← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 138

Sashe 116

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta riko hannuna, zamu fita ta juya tana faɗin. "Daga yanzu ba zan kara barin wani dan kutumar uba ya tab'a Zahra ba, sai na rotse mishi kai da kwalba." Ta fada tana jan tsaki, kamar munafuka haka muka bar dakin. "Me yasa kika mata haka?"
"Dalla can, ke kenan kina mutuwa kan kowa babu me mutuwa akanki." Haka muka bar cikin gidan. Muka tafi wajen gida Inda Majid yake zaune da SK Lamido da yazo yau da safe. Hira suke sosai kamar sun shekara dari a tare saboda kawai Majid ya gano babu alaƙar kome a tsakanin mu shi baban Amirah ne kuma mutumin Zuzu.
Abun da ya sa Zuzu ta yiwa Zaytoonah haka, ba kome bane daren jiya suna waya da SK Lamido, sai ta ji ana kuka falo, lokacin Zahrah tayi barci. Shine ta fito taga ita da Majid ne ta zube a gaban shi tana kuka, da rokon ya aure ta wallahi tana son shi ta fi Zahra tasan yadda zata kula da shi wannan abin yabawa Zuzu haushi, ta buga tsaki kawai ta wuce abinta. Wannan abin ya tsayawa Zuzu a rai don gani take kamar cin amana ce aka yiwa Zahrah.
Shine fa da safe ta tashi da haushin Zaytoonah koda ta shigo da kuka kasa mata magana tayi, tare da cewa" wallahi kika sake Zahra ta ji wannan labarin sai kin yi danasanin haka." Daga nan bata kuma bi ta kanta ba, don ta lura yarinyar yar iska ce, ga cin kai kiri -kiri.
Haka yasa bakiɗaya ta ɗauki wannan matakin, ai tasan Zahra zata iya barin kome akan yan uwanta, a yanzu Majid din shukar yardar shi yake son yi shegiya zata musu wasarere.
Haka muka bar gidan sai dare muka dawo ana sallar Magariba, muna shigowa Mama muka samu a falo, ta bini da idanuwa. "Ina Majid?" Tab'e baki nayi zan yi magana Zuzu ta ce mata. "Suna tare da Uncle din Aamirah!" Don a kan idanuna cewa take Baban Aamirah Uncle.
"Tow kuyi sallah, tuwo miyar kuka nayi." "Sannu da kokari!" Na ce mata, muka wuce dakinmu, kwanciya Zuzu tayi tana faɗin. "Washi amma Hamma Majid, dan kurewa soyayya maleji ne, don Allah ki ga yadda ya tare ki da zaki zame?" "Ko ba soyayya ba."na fada ina shiga ban daki. "Wallahi yana sonki." "Mtsss" na ja tsaki ina yin abinda ya kai ni, ina fitowa ta ce. "Omo gayen nan ya saka mace a daki, yayi ta lafta mata bulala sai tayi bul-bul da ita." Tana lashe baki.
"Zuzu yaushe kika zama yar iska ban sani ba?" Fari ta min da idanuwa Allah yaso Baraka da Amirah suna falo suna tasu sallah akwai ban daki a falo. "Ke akwai Zaytoonah fa."
"Ina ruwana, ni dake nake, nifa da akwai makarantar koyan rashin kunya da cire kunya Allah sai na saka ki, kiyi karatun d'aga kafa."
"Allahu Akbar!" Na tada kabbar ta fara sallah, dariya ta kwashe da shi. Sannan ta wuce banɗakin tayi Alola tazo gefena ta tsaya itama ta fara sallah.
A hankali muka idar, ina addu'a itama ta fara addu'a, har da hawaye nasan damuwarta kusan a tare muka shafa. "SK Lamido ya koma Nafada fa." "Allah sarki,ba dai abin yazo ba."
"Tow gamu nan, Baffana ya ce ya hada shi da ni ya tambaye ni na turo shi. Zahra yana da mata fa!"
"Kuma sai Allah ya nufa kece zai samu albarka a cikinki, Allah ya tabbatar."
"Ba zan iya zama da kishiyoyi ba, na gaya mishi gaskiya!"
"Zaki iya mana, kin ga Mamanshi tana sonki. Yan uwanshi tun kafin su ganki su san Aamirah yar shi ce suke sonta suke hidima da ita, ina ga lokaci yayi da zaki samu kwanciyar hankali dan familyn mutanen kirki ne."
"Ina matuƙar tsoro ne." Ta fada tana kallona. "Zuzun da na sani bata da tsoro!" "Karya ne naci uban duka a America."
"A nan babu me dukarki sai dai." Na kwashe da dariya, haka muka fito muka bar Zaytoonah adakin, Majid na samu a falon, suna maganar komawar shi cikin yan kwanakin, har na saka abinci na koma dakin na samu sai kuka take. "Zaytoona tashi muje!" Na janyota, kawai yarinyar nan ta wanka min mari, sai da naji shi har tsakiyar raina. Dama ashe da na tashi na shigo Mama ta biyo ni, ban tab'a ganin fushin irin nata ba, yadda tayi ta rufeta da duka. Kamar zata kashe ta yasa na fasa ihu. "Wayyo Allah don Allah ku zo!"
Da gudu Majid ya shigo, dakyar ya rabata da Zaytoonah wacce tsoro ya kamata kamar zata mutu, bata tab'a dukarta ba tunda ta haife ta kamar kwai haka ta rene ta. Zama nayi ina kuka a wurin Mama sai huci take. "Wallahi kallon banza kika mata, sai na tsiyayar miki da ruwan idanuwa,.balle mari hannunki kuwa ban balla shi ba sai kunya."
Kuka take har da birgima tana wayyo hannunta, gara ta mutu ta huta. "Tsuk sai me idan kin mutu? Dama kin dami kowa gara ki mutu me irin halin Addah!" Inji Zuzu tana jan hannuna zuwa waje, don Majid yaja hannun Mama sun fita, ranar naga tashin hankali.
A daren a dakin Mama na kwana, don cikin dare sai da aka saka min ruwa, da asuba ina farkawa Mama na samu tana rike da hannuna me karin ruwan, "sannu kin ji!" Murmushi nayi mata. "Mama ya Zaytoonah din?"
"Basu jima da barin garin nan ba" tashi nayi zaune "ki kula da ciwonki."
"Mama me yasa ta tafi babu sallama!"
"Hmm eh gara ta tafi."
Sai da ruwan ya kare na shiga ban daki nayi Alola nazo nayi sallah, sannan na kwanta. Ina sauke ajiyar zuciya.

A hanya dama Marwa zai kaita daga can su wuce Nijar, yana gaba tana baya driver da xai kai su yana gefe. "Hamma Abdul Majid ka gaya min ni ko ita?"
Banza yayi da ita, tayi ta magana amma bai ce mata cikanki ba, kuka tayi ta musu babu wanda ya kulata har suka bar garin daoula, bata daina kuka ba kuma bata ji a ranta ta daina kukan ba, "Ka gaya min da ni da Zahra wacece kake so?" Juyawa yayi yana faɗin. "Yanzu naji magana ai na gaya miki tun farko ina sonta, ke na gaya miki bana sonki."
"Kace baka sona? Ni ka gayawa baka sona? Tow shi kenan dukkanmu mu rasa kowa ya huta." Kawai ta saka dan kwalinta ta shake wuyar driven, tukin ya kwace hannunshi, ya faɗa daya titin, kafin Majid yayi wani yunkuri tuni trela tayi kwallo........😹😹🤣 Jinin Addah yana yawo a jikin Zaytoonah...
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce
[5/29, 07:47] Hlm: BHB263
Wani irin juyi motar tayi a tsakiyar titin ga babu haske a garin, salati Driver da Majid suke, ita kan tunda ta bugu bata kara motsi ba, can gefen hanya motar ta hantsila.
Mai motar da ya buge su ne ya tsaya shi da Yaranshi, suka fita aka firfito da su Majid aka kai su gefen hanya, kafin aka kira motar asibitin, abin mamaki ja'ira bayan buguwa ko kwarzane bata ji ba, amma Majid da drivan sun jikata, ba ma kamar Majid, domin kwalba sai da ta yaga mishi baya, haka yasa aka shiga dashi aiki da gaggawa. Kafin wani lokaci labarin ya isa kunnen Mama Aminatu da Zahrah.

- Yadda muka gansu cikin wani hali ya girgiza ni, haka yasa bakiɗaya na shiga wani irin yanayi domin ji nake kamar ba ni ba, bana son naga wani nawa cikin wani hali,. A lokacin da muka shiga dakin Zaytoonah tana barci amma bakinta bai daina fadar magana ba. "Sai ka zab'a ni ko ita, ko kuma kowa ya rasa ka." Abin da tayi ta faɗa kenan, takaici ya kama Mama zata nufi kan Zaytoonah na riketa.
"Kyale ta, tana cikin wani hali bata san waye a kanta ba, don Allah barta."
"Hmmm!" Ta faɗa da damuwa a ranta, "Me zancewa Dadah idan ta fahimci Zaytoonah ce tayi sanadin hatsarin tunda ga abinda take fada " Nima rasa abin faɗa nayi haka muka ci gaba da zama har ta farka. Tana ganina ta fashe da kuka. "Ina Hamma Abdul Majid!" "Yana dakin shi."
"Don Allah idan bai mutu ba, ki bar min shi mana!" A fusace Mama tayi kanta. Na sha gabanta. "Me kike nufi?" "Na taso da soyayyar shi amma shi tun da ya ganki ya juyawa soyayyata baya."
"Dama saboda shi kika mare ni?" Cikin kuka ta ce min. "Eh don Allah ki bar min shi don Allah." "Waye ya gaya miki muna soyayya ne da shi?"
"Ko baki son Majid na rantse da Allah sai kin aure shi, ke babu wanda ya isa ya raba ki da Majid, ita kuma ko zata mutu babu ita babu Majid har duniya ta nad'e."
"Mama ni Yazid nake so!"
"Ba Yazid ba ko waye wallahi ba zaki aure shi ba, idan har na isa dake ba zaki aure kowa ba sai Majid!"
Daga haka ta koma dakin Majid din ya farka, shima kuma da sauki. Bayan fitar ta Zaytoonah ta sauko daga gado har da riƙe kafata tana kuka. "Don Allah ki saka baki ta bar ni na auri Majid!"
"Tashi idan har Majid ne kamar kin same shi." Na fada mata,domin har ga Allah bana son shi, asalima bana jin shi a raina. Haka yasa na ga babu amfanin tsayawa batawa juna lokaci.
Chapter 116 · 0% Book details