Sashe 75
Bakin Haure Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Bayan wata biyu, an sallame Amaan har lokacin Jamilah bata farka ba,abin har ya fara kashe jikin kowa, shima Majid ba karamin matsanancin damuwa ya shiga ba. Haka yasa suka fara tunanin ko a fita da ita waje ne. A bangaren Zaytoonah kuwa an nima sama mata Makarantar Jinya a nan Niamey, inda ta fara da taimakon Nabeeha.
Tun faruwar Al'amarin su Amaan ba a kara jin motsin ko Hajiya Tani, amma kuma sai dai lokaci zuwa lokaci ana samu abu marasa dadi da suke faruwa, a tsakanin Kamfaninsu da kuma wasu abubuwan. Hakan yasa Majid ya ɗan fara bibiyar kamfanin da taimakon Aryan wanda ya amshi matsayin Anisah, suka koma bakin aiki gadan-gadan. Ya ajiye aikin asibiti idan ya dawo da dare sai ya leka asibitin. Duk da bai cewa Hajiya ya koma kamfani ba, sai dai haka ya mata dad'i domin addu'a da ta dad'e tana yi ne Allah ya amsa mata. Lokacin da bata zata ba kuma abin daɗin aiki biyu yake dubawa ko bai je kamfani ba, yana asibiti kuma da alamu aikin asibitin yana so ne har cikin ranshi, shi yasa ya ke lekawa idan ya samu lokaci. Amma bakiɗaya aikin bai da lokacin na asibitin.
A binciken da yayi na kamfanin yasa, aka shiga sallamar mutane musamman masu aikin bangaren tattalin arzikin kamfanin, don ya gano har dasu a cikin masu yi musu zagon kasa, sannan suna cikin masu yayyata wasu abubuwan, haka yasa bakiɗaya yaƙi yarda da kowa, aka sallame wasu aka kuma d'ebi wasu, a bangaren Jamilah kuwa sosai likitocin suka tsaya akanta, har Allah ya d'aga kafadarta bayan wata biyu tana sume, ba karamin farinciki Hajiya tayi ba, don su Yafendo sun koma da Maman Zaytoonah, aka barta a nan Nijar, sannan a bangaren Zaytoonah ba karamin haukar son Majid take ba, su kansu yan uwanshi, sun bata goyan baya, sannan haka yasa take shige mishi. Sai dai kamar yadda ya gayawa Hajiya gaskiya duk da bai fito ya ce yana da zabin ranshi ba, amma ya ce mata shi a kanwa ya dauke ta, ba a macen da zai aura ba. Shima din sai da a bakin Aryan da Amaan suka gayawa Hajiya, domin haka ya faru ne ranar babban sallah suna aikin Nama, ta kawo musu gasashen namar da ta gasa, don ana yankar ta tsaya akan Aryan ya diba mata, ta kawo kitchen tayi mishi denderu. Ta kai mishi koda ya amsa ce mata yayi. "Ya Allah ya bawa Zaytoon miji na gari." Hararanshi tayi tana tura baki, ta ce mishi. "Mimi bata da dady sai kai." "Eh dama ai ni ne dadynta." Murmushi tayi ta wuce, "Hamma yarinyar nan tana sonka, me kake nufi da Allah ya bata miji na gari."
Tab'e baki yayi yana faɗin. "Ita dasu Anisah kallo daya nake musu, bana ajiyeta a tsarin matan da aka halitta daga hakarkarina."
"Abdul kana nufin cewa." Lumshe idanunshi yayi ya bude akan wayarshi, da Umaima take kira, kashe kiran yayi ya kirata da kan shi. "Barka da sallah ya kike?" "Abdul Majid Mamman Ba'are!" Yarrr tsigar jikinshi ya mike, ya amsa a sanyayye. "Na'am Umaima minjibir." Ya amsa yana jiran yaji me zata ce. "A gida a can na fitar da miji, ni kuma ban ga wanda ya dace da ni ba sai, please Majid kada ka yi rejected dina." Iska ya ja yana jin shashekar kukanta. "Kiyi hakuri, Allah ya baƙi wanda ya fini, amma babu aure a lissafina."
"Please Majid, kazo gidan mu ka gaya musu zai aure ni amma ba yanzu ba, wallahi zan jiraka." Ta fada tana kuka, "A'a ba zan yaudari kowa ba, ni namiji ne da zan amsa suna a ko ina namiji, ba zan yaudari yar kowa ba balle har akai Allah ya kama ni. Ni ba Basimpe ba ne ɓalle na yaudare ki, kiyi hakuri nasan akwai waɗanda suke sonki baki basu fuska ba ne, kuma zasu fini sonki."
"Majid wallahi kai kaɗai nake so, don Allah kada ka min haka, idan ma Zahra kake jira ta mutu."
"Zahrah!" Ya ambata a hankali, kafin ya sake murmushi yana faɗin. "Ni ban santa ba, abin da na sani na gaya miki gaskiya babu shirin aure a tsarina. Idan zaki yi hakuri kiyi hakuri. Akwai wanda na san shi jiranki yake kuma zai rike ki da Amana da gaskiya amma ni idan na aure ki, zan miki rashin adalci."
"Majid ka gaya min baka sona."
"Idan na boye miki, ai babu armashi shi yasa nake gaya miki gaskiya kawai a wuce wurin."
"Allah ya isa rejected dina da kayi, in sha Allah sai kasha wahalar so kamar yadda nake sha akanka, kuma ba zaka tab'a haduwa da Zahrah ba har abada." Murmushi yayi yana kara rarrashinta, ita kuwa sai zaginshi take yi, amma shi murmushi yake yana bata hakuri, nuna mata muhimmancin hakurin dai da zata yi, ta samu wanda yake sonta ba wanda take so ba, ba karamin rigima tayi mishi ba, shi kuwa bai fasa rarrashinta ba. "Majid me kake boye min? Yarinyar da ka kwanta da ita a asibiti kake tunanin zata dawo gare ka?"
"Umaima! Ina son ki gane cewa ni babu wani shauki a raina. Sannan bana jin akwai bukatar haka. Mace hmm ba a haifi matar Majid ba." Wani uban ihu ta saka tana faɗin. "Karya ne Majid, karya kake wallahi yarinyar nan ita ce a ranka. Idan ita ce Majid ka kwallafa rai akanta, baka mana adalci ba wallahi." Shafa yar kasumbar shi yayi yana faɗin. "Ko daya yarinyar da ban san yanayin fuskarta ya yake ba? Yarinyar da ko cikin dubu na ganta ba zan gane ta ba."
"Jininka ne a jikinta, zaka gane ta wata rana idan tana raye, amma yarinyar nan bata min adalci ba."
Dakyar ya rabu da ita, Amaan ya zuba mata idanu, shi kan Aryan bai yi mamaki ba domin kuwa ya sha jin yana waya tare da cewa. A bincika mishi sansanin gudun hijira, ko za a dace. Amma shiru sanin cewa baya son magana kuma.idan ka tambaye shi bai zama dole ya baka amsa ba, yasa shi jan bakinshi yayi shiru. "Kai mata suna da matsala haka masu yan mata suke fama."
"Kai dai ka ji dadinka munafuki, kana da wacce take binka tana sonka amma dake kayi zubi da munafukai kayi shiru ka bar, Zaytoon tana wahala wacce me karfin ikon ce ta shammaci zuciyarka."
"Ba a haife ta ba." Inji Aryan yana kunshe dariyarshi. "Lokacin sai kuyi niman budurwa daya da Affan ko?" Dan gidan Aryan inji Amaan. Mur yasha kamar bashi ba, domin bai cika son su tasa shi gaba da tsokana ba, don haka ya haɗe rai ya cigaba da aiki, tun daga wannan ranar bai kuma ce musu kala ba, sai da Hajiya ta tuntube su akan lamarin Zaytoonah da Majid din ne suke gaya mata yadda suka yi da shi, karshe bata sare ba har daki ta same shi yana aiki a can kuryan dakinshi inda aka saka table da kome da kome, ta ja stool ta zauna tana kallon shi. Tunda yaga yadda take mishi kallon tuhuma yasan Hajiya yau no mercy. "Umaimah Ashe ta kira ka akan ka aure ta kaki?" "Hajiya idan na ajiye mace zata bukaci abubuwa dayawa, babu wacce zata fahimci yadda nake ji idan ba wacce take da sanin yadda rayu take ba."
"Majid yaushe ka fara magana." Shiru yayi bai ce mata kome ba, "Majid ban yarda da kai ba, ka ajiye maganar baka da lafiya ni nasan lafiyarka lau, aure nake son naka yi "
Shiru yayi bai ce mata cikanki ba, balle har ta yi tsammanin zai bata amsa. Ta cigaba da fada kamar zata mare shi. "Na rantse da Allah, ka fitar da mace ko ni nayi nawa ikon akanka.......
300₦
0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali
Katin MTN 400 07035133148
#Mai_Dambu ce
[4/20, 9:07 PM] Cutie cutie pie: *BAƘIN HAURE....🐾🐾*