← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 138

Sashe 114

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Haka matan shi, bai boye musu ba sannan ya sake daya ya bata dukiya me yawan gaske ya ce zai auri Zulaihah. Sai dai har lokacin Zuzu taki bashi fuska don ma ta kwantar da hankalinta ya ce mata ta shirya su tafi Marwa. Tace a'a ta fasa zuwa domin da kunya ta samu Zahrah ta ce ta bata yarta bayan wahalar da ta sha akan yarinyar wanda tayi ma Allah ya yafe mata.
Wannan abin da ya faru sai da ya kira Majid ya bashi address din Zahra a can douala, amma sai da ya gaya masa abin da zasu yi nan ya gaya mishi shima zai zo Nigeria ɗin, sai su tafi tare, kiran Zuzu yayi ya gaya mata, ita kuma ta gayawa Babangida ya ce musu ai zata zo yola zata sauka ba zata shigo Taraba ba. Hankalin Addah ya tashi, don taji har da Majid a bakin Ummi take jin matsayin su Majid. Don haka ta shiga dakin su ta cewa Zuzu.
"Da Lamido da Majid din nan waye ya fi wani?"
Ita Zuzu bata kawo kome a ranta ta ce. "Shi fa kamfanin gwala-gwalai ne da shi, zaki hada me shigo da gwala-gwalai? Lamido aikin shi shigo da gwala-gwalai ne shi kuma Majid Mamman Ba'are kera gwala-gwalai suke."
"Kenan shi Majid din yafi Lamido arziki?"
"Hmm! Nesa ba kusa ba."
"Tab" ta faɗa tare da juyawa ta bar dakin,. Can ta kuma shigowa tana faɗin. "Kina nufin zaki auri Lamido ne ba tare da kin fi Zahra ba? Ki san yadda zaki yi"
"Ai Zahra ba Majid take so ba, Sarki take so wani dan kasan Algeria."
"Yazid kike nufi?"
"Eh shi naji wai!"
"Sarki da Sarkin da Majid wanene yafi wani?"
"Ban sani ba!" Zuzu ta faɗa mata domin ta fara bata haushi. "Ki gaya min!" Ta fada da karfi. Har idonta daya da babu yana tsaftsafo da jini. "Dukkansu masu kudi ne, shi kenan!"
"Ko zan yi yawo tsirarar Zahrah ba zata tab'a.jin daɗin rayuwa ba." Ta fada tana fita daga cikin dakin, "ki kiyayye dai" inji Zuzu.
.... Ranar Laraba na iso Yola, Ni da Baraka da Amirah, muka iso cikin farin ciki. Abin mamaki sai ga Majid kamar an turo shi. Kame kaina nayi ina dauke kai, motar.da aka zo daukata har da shi, a ranar muka wuce Taraba duk da ban so zuwa ba. Domin na so na bawa Yaya Babangida yar ta na juya, dole suka min muka tafi. Lokacin da muka isa yan uwa da mutanen gidan sukay ta zuwa wurina. Sanyin halina da nutsuwata yana mugun janyo min mutane, haka yasa har yaran gidan suka baibaye ni.
Raba musu kayan tsaraba nayi, sannan na wuce dakin Amaryar Yaya Babangida na kwanta domin a nan xan zauna kafin na tafi jibi. Addah ta ji haushi da ban sauka ta kashe ni da magana ba,da dare ina zaune aka kawo min kayan ciye-ciye wai na Amirah. Zuzu kuwa tunda aka ce nazo bata yarda ta fito ba, sai na share kamar ban san tana nan ba, da na dauki kayan ciye-ciyen na bayar suka raba, washi gari da safe Alhamis na tashi da azumi a bakina. Na shiga har dakin kowa na gaishe su, sannan na wuce dakin su Addah. Tana karyawa muka shiga da su Amirah, komawa bayana Yarinyar tayi taga Zuzu wacce ta kasa dauke idanunta a kaina.
"Ina kwana addah?"
"Da ban kwana ba zaki ganni a zaune?" Murmushi nayi nace. "tow sannu!" Ban yi aune ba kawai sai ji nayi ta tofa min yawun bakinta tare da watsa min kunu a fuska, d'aga kaina nayi sama domin har Aamirah ta fashe da kuka. "Addah kenan, sara da sassaka baya hana gamji toho!"
Daga haka na wuce abina, ban kulata ba..
"Karuwa me bin maza woooo ashawo!" Daidai shigowar Majid da Sk Lamido. Dariya nayi lokacin da naji Zuzu ta amsa mata da cewa. "Ai kuwa Zahra ta dace domin ba ta dauko abin magana ba, ke kuwa gaya min meyee ban yi ba? Gata nan dai ribar da na samu,.kin yi? Kin ciyar dani da kudin yi, kuma kin sani nayi ina ga kawai a wuce dake layin masu lalurar hauka yafi kyau."
Cikin wani irin fusata tayo kan Zuzu. "Kada muyi abin kunya, domin ga Baban Aamirah!" Inji Zuzu, "Baban Aamirah yaci cin abu kaxan uban shi, Allah ya isa idan ya auren min ke, ni karuwanci zaki min don shi na haifeki,.Kiyi ki samo min kuɗi."
"Kudin! Kudi kika ce Addah? Addah kashe ni kawai ki kashe ni na huta." Ta fada kamar zata mutu. "
Zata yi magana na ce mata. "Ashe yawon da kika yi a duniya bai saka kin dauki darasi ba? Na zata ba zaki damu da Addah ba.." "Kai-kai -kai!" Kafin ta kawo min duka da wani katako me kusa. Majid ya rike yana faɗin. "Ba zaki daina ba? Ba zaki daina yunkurin cutar da ita ba ko? Kin ga Yazid ya kyale ki ko? Wallahi kika kuma wannan haukar sai na.saka a tura ki gidan mahaukata yadda zaki yi haukar da hujja!"
Yadda ya koma sojan, yasa ta tsorata domin ya bata tsoro ba iya ita ba hatta mu sai da kowa ya razana. "Ka kaita can, barin addah a cikin al'umma bala'i ne."
Ta fada tana haki, daga zuwa yanzu bata san yadda take ji ba, don kusan mutuwa take ji kamar Yanzu -yanzu. A hankali ta juya zata shiga dakin, duhu ne ya lullube ganinta ta zube a wurin, hankalin mu ya tashi muka yi kanta. Tare da nufarta da gudu.
Ai kuwa ban san lokacin da na fasa ihu ba, "Zuzu don Allah ku duba min ita." Yadda na birkice da sauri suka dauke ta a jikina aka fitar da ita, na juya na kalli ....
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400
#Mai_Dambu ce 300₦

[5/29, 07:47] Hlm: BHB262

"Sannu Addah kin ji dadinki, Yarki daya tak zaki kashe saboda duniya idan Zulaihah ta mutu sai ki zuba ruwa a kasa kisha, ban san ke wacce irin uwa ba ce? Son kanki yayi miki yawa, idan har kudi kike nima Addah kiyi ta nima amma ki sani idan Zuzu ta mutu sai na saka an daure min ke, wallahil azim!" Daga haka na juya na bar gidan domin na gaji da halin Addah, wannan mugun halin nata yayi yawa. Na saka Baraka da Amirah a gaba muka bar gidan.
Chapter 114 · 0% Book details