← Book details Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 138

Sashe 93

Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Haka tayi ta bibiyar shi da rayuwarshi, sannan ta saka a gefe guda ana bibiyar shi, da duk wani motsinshi akan idanunta. Yana sane amma ya share kamar bai san meke faruwa ba, sai da suka samu kusan wata biyu ana haka, ranar yasa aka binciko mishi ita, ya zuba mata idanu. "Na miki gargadi amma kin ki ji ko? Na ce kada na ganki a inda nake amma kamar na b'ata lokacina ne, kada na kara ganinki wannan shine kashedina dake, idan ba haka ba zamu samu matsala da ke, idan na kuma jin labarin kin saka wasu kananun karnukar da kika sa suke bina, zan shafe labarinsu bana son fitina. Sannan ni ba zan aureki ba, kai koda wasa ba xan yi mu'amala dake akan harkar banza ba, na baki shawara kada na kara ganinki. Abin da xan yi na gaba shi ne zan ɗauki matakin da zan baki mamaki"

Yadda yayi maganar yasa ya fahimtar da ita shi din ba kamar sauran mutane ba ne, yana da kwarjini da cika idanu, kanta a sunkuye ta ce. "Don Allah ba zaka aure ni ba?" Kura mata idanu yayi kafin ya dora kafa daya kan daya ya ce mata. "Na gaya miki gaskiya ne ko na barki da halinki lokaci ya gaya miki."
Hawaye ne y zubo mata tana jan kuka a hankali. "Ina sonka tsakani da Allah, da farko nazo ne ko zaka tayani, amma sai na fahimci kai baka cikin irin wadannan mazajen, amma ba zan tab'a give up ba. Sai dai kamar yadda kace zan nisance ka. Haka ba yana nufin zan rabu da kai ba ne har abada, ina nan akan bakana har sai ka juyo gare ni." Bai ce mata uffan ba, haka ya mike ya bar inda aka haɗa su." Ya biya kudin abin da ta sha, yana barin wurin ta fashe da kuka, sosai tayi kuka sannan ta saka sunglass ta fito daga gidan cin abincin.
Motar da take kula da zirga-zirganta, ta
buga tare da fadar ya kaita hotel. Can ya kaita ta kira yaran da ta saka suke mata aiki ta saka su daina bibiyar Majid din, amma ta basu wani aikin saka idanu akan wata mace da yake tare da ita. Sannan a daren ranar ta bar kasar abinta bayan ta tula musu kuɗi.

Zaman da nayi a Ba'are Company yasa ni kara sanin abubuwan akan tattalin arzikin kasa da na duniya, haka yasani nutsuwa na rubuta project me kyau ta yadda zan zama zakarar gwajin dafi. Buga kofar falo akayi "Na'am waye?"
"Baƙo daga Niamey." Rufe bakina nayi tare da shiga daki da gudu na dauko hijab har kasa, na fito da gudu na buɗe kofar.
"Hamma Amaan!" Murmushi yayi me haɗe da dariya. "Dubeta a cikin hijab sai ta dace da Mar'atus saliha, bani hanya na wuce."
Ba shi hanya nayi ya shiga, ina dariya.
"Kai Masha Allah, ashe anan kike raye shi yasa kika rena abin da GOLDEN EMPIRES suke baki." Kallon Laptop din gabana yayi yana faɗin. "Ya Salam, apple laptop." Ya faɗa yana daukar laptop din, wuce kitchen nayi na kawo mishi ruwa da kayan motsa baki, sannan na koma na had'a mishi abinci na kawo mishi wayar shi ce tayi kara,.naga ya rubuta. *Captain* dauka yayi ya saka a hand free. "Soja ya dai?" "Ina kake yanzu?"
Dariya yayi ya ce mishi. "Ina marad'i tare da kanwata."
"Kai Amaan baka jin magana, ita yarinyar nan ko mayya ce sai haka, kuma ka zauna a gidan gani nan zuwa kada ka sake ka bar garin nan."
"Tana jin ka kana kiranta mayya, babu adalci fa."
"Tsuk!" Ya ja tsaki tare da kashe wayar, murmushi nayi tare da zama a gabanshi. "Ka sha hanya ci abinci."
"Ba zan ci ba, ina Amirah?"
"Sun tafi islamiyya."
"Masha Allah!" Ya fara cin jollop din cus-cus da nayi, wanda yaji kayan kamshi da na lambu. "Ko zaki yi min alfarmar yin abinci ga wancan international tuzurun?" Don kada yace ina da bakin hali yasa nayi shiru amma nasan halin Chairman ba lallai ya ci kome ba."tow!" Haka na wuce na fara aiki muna hira sama-sama, ina da miya da kome, grill kifi nayi. Sannan na dafa white rice with coconut da vegetables, miya kuma na fitar da shi a frij kafin su zo nasan zai narke.
Sannan na fito na wuce dakina, nayi wanka tare da gyara jikina na fito muka cigaba da hira. "Kina da plan ne idan kika gama karatunki?"
"Eh ina da plan A&B plan A zan koma Nigeria na bar wani abu zan koma, idan ban samu damar haka ba, zan koma plan B zan nime aiki anan marad'i."
"Ga Alfarma ina nima a gare ki, offer na sama miki, daga kamfaninmu. Na zama sakatariyar Chairman."ware idanu nayi, tare da cewa. "A'a Ya... Hamma Amaan."
"Zaki iya mana, alfarma nazo nima kina da baiwar da zaki iya cimma abubuwa dayawa, Majid yana bukatar taimakon wanda yasan harkar tattalin arziki da cinikayya, ke kuma tattalin arzikin da cinikayya kika karanta, idan har muka dauke ki aiki a kamfanin, zaki taimaka sosai."
Gyara zama yayi bayan ya cika bakinshi da cus-cus, ya ce ."nasan zaki yi mamaki, Hajiya tana da sakatariyarta, Mama Salamatu shi kuma a lokacin shi yaki yarda da kowa gani yake kamar za a iya cutar da wani na shi, soja ne shi kuma likita Aryan kuma injiniya ne, dukkan mu idan kika cire Hajiya kowa da abin da yake so,kin ga har yau kamfanin na kwan gaba kwan baya, please ki taimaka ki amshi wannan offer din please " ya faɗa kamar zai yi kuka. Mikewa nayi zuwa kitchen na sauke abinci, na juye tare da zubawa a kula na dawo, ina murna na rabu da fitina ashe fitinar nan na bibiyata. Zama nayi a sanyayye na ce mishi. "Hamma!" "Don soyayyarki da Annabi ki amsa, don Allah, don darajar iyayenki." Hawaye ne ya zubo min. "Abin da yasa board da Sajjid suna kokarin tasawa dole su zasu bada sakatariyar ta gefensu, ni kuma da Hajiya mun shirya niman haka daga gare ki. Kina jin turanci, sannan nasan Faransancinki ma ba laifi, duk inda kika shiga a duniya zaki yi gogayya da takwarorinki don Allah, nasan munakisar da ake shiryawa amma idan na faɗa rayuwarsu Majid ce a hatsari, kuma ke kin san da haka, ƙoƙarinki shine ki fitar da kamfanin kunya. Nasan is too hard for you, amma zaki iya You can do it."
Haɗiye yawu nayi, tare da sunkuyar da kai babu wanda ya tab'a niman wani abu naki, "Hamma, kasan Chairman ya tsane ni." "Wannan matsalarshi ce, aikinki kawai ki tsaya akan abin da zaki yi, ni kuma zan sha kan kome dan banza me taurin kan tsiya, idan haka soja yake da taurin kai Future child dina ba su yi soja ba." Ya faɗa yana dariya. Kafin ya shiga rarrashina, yana bani baki yana kara tabbatar min ni alkhairi ce tunda ya ganni.
- Zuwa karfe shida na yamma suka iso shida bindinsa, murmushi a fuskata na amshi Aryan, lokacin da suka shigo falon sun samu Amaan yana cin dan wake shi da Amirah da take mishi hira. "Ku zauna kun tsaya kamar a bakin daga."
"Kai bana son iskanci tashi zamu yi mu bar garin nan."
"Bayan kunci abinci ba" ya faɗa yana kara zuba dan wakenshi a cikinsa. "Waye zai ci abincin." Inji Chairman, gyaran murya Aryan yayi yana faɗin. " Ta wannan bangaren gaskiya ba zan iya bin ra'ayinka ba, a zubo min." Haka na kawo abinci na shirya musu, Aryan yaci abin shi, har da cewa. "Idan da hali a zuba min dan wake na, a takeaway nayi gida da shi, shinkafar ta cika min cikina."
"Tow!" Haka na dauko wata kyakkyawar kula na zuba mishi, tare da kayan makulashe, ana kiran sallah suka mike. "Zan tafi, ina kara tuna miki girman alƙawarin da kika ɗauka."
Gyada kai nayi bance kome ba, saboda irin kallon da Chairman yake min har cikin jikina nake jin kallon irin kallon tsana da b'acin rai da fushi ne. Duk sun fita ya rage sai shi, fisgo hijab dina yayi yana huci. Jikina ne ya fara kyarma, na sunkuyar da kai kasa. "Laaa Mami Uncle yana miki kallon kud'a." Sake ni yayi yana me nufarta. "Ina Babanki?"
Da sauri na janye ta, ina shiga gabanshi. "Don Allah kada ka saka mata sunan da bata san da shi ba a baki, don Allah kada kasa ta tambaye ni kome don Allah."
Murmushi yayi yana mikewa yana kallona daga sama har kasa, "kada ta tambaye ki Babanta?" Hawaye ne ya zubo min. "Amma na had'aka da Allah ko?" "Tow ki fita daga harkar Amaan, duk kudin da yake samu yana spend din shi ne akanki ko? Me kike bashi yake...." Ban san ya aka yi ba, sai dai na tsinci kaina da hankade shi ina me jin takaici na ce mishi. "Out!" Na daka mishi tsawa. Ware idanu yayi yana kallo na, nace! Kayi sa'a ban yanke ka da mari ba, shine kawai."
Na nuna mishi waje, ya fita sannan na bi bayan shi. "Ki fita hanyar Dangina!" Banza nayi da shi domin bani da lokacin shi.har wurin motar na raka su sai na tuna ina da Dambu nacewa Hamma Amaan.
"Don Allah minti biyar!" Na shiga cikin gidan da sauri na kawo musu bokiti biyu, na mika mishi da yake gaba ban bawa Amaan ko Aryan ba, shi na cusawa.
"Hamma Aryan a kaiwa Nana daya, Hajiya daya."
"Sannu da ƙoƙari, mun gode."
Daga Ni har shi hararar juna muke, har suka bar gidan. "Ni sa'arta ne da zata zuba min kayan a jikina!" Ya faɗa yana hararar Aryan. "Tow Hammayo ya zata yi. Kawo na ajiye maka." Garin mikawa Aryan dambun ya buɗe, kamshin ya daki hancinsa. Wani irin yunwa ne ya taso mishi. Muzurai ya fara yi yana jin uwar hanjin shi tana murdawa.
Mikawa yayi tare da kamewa shi nan, kamammen mutum, amma ina dama can dan almajiri yace. Iya yunwa bata da hankali, iya yunwa taci mutum tara, haka Majid yayi ta muzurai yana haɗiye yawu. "Idan ka kai mu airport, zamu tsaya muci abinci."
"Ni dai na.koshi, dambun Hajiya zan ci." Inji Amaan, "nima ga danwake na ya ishe ni." Shiru yayi bai ce kome ba har suka isa airport, soft drink. Ya sha amma bai ji kome ba, fakar idanun Amaan yayi da suka wuce sallah, ya dumbuli dambu ya cika a bakinshi ya haɗiye dakyar, ya kara dumbular wani zai kai baki aka ce mishi. "Mr Mamman Ba'are, kaci a hankali zan yi kamar ban ganka ba."
Kunya ce ta kama shi ya haɗiye da kyar, kamar ya bude kasa ya boye kan shi, Aryan ya koma can wurin sallah, yana dariyar Majid.
Chapter 93 · 0% Book details