Sashe 31
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wannan abin ya tashi hankalin mutanen gidan, domin saura igiya daya a tsakaninsu, haka sai da aka yi da gaske ya dawo da ita, ya kuma kafa mata doka, tun daga ranar Tani take zuba mulki kuma babu wanda ya isa magana, sannan itama Tani tasan cewa yana biye mata amma mafi yawan hirarsu zai sako sunan Sa'adatu. Hankalinta a tashe ta nufi wurin Malaminta ya rufe mishi baki da zuciyarshi.
***
A Kano tayi bautar ƙasa, kasancewar Abbati yazo, tana gamawa ta wuce kasarsu a can ta haifi Amaan aka turawa Alhaji Mamman Ba'are sakon haihuwarta, dake a can kamfanin labarin ya same shi, Kuma dayake aikin bai shafi jaririn ba cikin farinciki ya tsayar da dan aiken ya bashi sako ya kai musu, amma shi dai bai taka har can ba, har tayi arba'in ta koma Kano. Dan abin da taxo da shi suka cigaba da rayuwa, bai kuma zuwa ba sai da Amaan ya cika wata takwas, ya turo Alhaji Abubakar Abzin, ya kara biya mata masters ta cigaba da karatu, haka tayi ta fama da Yara biyu ga karatu, koda Alhaji Abubakar Abzin bai zo ba, akwai mutumin da yake kawo mata sako.
Lokacin Abdul Majid yana da shekara uku da rabi, Amaan yana da shekara daya da rabi, domin har ta yaye shi. Sai ga Alhaji Mamman Ba'are da Tani dauke da d'anta karami da ta haifa bata jima ba, kuma abin mamaki shi kanshi Alhaji Mamman Ba'are ya kasa cewa kome akan dan na farko shi bai ce dansa ba ne, sannan kuma bai ki yaron ba, a wannan zuwa da yayi, rayuwar Abdul ta fara fuskantar matsala, abin da ya kawo haka, shine tunda suka zo gidan suka saka shi a gaba da duka, na safe daban na rana daban, idan suka mishi wannan dukar, zasu saka shi a daki a rufe shi, a manta da shi ita kanta Sa'adatu bata da ikon ciro shi, idan ta ciro shi kuwa Tani ta sakata a gaba da masifa sai kace ita ta haife ta, idan Alhaji Mamman Ba'are ya dawo kuma ta gaya mishi ya rufe ta da duka, ita uwar a wahale yaron a wahale.
A hankali Abdul Majid ya zama kamar dolo matukar Alhaji da Tani suna gidan zai na wani irin sizing kamar zai suma. Tsoro da firgici na Uban ya kara cika zuciyar Yaron, satin su hudu suka bar gidan, shine ya dawo daidai amma kuma sai ya xama ko sauti yaji mai karfi, zai zabura yana niman inda zai boye kanshi. Gashi zama da mutane bai saka ta saki jiki da kowa ba, haka yasa bata mu'amala da kowa.
Wani zuwan Mahaifinta taron Malamai na Afirka, yazo ya ganshi bai tsaya ba, ya dauke shi zuwa gidan Sheikh Muhammad Taj Kalarawi, ya ajiye mishi Yaron yana faɗin. " Malam Muhammad ka kalli yaron nan kamar akwai sihiri ko?" "Ikon Allah yanzu dan wannan yaron aka yiwa asiri haka?" Murmushi Sheik Aliyu Wodabbe yayi ya dauki Yaron. "Idan anyi ne don a ga bayan shi, in sha Allah ba zasu ga bayan shi ba. Sai ya zame musu gaggarabadau.." ya dauke yaron yana murmushi, "Alaraini kayi hakuri kada ka mai da musu sharrinsu."
"Ni ban musu ba, kuma ba zasu min na kyale ba. Kasan waye ni kuma kasan daga ƙabilar fulanin da na fito, wallahi ba zan bari ba." "Don darajar Ubangiji kayi hakuri amma shi ka tsare shi." Huci yake kafin ya sab'a yaron zai fita Sheikh Muhammad Taj Kalarawi, ya ce mishi. "Kawo shi!" Mikamai yaron yayi, sannan ya tafi ya koma wurin Sa'adatu. Ya tambaye ta meke faruwa da Yaron, amma bata ce kome ba sai kuka. Haka yasa shi fahimtar tana da damuwa amma ba zata fada ba, sati biyu ya yi a garin tare da tsayawa akan Yaron.
Wannan zuwan ya zame musu alkhairi, domin kuwa har makaranta aka saka yaron, bayan tafiyarshi Alhaji Mamman yazo da Tani. Hmmm ganin yaron yana makaranta da nutsuwa. Hankalinta ya tashi a wannan lokacin da ta saka mishi kahon zuka, domin kuwa duka take mishi wani lokaci idan zai tafi makarantar domin har gida ake zuwa daukar shi, amma zata hana a kai shi, duk da Sa'adatu tana son mata magana tsoron abinda zai je ya dawo yasa take rintsa idanunta.
Bata taɓa hanawa ba, sai sau daya tana laulayin cikin Aryan da aka zo za a dauke shi, Tani ta hana. Kasa hakuri tayi ta ce mata. "Gaskiya ba zai yiwu ba, ya tafi makaranta domin ba zai zama ya rasa nutsuwa ba, a gida bai huta ba sannan a can inda zai huta kice ba zashi ba, wannan ba yi bane ." Ta kamo danta ta fi da shi. Tana komawa cikin gidan Tani ta saka sakatar gidan zata rufeta da duka, ita dai bata san me ya faru ba, sai dai kawai an balle kofar gidan ne aka d'aga daga kan Tani da ta suma.
Koda Alhaji Mamman Ba'are ya zo don yaji labarin abinda ya faru, shima tsorata yayi da Yanayin Sa'ade, don haka ya tattara kayan Tani da d'anta. Bai kuma takowa gidan ba, har ta haifi Aryan ita da kanta tayi mishi huɗuba. Haka tayi ta rayuwa can wurin danginta kamar sun manta da ita, haka shima bangaren mijinta ya manta da ita, sai da ta kai dole ta cire Abdul Majid a makaranta. Dake makarantar Sheikh Muhammad Taj Kalarawi ne,. Ya daina ganin yaron domin Allah ya daura mishi son Abdul din, wani ikon Allah sai kamar an dakatar da shi da zuwa duba su. Haka ya watsar da tunaninsu.. yara uku babu abin da zasu ci, don haka kawai ta fita ta fara aikatau, tana wanke-wanke da abinci, a bakin titi, karshe ma karatun da take ne ya tsaya, akwai wani karamci da kanawa suke dashi, kasancewarta bakuwa kuma daliba, ganin bata zuwa aka tashi wasu daga cikin dalibai suka nimo labarinta, haka yasa makarantar B.U.K suka dauki nauyin sauran lokacin da ya rage mata, wannan karamcin da suka. Mata yasa bata iya mantawa da su ba, sannan daliban tsangayar suka hada mata kudi ta kama sana'a a cikin gidan, ba sai ta fita ba.
A bangaren yaranta ta saka su a wata makarantar gwamnati. Haka suka ta rayuwa da dadi ba dad'i. Har suka gama ta cigaba da xama a Kano, a hankali ta rungume Yaranta, ta cigaba da sana'a idan suka cinye jarin, sai ta nemi aikatau a gidan mutane.
Abdul Majid tun yana primary yake da kokari, sai dai daga lokacin da aka mishi tsawa, zai birkice ya koma kamar dolo, haka yasa wani lokaci yake hakura da makarantar ya zauna a gida.
Akwai gidan da take aiki, Yaron gidan ya nimeta da lalata, ita kanta bata sani ba. Sai da ta ganta a Office din yan sanda, an rufeta, tayi tayi ta musu bayani amma ina sharri aka mata, haka ta bar Yaranta a gida ,babu kowa sai Allah, tayi kuka tayi bakinciki har cewa take ita da ganin wannan rayuwar da mutuwa tayi ya fi mata, akan wannan rayuwar domin tana cikin tasku. Tun safe da Yaran suka karya har rana bata dawo ba, har dare babu labarinta, haka Abdul Majid yake goyan Aryan idan ya gaji ya sauke shi. Kwana suka yi babu kowa a gidan sunyi kuka har sun yi shiru. Washi gari da safe suka tashi babu Mamansu. Har rana bata dawo ba, dalilin da yasa Abdul Majid ya fita bakin shagon unguwar kenan ya sato bread,. Babu wanda ya lura da halin da suke ciki.
Haka aka rufe shi da duka yana rungume da bread din, yaki sakewa sai dukan shi ake yi, makocin sune ya ga ana ta dukar shi, shine ya karbe shi. An farfasa mishi jiki. Mutumin da yake lura da shige da ficen su, yaga yau bai ga Mamansu ba. "Abdul Ina Mamanku?" Yana sheshekar kuka ya ce bata dawo ba, har lokacin yana rungume da bread din,. "Me yasa ka daukar musu bread." "Aryan da Amaan yunwa suke ji Hajiya bata dawo ba." Jikin mutanen da suka dake shi ne yayi sanyi. "Nawa ne kudin bread din?"
"Dari ce!" Biyan kudin yayi ya saka yaron a gaba har gida, "ina mamarku take aiki?"
"Ta can ne?"
"Tow ka jira ni ina zuwa." "Tow!" Gidan shi ya koma ya amso musu kunu da dumammen tuwo, ya kawo musu Aryan da Amaan suka ci sai da suka kusan cinyewa sannan suka koshi, Aryan ya koma ya kwanta sannan Abdul Majid yaci kadan ya bar musu, yadda Mamansu take yi ta ci kadan ta bar musu sauran....
~~~~~~~~~~~~~~
```Shahararu goma aduniyan kayan mata wato m zee kamshi kayan mata kenan inakuke matan kwairai manyan Mata fah bamuna mataba Mata masu aji Wanda tasan kanta agidan mijinta kozokuyi gyara masu kyau da inganci Wanda zaisa oga nishadi yasashi farinciki atare dake kayanmu wane yaro sai uban yaro kinsha zumar makalemata dare daya wanka goma wanan set ne na kayan kwairai akwai fati budurwa mumuna da aeki Dan miyau malaka to shu,Umar Zuma zumar kiba gari kiba Zuma me lakani ningi tsumin lahaula hadin miski ba ahira dawando garin me kabara kasa ruwa sama ruwa wanan magani ba ,a magana magani sanyi mekyu maza da Mata ci da kaza ci da cicibin vlp yan shila ci da kifi nama kayan sakiba na gida danawaje munadakaya kala kala fani kamshi munada shu uwar humra namu ba irin nasubane akwai turare 24 hr turare kabasa Dana gida masu Dadi gakyau ga kamshi 08063845136```
#Mai_Dambuje.
[2/17, 5:06 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*