← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 146

Sashe 16

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Suna shiga d’aki Shuru Abla tayi kamar me tunani, dafata da ilham tayi ne yasata sakin ajiyar zuciya � na fad’a miki kidena sa damuwa aranki,ki duba kiga abunda husna take miki, gaskiya bana jin dad’i� Abla bata tanka mata ba sai ma murmushi da ta sakar mata,Inda suka bo’ye ledarsu ilham ta nufa Amma wayam babu ita babu alamar ta da sauri ta kalli Abla �,Abla banga ledar da na ajje anan ba , ko kin sauya Mata waje ?� Kai Abla ta girgiza mata alamar ah’ah suka shiga bincikar d’akin ga baki d’aya ko zasu ganshi amma wayam babu ,kamar zatayi kuka ta furta � yanxu Abla ya zamuyi kenan Haka zamu zauna kenan?Ni ina tunanin ko su husna ne ma Suka d’auka �, zato zunubi koda ya kasance gaskiya , ki kyautata musu zato, sannan idan kika yarda da ‘kaddara sai kiga Allah ya baki sama da hakan Kinji � cewar abla � naji Abla Amma kinsan su Zinariyya bazasu taba bamu abinci ba ,� idan kikai Imani da Allah sai kiga ya baki mafita , kinji? Komai ki dunga saka Allah a ciki sai kiga komai ya daidaita �, cewar abla , canza akalar maganar tayi ta hanyar furta � ya kamata muyi sallah tun kafin su Zinariyya Susan da zuwanmu �, da hakan ko wannansu yayi alwala suka kabbara sallah bayan ‘boye kararan da tayi a inda baza a yi saurin ganin saba , suna idar da sallah Zinariyya da ‘yar shila suka shigo cikin d’akin, wata shegiyar ashar Zinariyya ta saki, a tsorace ilham ta kalleta Abla kuwa ko a jikin ta, � kun gama yawan karuwancin naku? Kun mayar da kowa yan iska ko? Yau kam sai munyi maganin ku�, cikin daka tsawa yar shila ta kalli ilham � dan ubanki ki tashi kije uwar karuwai na d’akinta tana jiran ki , kafun mu had’a dake muci ubanku �, da Sauri cike da tsoro ilham ta bar dakin, ita kuma Zinariyya ta kulle kofar daga ciki, zuciyar abla ce ta buga amma duk da hakan bata nuna musu komai a fuska ba , rigar data ga sun fara cirewa ne yasa ta mi’kewa a tsorace jikinta har ya fara rawa , ganin yadda suke ‘ko’karin cire kayansune Yasa Abla saurin kawar da idanuwanta , tunanin yadda zata ku’buta daga sharrinsu ta soma , karara d’in data ajje ne ya fad’o mata , a wayance ta d’aukoshi batare da ko wannansu ya ankara ba , daga baki d’ayansu kayan jikinsu suka cire Allah ya temaketa ma da short wando da singlet a jikinsu, yadda suka fara nufotane yasa ta fara ja da baya da baya, suma suna bunta suna dariya � kwanda ki hakura muji dadin juna zai fi miki amma yau babu abunda zai hana ban d’and’anakiba � cewar yar tsila , ita dai Alba babu abunda tace musu sai ma mayar da hannunta da tayi baya tana kwance karara d’in ta cikin Leda, Zinariyya ta saka hannu zata kamota kawai Abla ta fesa musu kararar nan a jiki, tare da kaucewa, dariyar mugunta suka saki har da tafawa , “kin d’auka ‘yar ‘kasar nan da kika samana zai mana abu? Yau ko me zakiyi sai mun ciki�, itadai Abla babu abunda tace musu sai ma addua da take yi cikin zuciyar ta, zasu ‘kara kama tane kamar daga sama yar shila taji kamar abu ya tsireta tayi saurin dakatawa tana ta’bawan, bata Ankara ba wani ‘bari wuyanta shima taji kamar abu ya tsireta, kallan ta Zinariyya tayi tana ‘kokarin tanbayarta menene taji itama kamar abu ya tsireta, da sauri ta saka hannu tana sosa wa , a maimakon ya dena sai kuma ya ‘Karu, da sauri da Sauri kamar had’in baki kuma suka soma Susar jikinsu hankali a tashe , duk inda suka sosa a maimakon wajan yayi sau’ki sai ma ‘karuwa da yayi, a haukace Zinariyya ta manne jikin bango tana susar jikinta, yar shila kuwa burgima ta somayi a kasa tana kururuwar jikinta , ga baki d’ayansu sun fita hayyacinsu babu abunda suke sai susar jikinsu, Abla kam dariya da tausayin sune ya kamata lokaci d’aya musamman katakwan data ga ‘yar shila ta d’auka zatai Susa dashi, Zinariyya kuwa kamar wata ‘kadan garuwa sai bun bango take , ilham ce ta fad’o mata arai shiyasa tayi saurin bud’e kofar da Zinariyya ta kulle cikin da bara gabanta na fad’uwa da sauri ta nufi haryar da zata kai ta d’akin uwar karuwai haryanxu hannunta da ledar karara.
Chapter 16 · 0% Book details