← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 138

Sashe 80

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya juya yana bin bayanta da idanu,shin me rayuwarshi ta amfanar mishi? Me gatan da ya ke da ita tayi mishi? Babu kodaya, a kodayaushe burinshi ya sami kintsatsiyar yarinyar ya lalata mata suna don basu cancanci shiga jami'a ba ko me? A rayuwarshi ko rashin kunya yaga mace take yi tsanarta yake domin yana ganin ta gama lalacewa babban burinshi ya lalata goben kamilalliyar mace, domin yasan dama wasunsu ba karatun ya kawo su ba, lalacewa ce ta kawo su makaranta. Da farko ganin Zahra ya kwadaitu da ita ne saboda wani irin dirin da take da shi, haka yasa shi matukar bukatar yayi nasara akanta. "Boss ko muyi mata daukar amarya ne?" "Kai duk maganar da tayi bai shiga jikinka ba ne?" Inji daya daga cikin abokan Abdullahi, "Ya ne?" "A 'a tunda yake wata ta tab'a mishi irin wannan maganar? Don haka yarinyar nan ta tuna min da abinda na rasa, ban san hakkin yan matan da muka lalata ba, kaga tafiya ta Allah na tuba." Haka ya tafi ya bar su, kafin kace me sauran biyun sun gudu sun bar Abdullahi a tsaye shi ɗaya kamar gunki.
*Ni kan tunda na bar wurin, sai naji hawaye masu yawa suna zubo min,* nasan ba wayo na bane ko iyawata ba, kawai ikon Allah ne da buwayarshi. Aji na koma na dauki Jakata, na fita zuwa gida. Haka na wuni suku-suku. Sam na manta da batun zuwa aiki kamfani.

Niamey
Cikin bala'i ta nufi cikin gidan Hajiya, tun daga bakin kofa take kwala mishi kira. "Alhajin Allah, Alhajin Allah,!!" Barci yake amma haka ya farka tare zuro kofar shi daga gado, ya gaji da fitinar Nana wallahi kamar ya gudu ya bar garin. "Alhajin Allah!" Ta kuma kwala mishi kira. "Nana Barka da zuwa " "Yawwa ba wurinki nazo ba" ta fadawa Hajiya tana baza hanci ita nan tazo wurin jikanta. Kasancewar yau Asabar yana hutun karshen mako, amma haka Hajiya Nana ta zo kawo mishi rigima. "Sa'adatu ina Alhajin Allah." "Yana dakin shi." "Au sai na roke ki ne zaki kira min shi?" Gyaran murya yayi daga bayanta. Washe baki tayi tana faɗin. "Dan arziki irin albarka, kun ga d'an da aka haifa tsiya tana barci, bata farka ba balle ta ganka. Alhajin Allah dan maliki me had'arin CFA, Hmmmm" ta kuma ce cikin sigar gulma da ya kawo ta. Zama yayi yana fuskarta ta tare da hamma yana mika. "Assalamu alaikum!" Muryar Aryan da Zaytoonah ya ratsa falon, juyawa tayi ta wani turbune fuska irin bata yi maraba da zuwan su ba. "Alhajin Allah, magana ce ta kawo ni. A tow ni dai tunda na ziyarci garin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, na dawo rakiyar munafukai da yan tsugudidi, sannan nayi alkawarin agaban Uban fatsima ba zan kara cin amanarka ba, tunda dai Umaran kai ne ka biya min ko?"
Gyada kai yayi yana kallon Zaytoonah da take narke mishi, salon fitina kala kala, Zaytoonah ta sani, duk da surutun da ake na cewa suna soyayya bai tab'a cewa kome ba, amma yana damuwa da ita, domin bai da abokiya na kusa kamarta, a lokacin zamanshi a kamaru, ita ce abokiyar hirarshi. "Hamma!" Bude shanyayyun idanunshi yayi akanta domin yadda take mishin nan, baya ya iya daukar abin, tausayin ya kasa koyawa kanshi sonta yake ji.
"Ke bana son karuwanci, kin zo kin wani min bake-bake ke gaki nan yar bala'i. Wallahi gaban kika taras,ke har kin isa ki saka min jika a gaba? Haka kawai ban da karuwanci kin wani zo kina wani hamma a'a gatari ne, da ke da munafikin da yake zugaki wallahi sai na sha dammara mu doku. Kunji min munafukar yarinya wani hammmmma, a'a gatari ne Sa'a zo ki dauke min wannan me shigen fatalwar a gaba, nazo ganawa da jikana kin wani fito sai kace an daurawa cokali zani, wani hamma."
"Gaskiya Nana baki kyautawa." "Dalla can ka rufe min baki, ka wani zo da dogon wuya kamar autar amale, wallahi ahir dinka Ariyan na gaya maka ka fita idanuna domin nasan munafurcin da yake cin ka, algungumi da kai kamar tukunyar mayu."
Zuba tagumi Majid yayi yana kallon Nana tana faɗa akanshi. "Ina jinki Nana." "Raina ma ya b'aci duk na manta abin da nazo gaya maka, haba don Allah ayi duk gidan sa'a ba mutane na gari sai kai, duk mutanen banza aka haɗa, alawadan naka ya lalace."
"Hmm! Muje na rakaki." "A'a zan tafi da kafata." "Tow muje na saya miki nama mana Nanata." Washe baki tayi tana faɗin, "ke dai Sa'a kin iya farar haihuwa, kin ga d'a nagari, rabona da naci Nama tun bayan mutuwar Mamman." (🤣😹😂🥲😭 Nana bata tsoron ilahi) "Tun mutuwar Abba rabonki da nama kika ce fa?" Inji Amaan da ya shigo gidan, "Eh karya nayi Alhajin Allah?" Share ta yayi ya wuce dakin shi ya dauko key, "Nana kina jin tsoron Allah a cikin lamarinki, ban da tada husuma wai rabonta da cin nama tun mutuwar Abba." Ai kuwa Nana tayi caraf ta fasa ihu, tare da zama a wurin dirshan tana kuka. Tsaki Majid yayi, ya lura sam idan akwai waɗanda suka fi Nana fitina Aryan da Amaan ne, "Wai meye haka ne Aryan, Amaan kai da kake babu." Inji Hajiya,
"Hajiya kyale wannan tsohuwar bata da aiki sai fitina, wallahi duk ta saka Abdul a gaba sai kace danta, tayi kukan jini mana." Saukowar Majid ne yasa ta sake karkace kai tana kuka. "Tashi muje Nanata." Mikewa tayi tana faɗin. "Kaji abinda suke gaya min.,"
"Allah ya shirya su." Ya faɗa suka fita, yawo yayi ta yi da ita tana bashi labarin gulmar shi da aka yi a dakin Hajiya Rabi, da kuma wani abin da bata fahimta ba, shine ta ce mishi. "Mun gama da daya shima Ubanta mun hana shi magana."
"Inji waye Nanata?"
"Hmmm! Inji Balaraba yar gidan Rabi. Kasan bin malamai take ko boka ya ganta ya barta anan ta hadu da wanda yasa mijinta ya sake ta shima ya aure ta,a tow mutum idan ranshi mugun nufi ne ai ya gani akwaryar shi. Kai dai a bar kaza cikin gashinta, domin da tarhona tana magana da ta gaya maka, tsinanniyar yarinyar nan ashe ita ta kai Tani wurin bokan da ya shiga tsakanin Sa'adatu da Mamman. Bayan dukar Sa'adatun da suke yi lokacin da mahaifinka ya aure ta, nasan nayi laifi amma wallahi na tuba." Ta fada tana kuka bayan ta cika nama a bakinta, jikinshi tsuma yake yi ta ce mishi. "Sannan naji suna cewa ai tunda kwan ya fashe Amaan ya samu lafiya babu abin da zai iya cutar da shi. Kwan me suke nufi?"
"Nana ina zan sani?"
"Na gode sosai Nana!" Daga nan ya wuce da ita, gida suna isa ya kira Sheikh Aliyu Wodabbe a waya. Bayan sun gaisa ya gaya mishi maganar da yaji a bakin Nana. Murmushi Dattijon yayi sannan ya ce mishi. "Kada ka damu kamar yadda muka fara, a hankali kome zai fito maka."
"Baffayo Hajiya gani take kamar da gayya nake."
Dariya Dattijon yayi sannan ya ce mishi. "Lokaci na zuwa ai, kada ka damu zan muku aike insha Allah kai da yan uwanka."
"Na gode sosai Allah ya kara lafiya da nisan kwana."
"Amin Ya Allah, Ubangiji ya kawo maka sauki da mafita."
Daga nan suka yi sallama, dama abin da yasa shi shiru kenan, amma akwai abin da yake son fahimta, waye suka hana shi magana? Akwai wani a cikin gidansu da aka hana shi magana ne?
Tunanin shi ya gama yawo bai hango waye ba, amma tabbas tunda yaji yasan akwai magana.

Haka ya tattara ya ajiye kome a gefe, sannan ya shiga harkar gabanshi. Amaan ya same shi da maganar zuwan dalibai uku da zasu yi aiki a kamfanin, bai tsaya ya saurare shi ba, sai dai wani abokin Amaan din da aka dora akan aikin me suna Dan larai. Dan larai dai dan daudu ne, tun ranar juma'a Amaan yake bin shi akan ya saka hannu ya ce shi dai ba zai ɗauke shi aiki ba, har ranar Monday da suka fito zasu aiki yake tuna mishi. "Dan larai dai zai zo don Allah ka ɗauke shi aiki."
"Idan na dauke shi, Afiyyah kai zaka dauke ta."
"Kai ni bana son fitina don Allah ka ɗauke su, yanzu baba Haladu ya ji cewa ina da hannu akan daukarta aiki sai naji magana."
"Shi kenan, zan duba takardunsu sannan idan basu min aiki a cikin wata goma ba, zan Kore su."
"Eh na yarda." Haka kuwa suka isa kamfanin suka shiga meeting, sannan aka tattauna akan ɗaukar ma'aikata akwai daliban tattalin arziki da zasu zo, wannan abin ya musu dadi domin tun koran wasu ma'aikatan ba a kuma dibar ma'aikata ba, sai wannan karon.

Tun ranar da nayiwa Abdullahi tass, ban kuma ganin shi ba, amma tabbas nasan zai dawo, sannan a gefe guda yadda ake kawo min maganar kamfanin BA'ARE GOLDEN EMPIRES, yasa jikina yayi sanyi domin Allah ya gani bana son tashin hankali, gashi ance bakiɗaya Yaran tsohuwar Chairwoman na kamfanin anan suke aiki. Wannan abin ya dame ni gashi saura kwanaki ne mu tafi. Ina ta tunanin idan zan tafi dole zan tafi da Amirah don ba zan iya zirga-zirga tsakanin Niamey da Marad'i ba.
Wannan abin ya sani jin wani irin damuwa, domin bana son nisa da gida kuma tow ya zanyi.
Chapter 80 · 0% Book details