Sashe 85
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
gasu dauke da kayan abinci niki-niki. "ba sai kinyi girki ba." Gabakidaya a takure nake, har addau nake ya bar gidan na samu iska na shaka."kafin ki hukuntani kanwata ki saurari me zance." "Don Allah ka tafi zamu yi magana, gobe." Yadda yaga na takure wuri guda yasa shi cewa. "Ba zan tab'a cutar dake ba, tunda na ganki naji kamar wajibi ne a kaina na taimaka miki, amma idan bakya bukata ba zan miki dole ba. Sannan ga yadda wannan kada ki sake tafiya baki sanar ba, domin muna aiki Asabar da Lahadi department ɗinmu." Ya saka kai ya fita, ina ga yadda yake share hawaye sai naji bakiɗaya ban kyauta ba, ai da na saurare shi naji meke tafe da shi amma na kasa bashi wannan damar. Haka na kwana abincin da muka zo da shi naci, wanda ya kawo mana na ajiye shi, washe gari monday na tashi da azumi, ita kuma na mata dumame, muka fita aiki da ita, awurin masu gadin kamfanin na ajiyeta na shiga. Lokacin da suka shigo kamfanin ya hango Amirah, sauka yayi ya nufi wurin Masu gadin ya ce mata. "Mirah!" Ya mika mata hannu da sauri ta nufe shi. "Ina Mamanki?" "Tana can!"ta nuna mishi cikin kamfanin. "Ok muje yawo?" Girgza mishi kai tayi tana fadin. "Mami zata yi fushi." Riko hannunta yayi suka shiga kamfanin, dama Majid da Aryan tuni sun shige basu san me yake yi ba, sai da ya tafi office ɗin Majid da ita. "Uban Teresa yar wa ka samu?" "Yar yarinyar nan Fadima Abubakar." "Yawwa kai ne ka bata takardun kamfani?" "Eh!" "Haba ko da naji, yau da asuba naga wani analyzing da aka yi akan kudin da ake kashewa a kamfanin. Sannan naga kai tsaye board ta tura fa." "Eh ni na bata kome." Ya faɗa cikin Murmushi. "Ban tsaya dubawa ba, na rufe na shiga wanka, yana rungume da yarinyar yake kallon Laptop din Aryan da yake magana, Majid yana sauraronsu. "Ranar Alhamis na bata fa, yau monday har ta cire abubuwan da ake yi da kudi babu gaira babu dalili, idan har sanin makaman aiki tazo a matsayinta na daliba, ina ga mai xai hana a dauke ta aiki dindindin." Abin da suka fara dubawa, kudin da ake kashewa akan abinci a duk wata, ya haura abincin da ake yi duk watan, don haka idan aka rage kudin aka saka akan ma'aikatan kamfanin zasu fi mora sama da abincin da ba wani cinye shi ake ba, sannan ma'aikatan da suke haya a wasu wuraren kamata yayi a basu damar zama a cikin gidajen estate din, ba wai sai ma'aikatan hucin gadi ba, sannan kamata yayi daga kan masu tsaron kamfanin har zuwa masu aiki a cikin kamfanin, a hada masu damar insurance card, yadda ko ina zasu ba sai sun nime tallafin kome ba, akan lafiyarsu. Sannan kamfanin ya kamata ya duba iyalan waɗanda albashinsu bai.da yawa a kara ma su, sannan a wancan kudin abincin ya kamata a yi wani asusun da zai taimakawa marasa karfin cikinsu. Idan har kamfanin tana samun riba duk shekara tow ya kamata ma'aikatansu, su fahimci aiki sannan asabar da lahadi, a ajiye shi ya zama ranakun hutu ga al'adar kowani ma'aikaci na duniya. Yadda suke karanta rubutun sai da Aryan yace musu. "Yarinyar nan ba iya kamfanin nan ba, bakiɗaya kamfanin BA'ARE GOLDEN EMPIRES a samo mata office da team din da zasu jagoranci wannan baiwar ni " "Nayi rejected din rubutunta, kada a sake a board members su gani, a goge shi." Inji Majid ya faɗa yana mikewa, "sannan ka mai da mata da yarta, ta tafi gida an dakatar da ita don zuwa da yarinyar da tayi, wani sati ta dawo ta kuma rubuto sakon ban hakuri abisa kutse da tayiwa kamfani." "Ni ne na bata duk abinda tayi, ba wani ba don Allah kada ka tab'a min kanwata." "Kanwarka?" Inji Majid. "Eh "inji Amaan. "Tow idan na ce bana buƙatarta a kamfanin fa." "Hamma!" Hannu ya d'aga musu. "Ta tafi idan kuka kara magana sai na Kore ta. Kuma na lalata takardunta." "Wannan rashin imani ne." Inji Amaan, yana zama tare da rike bayanshi da yake mishi ciwo, yadda Majid ya fita a office din haka Aryan ya fita, shima rike hannun Amirah yayi suka fita. A harabar kamfanin suka same ni, ina tsaye wurin masu tsaron. "Mami!" Ta tsunko da gudu, bude mata hannu nayi, Ya Amaan na zuwa na gaishe shi. "Ki koma gida da Mirah, wannan satin ku yi shi tare sai mu duba makaranta zuwa Monday ta fara." Ya faɗa yana nuna min mota, shiga nayi. ......