaka kira min mugun nufi, mutuwa ban da dole waye zai so ta, idan ma don ni kake kiranta tow ahir dinka futsararen banza." "Allah ya baƙi lafiya, da nisan kwana tunda bakya kaunar mutuwa." "Sa'a ki jawa d'anki kunne wallahi ya fita idanuna ko, hukuma ta shiga tsakanina da shi." "Nana me yayi zafi da za a saka hukuma." "Nanata tawo ki kyale su don Allah." Inji Majid da yake sama a tsaye. "Yawwa Alhajin Allah, fari me farar aniya akawali kak'i musayar, Bijimin sa me bawa raguna da awakai tsoro, gaishe ka Namijin duniya daga kanka kallo ya ƙare." Duk da Hajiya wannan bai dame ta ba, amma yau jin kirarin Nana sai ya shafe mata duk wani kunci da damuwa da take ji akan Majid, kirarin ya dace dashi, sau dayawa tana son ace tayi mishi kirarin amma yau da Nana ta yi mishi sai ta ji kamar fansarta tayi da wani abu me daraja, wani abun sai ranar da ta ganshi da farar shaddar aure, ranar bata san me zata yi ba, bata san wani farincikin zata shiga ba, duk ranar da Majid yayi aure. "Nana dole yau na sayo miki kilishi, da wannan uban kirarin da kika yiwa Zakin Hajiya." Washe baki tayi tana faɗin. "Yawwa Aliyu Haidar, na san zaka saya ai basu boloko ba." Ta fada tana hararar Aryan. "Oho dai shima don ki yabe shi ne, amma ai ba don Allah zai saya miki ba. Idan kin dage na saya miki zan saya miki amma da sharadi?" "Sharadin ya wuce ka saka min guba na mutu." Ta fada tana hararar shi, tare da haurawa sama, har falon Majid ta shiga. Tunda take bata taɓa sanin Majid yana da matsalar zama cikin duhu ba, sai yau domin falon shi kawai ta shiga ta ga ko ina duhu. "Alhajin Allah!" Kunna hasken falon yayi, ajiyar zuciya ta sauke tana fadin ya kome na falonka me duhu?" Murmushi yayi ya ce mata. "Ba kome!" Shiru yayi yana me bude mata wata jakar bagco, kunshin takarda ne kato, a hankali ya warware kafin sai ga jarida da maiko-maiko. Kilishi ne sai kamshi yaƙe. "Naki ne wannan Hajiya." "Anya Alhajin Allah, baka sangarta ni ba?" "Idan ban sangarta ki ba, waye zan sangarta." Ya tura mata kilishin, sauka tayi daga kujerar ta zauna a kasa,ta fara ɓantara tana ci hankalinta a kwance, don ba karamin dadi take ji ba, yadda Abdul Majid ya damu da ita, shi kuwa yana yin haka ne don nasihar Hajiya akanshi, kullum bashi hakuri take da nuna mishi muhimmancin hakurin da suka yi yau ga Nana ko Yaranta bata kulawa kamarshi. Sannan shi daya ne yake iya juyata cikin ruwan sanyi a zauna lafiya. "Alhajin Allah, akwai wani abu ne a tsakaninka da Afiyyah?" "A'a!" Ya ce mata. "Yo ai nasan za ayi haka, da dai Ariyan ta ce zan ce ai haka ne don idanunshi a tsatsaye suke kamar na bazawari don ma baya saka kwalli." Ta fada tana wani haɗe rai. "Assalamu alaikum!" Turus Zaytoonah tayi don bata zata Nana tana sama ba. "Zaytoon ya dai?" "Umma ce ta ce na kawo maka." "Mtsew! Asaran fage fallin daki, mace bata isa mace ba, sai naji ance namiji yake bibiyarta." "Nanata meye haka?" Yau kan Nana ta cika Zaytoonah cikin fushi ta ce mata. "Idan kin so akan Hammayo ki aure shi ki huta da min habaicin da kike. Ban da rashin girma kina da jikokin amma kike saka min ido da magana." "Zaytoon!" Ya daka mata tsawa, "kina da hankali kuwa?" "Bani da shi akanka ba ni da shi, ban san inda yake ba. Tun zuwana garin nan matar nan take gaya min magana ban kulata ba, dadin abin kai ne nace ina so ba wani ba, ita da ta gagara tsayawa akan jikokinta suka lalace shi ne zata bude baki tana gaya min magana? Meye ne ban sani ba, sai yanzu da ka zama na mora zata Ishe ni da kinibibi. Indai don kin ga ina gidan jikokin ki ne, kike gaya min magana Nana zan bar gidan kuma in sha Allah sai Allah ya saka min." Ta juya tare da barin falon, har ta isa waje ta tsaya cikin kuka ta ce mata. "Ki gane duk abinda kike yi ba burge kowa kike ba, suna biye miki ne saboda sun tsotsi tarbiyya da nagarta ne, sannan ki gaya min a addinin musulunci a ina aka ce mace idan ta ga namiji tana so kada ta faɗa mishi. Ki saka idanu akan Afiyyah da take gabanki ba ni...." "Get out!" Ya daka mata tsawar da har akasa ana jin su. Kallon shi tayi cikin fushi ta ce mishi. "Ba iya falonka ba, hatta gidanku zan bar muku. Ku zauna da masoyanku." Ta juya da gudu ta sauka daga sama, zuwa falon kasa bata saurari abin da Amaan da Aryan suke fada ba. Ta wuce dakinta, ta shiga had'a kayanta duk abinda suke yi Hajiya tana ji bata ce uffan ba. Asalima bata son shiga rigimar da ta hada har da Nana ne.