← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 138

Sashe 106

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tabbas rayuwar shi zata fara gyaruwa kenan, haka yasa shi godiya tare da kwanciya a wurin, ya rasa farinciki zai yi ko bakinciki. A nan yake kwance har barci ya kwashe shi.
... Rigimar da muka yi da Yazid ba karama ba ce, haka yasa har ya kira nurse suka min allurar barci, haushinsa na boye min inda su addah suke ya sani jin ba dad'i. Washe gari.
Karfe sha daya na farka, Addah na fara karo da ita, ban ganshi a dakin ba. Kallon addah nayi da kyau naji gabana ya fad'i babu ido daya, tayi wani irin baƙi. "Zahra kin farka." "Eh Ummi, ko zaki kira min nurse ta cire roban nan nayi wanka da sallah"
"Tow!" Ta fita.
"Sannu yar duniya mage taji kulkuli, kin yi shan dandan uwa kud'a a jikin gyambo. A lokacin da nake tunanin nawa Yar rayuwarta ya lalace ashe ke taki rayuwar kyau tayi har ana ina-ina dake yar gwal."
"Addah zaki fara jidalinki ko?" Inji Ummi da ta shigo da nurse. Cire min ruwan tayi, da taimakon Ummi tayi wanka tare da alola. Sannan na fito zuwa waje. Sai jifana da harara Addah take kamar ta ga kashi. Bayan na idar da sallah, na cewa Ummi. "Babu wani abun ci ne yunwa nake ji." Haɗa min tea tayi na sha na koshi, ina ajiye kofin Yazid ya shigo shi da Amirah da take ta rikici, tana ganina ta faɗa kaina da gudu. "My heart, sannu kin ji "
"Mamina ina kika shiga?"
"Zahra Yar wajen Zula...."
"A'a yar Zeehrah ce." Ya fada yana hararar Addah da ta bude baki zata yi magana."Mamina su waye wannan?" Ya nuna min su, "wancan mama ce, wannan kuma Ummanki ce."
"Hmm! Bana son wancan Mamanki, tsoro take ba ni."
"Akul na kuma jin haka," dake ban saba mata fada ba, kuma bana mata tsawa. Da sauri ta juya wurinshi, ta fashe da kuka. "Dole ne sai taso ta? Ai ba dole ba ne." Shigowar Majid yasa samu zubawa kofar idanu shi da Nana ne, yana rike da kwandon abinci.
"Ayya wannan yarinyar kina ganin Jarabawa, sannu Allah ya baƙi ikon cinyewa Alhajin Allah kawo abincin nan taci."
Ta fada tana kallon yan dakin, kafin ta sauke idanunta akan Yazid. "Wai wannan baturen shi zaki aura ne?" Ta tambaye ni, murmushi nayi nace mata. "Nana zauna, ke ce da rana tsaka nan!" Na kauda zancenta. Zama tayi tana kallon Addah. "Wannan me kama da yan alaziyi wahidi din fa?" Dole idan ka ga Addah kayi tunanin yan bara ne ko irin masu bin yawon gidajen mutane maula. "Gwaggona ce." Na fada cike da kunya, "Ai!" Addah tayi baki, ta lalace babu wannan kyan da yake rud'ata.
Babu jikin nan me kyau da haiba shi yasa kowa ya ganta, sai yayi min magana. Abinci ne mai rai da motsa zuciya. "Ina Amaan ne?" Na tambayi Nana, tab'e baki tayi tana faɗin. "Ai bai da lafiya ne." "Subhanalillahi Ubangiji ya bashi lafiya."
Tabbas na jima ban ga Amaan ba, na zata ko Majid ne ya hana shi zuwa nima kuma ban tambayi rashin ganin shi ba. Ajiyar zuciya na sauke lokacin da ta zuba min jollop din taliya da yaji kayan hadi har da nama. "Ummi muci mu biyu." Zama tayi bayan ta wanke hanunta, sannan aka zubawa Addah. Kallon agogon hannun shi yayi ya ce mana. "Babu wani isashen lokaci su ci mu tafi." Yazid da yake bakin gadon ya dauke kai, yana faɗin. "Idan da kasan gubar da yake cikin wancan me ido ɗayan ba zaka sake su hadu da Zahra ba, ai nasan inda suke na san yadda zasu hadu, amma naki hada su. Dake kai kanka baya ja shine bari ka haɗa su? Ka sani wannan ba kome ka haɗa ba, sabon tashin hankalin ka budewa Zahra duk yadda kake tsammanin zaka kare rayuwar Zahra baka kai ni ba, amma haka na kyale wancan hatsabibiyar matan, don haka kafin wani lokaci ka nisanta su da Zahrah." Ya faɗa da harshen French, duk da bana ji sosai amma na tsinci wasu abubuwan, kura mishi idanu nayi, ya fada a hankali. "Ko ita wannan yarinyar da zaran na fahimci damunki zata yi zan rabata dake balle kuma su."
Muna gama ci, Ummi ta ce min. "Kika ce ya Babangida yana jalingo?" Gyada kai nayi ina murmushi."anya ba xan biku ba."
"Ance zuciyarki ce take da matsala, idan kika bimu wasu zasu iya kashe ki, babban farincikina. Duk tsawon shekaru baki manta da gida ba, kin tafi gare su." Tari nayi na ce mata. "Na je ne don naga ko kin koma, amma yanzu zan kira wani daga can, zai kai ki har wurinshi, ban cika alkawarin Yakumbo ba, ina fatan Allah kada ya kamani da rashin cika alkawari."
"Ko daya, da kika nisance mu ba ga rayuwarki tayi kyau ba, kin je Har Takum?"
"Takum?" Majid ya tambaya yana kallonmu. Dariya Yazid yayi yana faɗin. "Kada ka sake ka ambaci sunan wancan yar iskar, kafin ka kara lalata kome, kyale kowa zai bayyana don kanshi."
"Kasan garin mu ne?" Na kalle shi, "A'a lokacin da kika koma na tura har can ne."
"Ai ho!" Ya faɗa, haka kawai nake zargin Yazid. "Me kake nufi da yayi shiru?"
"Ni kada ki saka min jakar tsana, don na lura haushina kike ji." Ya faɗa yana dariya....
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400 8130269641
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB257
Sakin baki nayi cikin takaici na ce mishi. "Nayi maka kama da mahaukaciya ce?" Gabana ya dawo ya zauna, "Wane mutum inji mutuwa, Ina sonki!" Ya faɗa da karfi yadda kowa a dakin sai da yaji, a diririce na d'ago kai ina kallon yan dakin musamman Majid da yayi wani irin kalar tausayi. "Wannan wani irin zance ne?" " Da gaske ina sonki Zahra naga idan ban yi kome akan idanun kowa ba za a iya samun matsala."
Riko hannuna yayi yana faɗin. "Babu abinda ya dame ni, a gaban kowa zan bayyana abin da nake so, ki amshi soyayyata da hannu bibbiyu." Ya faɗa yana kallon Majid da wutsiyar idanu. Ko ni kaina da naga yana satar kallon Majid, haka satar kallon Majid nake balle shi da ga abin da yake nufi.
"Muje." Ya faɗa da wats irin murya da na san ta b'acin rai ne zalla, mikewa nayi ina kallon Addah da nasan da magana a bakinta. Matsawa nayi tare da faɗin. "Addah in sha Allah karshen wata zan zo na ganki."
"Ni zaki gani? Tow kada ki tako inda nake ba tare da Zulaihah ba, sannan ki bani yarta na tafi da ita." Da sauri na dawo da Amira bayana. "A'a ba zan baki Amirah ba, ba zan iya ba duk inda Zuzu take zan nimo miki ita, amma don Allah kada ki raba ni da Amirah." Na rungume Yarinyata, don ina ga mutuwa ce kawai zata raba mu da juna.
"Ba zata nimo miki yarinyar da ke kika sayar da kanki ba "dan ja baya Addah tayi tana kallon Yazid, "wannan tsakaninmu ne na zumunci idan kana shiga Allah zai saka mana " dariya yayi yana faɗin. "Zumunci? Daga yau ba zaki kuma ganinta ba, balle har ayi zancen zumunci." Ya faɗa da yanayinshi mai matukar razanarwa ba zaka dauka shi ne ya gama dariya ba, haka suka fita ina kallonsu, "ko a cikin dangi bana fatan Yarana su farka su ga irin wannan matar."
"Hmm!" Na fada ina rungumar Amirah, sake shigowa Ummi tayi tana faɗin. "Zahra baki bani number shi ba?"
"Zai zo ya dauke ku a Abuja, sannan zai kai ku har jalingo!" Inji Yazid,
"Na gode sosai Zahra, Allah ya tabbatar da alkhairi mu sha bikin ku." "Ke;" na fada da karfi, da gudu ta fita.
Haka ya tsaya yana min dariya, tura baki nayi ina faɗin. "Ni dai ka daina min dariya." "Nayi ɗin! Na tura wurin Babangida ne, ina tsoron kada na rasa ki."
"Abhna Mamina tana irin abin da nake yi "
"Ai yarinta na damun Yan matana." Ya faɗa yana zungure min goshi, "wallahi ka daina bana so."
"Sai kiyi."
Idan har farin ciki da saka mutum shine ke warkar da mutum, tabbas Yazid ya san kan yadda zai shawo min kome nayi dariya, haka muka wuni a tare da juna.
Bayan ya tabbatar sun bar kasar shi da Nana, ta ce mishi. "Wancan baturen santa yake ko?" Bai bata amsa ba, ya cigaba da tukin shi. "Hmm! Alhajin Allah sanyi kayi da lamarinta. Idan har mutum yana son abu nace mishi yake tare da cusa kanshi har sai ya samu, ba wai kana baya-baya da abin ba, Yarinyar nan ina jin alkhairori masu yawa a kanta, amma kake wasarere da ita. Gaskiya ka cire zurfin ciki ka fuskance ta ku fahimci juna."
Har suka isa gida Nana bata daina,bashi shawara ba don har ga Allah tana son shi Da Zahra a duk lokacin da ta kalle su sai ta ga kamar an halicce su don juna ne, kowannensu yana da tashi baiwar da da yanayi.
Chapter 106 · 0% Book details