← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 138

Sashe 42

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*020*
"Kai ko kunya baka ji ne? Ace kome nice zan maka. Dukkansu hudu kokari suke su kyautata min amma kai dayake baka da lissafi ka kwaso jiki kamar fulawar da aka watsa mata yeast kazo na baka kudina ko Amaan Mamman Ba'are." Wata irin kunya ce ta kama shi, "Hajiya don Allah." Tsuke fuska tayi tana harararshi. "Kowacce uwa tana iya kokarinta akan Yaranta, sannan iya kokarin da nake akan ku ko da ace aiki aka sani baku isa biyana ladar ba, domin iya ƙoƙarina nayi kuma ina kan yi, Amaan ni na haifeka amma ni nake kuka akanka kannenka ban yi kuka akansu ba, sai kai." Murmushin takaici tayi tana kallonshi kafin ta cigaba da cewa. "Su waɗanda ka ke kai musu sirrinmu basu baka kudine? Mara zuciya wanda lissafinshi daban da na kowa. " Yadda take fada har wajen gidan kowa yana jin ta, tabbas Hajiya ta fusata kuma takai bango. Robar ruwa Aryan ya fito da shi ya mika mata, ta amsa tana me kai bakinta. "Zaka iya tafiya Mr Mamman Ba'are!" Yau ko yar borin kunyar nan da yake yi na takalar Aryan bai yi ba. "Daga yau kada na kuma ganinka a kamfani bayan mun tashi, sannan wannan Bluetooth da ka saka musu shine na cire kwanankin baya. Amaan ka fita idanu ko na sallama musu kai." Subul subul ya fita, yadda kuka san (Gfresh Al-Ameen Kano state material, haka Amaan Mamman Ba'are yake🤣) haka ya fice abin shi, a harabar gidan ya hadu da Majid da Yaran Aryan suna wasa, sai ihu suke yana tayasu.

Tsayawa yayi yana kallon yadda suke wasa cikin jin dadi da nutsuwa, me xai yi ya samawa Matarshi nutsuwa ne. Ba zai iya rayuwa babu ita ba, haka yasa shi juyawa ya fita kai tsaye bai tsaya ba sai can wajen gari, gidan Sajjid Mamman Ba'are. Ya shiga cikin gidan a harabar gidan ya ga motarshi tabbas yana gidan, zai shiga masu tsaron gidan suka hana shi dole ya zauna a harabar gidan ya jira shi. Har zuwa wani lokaci kafin Sajjid din ya fito da gajeren wando da yar singlet. Ya tsaya yana kallon Amaan Mamman Ba'are. Kafin suka kwashe da dariya tare da rungumar junansu. "Nayi kewarka Baby na!' inji Sajjid, "Nima haka My love!"
***
camp
*Idan har akwai wanda zai ci amanarka tow kada ka damu kowa, koda zasu haɗu baki daya su ci amanarka matukar ka yarda da Allah magana ta kare, amma wanda ka bawa yarda ya ci amanarka sai kaji kamar zaka mutu, zuciyarka ba zata yi jimirin daukar kowacce nauyi ba. Ina jin wani irin ciwo me zafi*
Bude idanuna nayi ga babu kowa a cikin tantin mu, daga ni sai Baby. Kayan Addah ma babu babu kayansu Ummi, wani kar'ar fashewar abu naji, kafin na fara jin Ihun mutane da kukan Yara yana kusanto ni.

Ƙarar harbe-harbe yana kusanto inda nake, bansan ya aka yi ba amma sai ganin tantin mu ya kama da wuta nayi, haka na sunkuci Baby na fita da gudu, kamar yadda kowa yake gudu haka nima nake gudu, gudun da ban san inda muke jefa kafar mu ba,mu dai gamu nan ana kad'a mu kamar wasu awakai. Mun yi tafiya me nisan gaske a cikin daji, babu ci babu sha tun daga wayewar gari har rana ta faɗi, sannan baka san waye a kusa da kai ba, shima kuma don rud'ani ba zai ce ya san waye kai ba, sai yau na kara jin kamar da mutuwa nayi da abinda Zuzu da sauran Yan uwana suka min,amma me yasa zuciyata taki yarda Zuzu zata yaudare ni. Duban Babyn nayi naga bata motsi. "Wayyo Allah na, Yarinyata bata motsi jama'a ku taimaka min kada ta mutu!" Ihun da nayi ta musu kenan ina cika musu kunne, hasko min torchlight aka yi na runtuma da gudu kamar mahaukaciya, na ce musu."ku duba min ta mutu ne!?" Na fada ina ihu. "Ke ki nutsu!" Aka daka min tsawa, amma ina baki daya kamar wacce aka toshe min kwakwala, haka nayi ta musu ihu da rokon su duba min yarinyar ko ta mutu. Can hasken wani dakin da aka kafa shi a dajin ya kunnu, fitowa yayi sanye da jallabiya. "Yallabai ka tafi zamu magance matsalar!" Yana zuwa ya amshi Babyn. Sannan ya juya da ita, "ina xaka da ita? Ina zaka kaimin Baby na! Bani ita ta mutu ne?" Fisgo ni yayi ya tura ni dakin tare da rage hasken dakin, dumin dakin ya kara sani shiga hankalina. Daukar wani torchlight yayi yana haskata, kafin yayi magana cikin wata irin murya me sanyi, duk da Muryar shi da take da matuƙar sanyi da dad'i haka bai saka na fahimci cewa dani yake magana ba, sai da ya kuma haska min torlight ɗin na ce mishi. "Kace ta mutu?" Ajiye fitilar yayi ya ce."yaushe aka haifeta?" "Jiya!" "Ina Mamanta?" "Gani nan!" Na nuna miishi kaina,kamar bai yarda da ba sai kuma ya koma kan yarinyar ya ce min. "Yaushe rabonta da shan nono?" "Jiya da daddare!"
"Zo ki bata!" Ya faɗa min yana mika min ita, burina Baby ta rayu. Ciro mata nonon nayi na saka mata a baki bata amsa ba. "Bata karba ba" janyo wani kofi yayi ya matsa jikin wani irin murhu, ya kara kofin kafin wani lokaci yayi dumi, janye kofin yayi ya mika min yana faɗin. "Taimaka min ya huce!" Haka nayi ta hurawa har ya huce, sannan ya amsa ya saka mata a baki ruwan ya fara shiga bakinta, tana fara sha kuwa sai gashi ta kware, d'agota yayi yana shafa bayanta sakin baki nayi ina kallonsu, sai da ya gama dubata ya bani ita, na saka mata nono ai kuwa ta rike da sauri, zafin da ya ratsa bakin nonon da kaina yasa ni sakin yar ƙaramar ƙara. Bai kalle ni ba, amma kuma ya juya baya ya kwanta abinshi, har ta gama sha ya ce min. "idan kin fita kice Ado ya kai ki wurin Uwar mugu zata kula daku. A mata wanka a nad'e ta kafin gobe!" Fita nayi a bakin kofar na samu Ado. "Muje!" Ya ce min, har wurin Uwar mugu ya kaini, ya gaya mata sakonshi. A daren ya kafa mana tanti shi da wasu mazan, uwar mugu wanka tayiwa baby ta kara bata madara. "Ina Addah da Ummi?" Murmushi tayi ta ce min. "Suna lafiya a cikin wannan yanayin, sun zata kin mutu ne."
Mika min ruwan zafi tayi na sha a hankali, har na gama sannan wani irin barci yayi gaba damu, daukar Baby tayi ta kai mishi. "Kika ce Nawwas ya sayar da uwar Jaririya?" Cikin tsannanin biyayya ta ce mishi. "Eh Sarki a dawa Sarki sarari. Ba iya uwar yarinyar ba, wannan bakar al'adar shin nan, ta sayar sassan jikin dan Adam yana nan bai daina ba, sannan akwai kanwar Babanta da take da bala'in son kudi."
"Uwar yarinyar tana raye kenan?" "Eh amma an fitar da ita tun yammacin shekaranjiya."shiru yayi yana kallon Babyn. "Nawas babu imani a cikin lamarinshi."
"Ba laifinshi bane kakar yarinyar ta bukaci haka." "Je ku kwanta."
------ Tafiya muke cikin koriyar ciyawa, ina gaba rike da Baby ina mata dariya, sai ji nayi kamar an hand'akani cikin wani rami me duhuwar gaske wanda bana iya hango farkon ramin ga Baby tana ta callara kara.
"Ki rayu a wurin." Cikin wani irin kuka na ce. "Wurin akwai duhu bana ganin Baby." "Ki zauna a wurin haske zai zo miki." "Taimako!!!!" Da wannan Ihun taimakon na farka, naga Baby har an mata wanka an kara nad'e ta, babu kowa a dakin sai abinci da aka ajiye min, tashi nayi na fito waje. Naga an zubawa kofar tantina idanu ga mutane kowa ka gani a firgice yake. "Gimbiya ke ake jira!" Addah ta faɗa tana hararata. "Addah!" "A'a gatari ko guduma." Ta fada tana juya min.baya, Allah ya gani ina da rauni wurin Ibada, alola nayi na wuce ciki na gabatar da sallar da yake kaina sannan nayi na asuban yau da garin ya gama haske tas, sannan na koma dakin na goyi Baby a tsaye naci abincin na rikema addah sauran, don nasan bata samu kamar wannan ba, lokacin da na fito aka nad'e tantin, wato tunda na nufi wurin Addah na fahimci matar nan bata da mutunci, mika mata abincin nayi ta fauce. A can gabanmu na hango Ummi ban kula ta Addah ba, na tafi na same ta. "me yasa kika tafi kika barni." "Ba gashi kin same ni ba!" "Amma;" gyara goyon Yakumbo tayi tana me cigaba da tafiya, kafa babu takalmi sai lokacin na fahimci nima haka nake tafiya,ga tarin kayoyi.

Kamar wasu shanu haka muke ratsa tafiyar cikin dazuzzuka da kwazazzabai. Babu abinci babu ruwa, "Ummi ko zaki kawo yakumbo ki rike min Baby!" A gajiye ta ce min. "Eh!" Haka na bata yar ni kuma na amshi Yakumbo, muka cigaba da tafiya muna ratsa hamada da kwazazzabai. Sai da yamma tayi likis aka tsaya, na ajiye Yakumbo, hawaye na zuba min domin Baby kuka take, tun daga taimakon farko da na samu ban kuma samu ba. Haka nayi ta jigila da Baby dakyar muka yi sallah, kuma baki daya haɗawa muka yi, Abin tambaya anan ina za a kai mu? Babu me amsar tambayar nan, sai dai a cikin tawagar maza naji ana bayanin wasu sun mutu.
A hankali naji wani abu ya tokare min kirjina, ruwa da yar karamar busashen gurasa aka bimu da ita, mukaci muna lashe hannu, domin dai bai Ishe mu ba. Haka muka kwana cikin wani irin sanyi, muna tsaka da barci wata ta fasa ihu. "Wayyo Allah maciji ya sare ni!" Tashi kowa yayi zaune, aka fara haska torchlight, sai gashi nan wuluk, ya kara fasa kai zai kai wani saran daya daga cikin mutanen da suka fito ya samu ya harbe shi, sai da ya fasa mishi kai, matar ma bata haura minti biyar ba, ta fara shure-shure kumfa yana futa bakinta, kafin wani lokaci ta ce ga garinku. Cikin tsananin tsoro muka kara tattara kanmu wuri guda, haka aka bar gawar domin muna farkawa nan bamu kara kwanciya ba, sai tafiya haka muka yi ta ƙeta daji da kurmi.
Chapter 42 · 0% Book details