← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 146

Sashe 96

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Almost 2 minutes Big Boss yana cikin ruwan nan shida Abla , idan mutum ba lura yayi ba sai ya d’auka baya cikin ruwan sabida yadda yayi mugun nutsewa, cikin ‘yan seconds d’in da basu wuce 30 ba inda suke ya soma yin ja alamar d’aya daga cikin su ne ya ji ciwo. Ko mintuna d’aya cikakkiya basu ‘kara ba ya janyo ‘kafarta ya fito da ita daga cikin ruwan, gashi ya had’e face d’insa da tayi mugun yin ja na ‘bacin rai . Guntun tsaki yaja ganin yadda kayan jikinta suka manne mata , har yanxu face d’insa ba fara’a ya kauda kansa tare da mi’kewa batare da ya kalli side d’in da take ba ya d’auki Coat d’insa white colour xai ‘bar wajan , bayajin zai iya temaka mata amma idan ta mutu shine da lefi a Wajan Allah , wani ‘karamin tsakin ya ‘kara saki ya nufo inda take a kwance bata ko motsi, kamar zai kai
Hannu kan face d’inta ya ‘kara jan wani tsakin , gefen face d’inta ya d’an duka tare da furta �
Hey !� Shiru Abla bata motsa ba , a karo na biyu ya d’an mari d’ayan side d’inta yana furta “Hey� still ba’a amsa masa , ganin yadda ruwa ya fara fito mata daga gefen bakinta kad’an yasa ya ‘kara sakin wani gajeran taki , Hannunsa d’aya ya kai Daidai saitin cikin ta yana yatsine fuska, yana dan na mata cikin, sai ga ruwa nan ya fara fitowa daga bakinta sosai , akaro na biyu ya ‘kara danna cikin kamar Wanda akai wa dole ,wani ruwan ne ya ‘kara fitowa daga bakinta,lokaci d’aya ta soma tari, idanuwanta da ta fara bud’ewa sosai take ganin bishi bishi a cikinsu, a karo na uku ya ‘kara danna mata cikin , lokaci d’aya gabaki d’aya ta fito da ruwan bakinta , bai tsaya a ko ina ba sai a kan face d’in Big Boss .
Cikin tsananin ‘bacin rai ya sha’ko wuyanta, lokaci d’aya ta ware kyawawan eyes d’in ta akan kyakkyawar face d’insa , jijiyoyin kansa sosai suka fito rud’u rud’u na ‘bacin rai , ga kwayar idanuwansa da lokaci d’aya ta ri’kid’e ta koma ja, kakarin mutuwa Abla ta fara Sabida irin mugun sha’kar da ya kai wa wuyanta, hannu d’aya ya d’aga zai tsinka mata mari tayi saurin runtse idanuwanta gagam tana jiran jin saukar marin sa , ‘karamin tsaki yayi a ‘kasan ma’koshi tare da mi’kewa tsaye , cikin Sauri Abla ta ware idanuwanta ganin be mare tan ba da Sauri ta mi’ke tsaye zatayi masa magana wani saban jiri ya ‘kara d’ibarta da ‘karfi ta furta � Wayyo Allah..� tana ‘ko’karin fad’awa swimming d’in, cikin zafin nama ya ri’ke rigar hannunta batare da ya ta’ba taba, lokaci d’aya Abla kamar me iska ta fad’o jikinsa a sume ,gabaki d’aya jikinta ya saki sabida tsananin tsoran da ya kamata. A hankali Big boss ya furta � Huh�, be kuma bi takan taba ya nad’e ta cikin coat dinsa kamar wani bargo, yadda ya d’auketa kamar Wanda ya d’auki Baby , dan hatta face d’inta ba’a gani
Haka ya d’auke ta ya Fito daga cikin Garden d’in, cikin Sauri gabaki d’aya sojoji suka sunkuyar da kansu musamman yadda ‘ka’k’karfar muscles din Big Boss Suka ‘kara fitowa Sabida ji’kewar da rigarsa tayi , ko kallan side d’in motar su president beyi ba ya wuce cikin part d’insu. Gabaki d’aya sojojin president suna ganin fitowar Big boss suka sauke bindugunsu tare matsawa gefe suma sara masa.
Hannu Alice ta d’ora aka kamar zatayi hauka � No!!!! No!!! Dady ! Me yasa zai d’aukota ?Ni ya kamata ya d’akko! No Dady , Do something now ! Just bana san komai a d’aura mana Auran mu yanxu !�, cikin cool voice her excellency ta furta � No sweety calm down ! He’s your husband ki bari musamu mu fita daga baya sai ayi maganar auranku � Girgiza mata kai Alice tayi a hauka ce ta furta � No mom ! Baki ga wata banza ya d’auko ba ni ba ! Dad say something ko kuma ni naje na saukar da ita �, cikin tsawa president ya furta � shout up stupid ! Baki ji abinda mom dinki tace ba ?� Cikin mamakin Alice ta furta � Dad ? Ni kake wa shouting ? Good !� Itama cikin tsawa ta kalli babanta babu d’igon girmamawa akan face d’inta ta furta � Na fuskanci yanxu baka soma , it’s okay mom ce kawai take sona then I will killed everyone sannan na rayu da Wanda naka so�, tana kai ‘karshen maganarta ta fito daga cikin motar gabaki d’aya idanuwanta sun rufe da kishi , Her excellency ce ke faman furta � No! No sweety! � shima rai a ‘bace His excellency yasa sojojin sa su tada mota, Her excellency zatayi masa complain shima rai a ‘bace ya daka mata tsawa, sai alokacin sojojin Big boss suka matsa masa ya wuce , da zasu fita har sara saida sukai. Sai a lokacin tsoro yashiga Alice ganin Dad d’inta ya tafi , ta d’auka zai fito ya lallasheta ne , da d’an ‘karfi ta furta “Dad! � tana ‘ko’karin bin bayansu,wani irin bugu da Victor yayi mata a kafad’a sai data zube ‘kasa bata motsi.
***** Big Boss yana shiga cikin falourn ya tarar da ba kowa , Daidai kan 3 sitter ya saki Abla kamar wata kayan wanki yayi wucewarsa . Yadda ya saketane yasa ta gangaro ‘kasa sai ji kake kummm ta bige ‘keyarta, cikin Sauri ta bud’e idanuwanta Sabida ta ji zafin buguwar da tayi a ‘kasa , mamakin ganinta A falour tayi , cikin Sauri ta kalli rigar jikinta kamar me san tuna wani abu, a hankali ta kai hancinta kan rigar tana sunsunar ‘kamshin jiki, lokaci d’aya ta lumshe idanuwanta sabida yadda taji ‘kamshin turaransa ya Dakar mata hanci , har wani ajiyar zuciya take saukewa , a hankali ta tashi a daddafe tana ‘kara rungume coat d’in jikinta , ganin babu kowa a falo ga sanyi da take ji yasa kai tsaye bata zauna ba ta wuce d’akın ta .

********* Direct d’akin little ya nufa , yana shiga ya tarar dasu gabaki d’ayansu sun zagayesa ga babban duvet da aka lullu’be masa jiki dashi , hatta yanayin d’akın prince ya mayar masa dashi warmer , yana ganin Big boss ya tashi tare da duvet d’insa be yi wata wata ba ya fad’a jikin Big boss , shima da both hand d’insa yayi hugging little yana lumshe eyes d’insa , kamar me shirin yin kuka little ya furta � yaya ina Lil ? Babu abunda ya sameta ko ?�, amaimakon Big boss ya amsa masa tanbayarsa sai ma kallansa da yayi cikin cool voice ya furta � are you okay ?� Da Sauri little ya jinjina masa kansa , maida kallansa Big boss yayi kan prince ,shima cikin Sauri ya juyowa da Big boss system d’in gabansa � yaya watches this please !� Kallan system d’in Big boss yayi , hatta bobo da uncle duk gabaki d’aya system d’in Suka zubawa ido , gabaki d’aya abunda ya faru tun zuwan su little pool da lokacin da ya barta ita da Alice da abunda ya faru tsakaninsu har ta jefata cikin ruwan sai da suka gani, rai a ‘bace bobo ya furta � She’s too much ! Har kisa ?� Yana kai ‘Karshen zancansa ya bar d’akin , Big boss kuwa ta’be bakinsa yayi kad’an kafin ya ri’ke hannun little suka bar d’akin zuwa part d’insa .

✨✨✨✨

Abla tana komawa d’aki wanka ta shiga shaf shaf,sannan ta canza kayan cikinta zuwa wasu masu kaurin kad’an , coat d’in Big Boss da ta ajje kan gadon ta d’auka , bata san lokacin da murmushi ya su’buce mata ba , har wani rungume rigar take , yadda ta hango face d’insa a had’e lokacin da ta far fad’o ne ya ‘kara fad’o mata a rai , cikin sauri kamar wacce akace yana kallanta ta ‘boye face d’inta cikin rigar, gabaki d’aya murmushi ya ‘ki ‘boyuwa akan face d’inta ,ga abunda ya faru yana ‘kara fad’o mata arai kamar yanxu ne yake faruwa , akaro na ba adadi ta ‘kara shinshinar rigar ta saka ,kafin ta zurata a jikinta duk da yadda tayi mata yawa a jiki sosai , Daidai bakin Mirror ta tsaya tana bin jikinta da kallo ga murmushin ta da shima ya’ki boyuwa har yanxu , hannu d’aya ta saka lokacin da ta kalli mirror d’in kafin ta saki wani blow kiss a tafin hannunta , ita kad’ai kamar zararriya zai juyi take cikin d’akin tana sakin murmushi.
Knocking d’in ’kofar da akai ne Abla tayi saurin cire rigar Big Boss ta jefata a cikin wardrobe kafun ta bud’e ‘kofar, Prince ne tsaye a Wajan hannunsa da wani coffee me zafi da sai faman turiri yake d’auka , yana kallanta ya sakar mata murmushi tare da mi’ka mata coffee d’in � just for Lil , ya kamata kisha da zafinsa kar kiyi mura �, Godiya Abla tayi masa sosai bayan ta Amsa cup d’in, kafun ya juya yabar wajan ita kuma ta koma cikin d’aki dan ita batasan da fad’uwar little cikin ruwa ba .
Sosai ta sha coffee d’in dan sai data shanyesa gabaki d’ayansa tana sakin ajiyar zuciya, ga jikinta da ya fara d’aukar d’imin la’asar, Alwala kawai tayi ta zauna tana jiran kiran sallar la’asar ga tinani barkatai dake ‘ko’karin hana zuciyar ta sakat.

Bobo yana fita direct waje ya fito ganin Alice kwance a ‘kasa ga su Victor da suka saita mata kai da bindiga , cikin bada umar yasa su sakata a cikin mota, babu ‘bata lokaci kuwa Victor ya bud’e boot d’in motar Bobo ya sakata tare da kulle wa , Robert yana driving seat ko sauran sojojin bobo be d’auka ba da gashi sai a Robert sai kuma Alice da aka jefa cikin mota, babu ‘bata lokaci Robert ya tayar da motar cikin mugun speed tare da barin gidan gabaki d’aya .
Chapter 96 · 0% Book details