← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 146

Sashe 111

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yau Big Boss baya cikin gidan shiyasa ta sake sosai , lokacin kai abincin simba nayi ta kai masa , tana dawowa suka d’anyi karatu da yaya little, sannan ya d’akko musu game d’insu suka dunga yi , ciki kuwa harda Abla akeyin game d’in .
Tun da rana take ji kamar ta kusa yin al’ada sabida d’an murd’awa da cikinta yake yi kad’an amma bata kawo suwansa yau ba , har ta idar da sallama ta fara jin cikinta yana murd’a mata kad’an kad’an, lokacin da taje wanka ne taka zuwan al’adanta ga ciwan maranta da ya fara tsanta mata , a daddafe ta samu ta saka pad kafin ta shirya ko kwakw kwaran tsayuwa batayi sosai ga ciwan ‘kafarta da shima yake mata zafi sosai , tun tana iya küre wa har ta kwanta a ‘kasa kan tiles tana musu ‘musu ita kad’ai , murd’awar da cikinta yayi mata da ‘karfi ne yasa ta fashe da kuka , cikin ‘kan’kanin lokaci ta nemi ficewa daga cikin hayyacinta, hannunta dafe da cikin ta sai faman jujjuya face d’inta da ta ji’ke da gumi take , tun tana iya nishi har ta ‘kara tsanta kukan ta , ko iya bud’e idanuwanta batayi Sabida azaba, bakajin motsin komai sai kukan Abla da take yi da iya ‘karfinta, tanayi tana birgima a cikin d’akin, knocking d’in ’kofar d’akın akai kusan sau biyu, Abla tana ji amma babu damar ta bud’e bakinta Sabida yadda ta galabaita sosai, Little ne ya turo ‘kofar, yadda yaga Abla ne yayi matu’kar tayar masa da hankali da Sauri ya ‘karasa inda take yana tanbayar ta meke damunta amma ina kwata kwata Abla batasan ma me yake cewa ba, fahimtar hakan ne yasa ya fita daga cikin d’akın a guje , Big boss ne zaune Kawai a falourn sai uncle da prince , yau bobo baya cikin d’akin , a rud’e little ya ‘karaso Inda yake � yaya !� Yadda yaga face d’insa tayi ja ne yasa ya d’an kallesa � Yaya lil bata da lapiya please kazo muje ma dubata dan Allah � banza Big Boss yayi masa kamar ba dashi yake ba , prince yana so yake ya dubata amma yana tsoro Sabida ganin big boss , tunda ya shigo uncle kad’ai yayi wa magana da alama zuciyar sa tana kusa kusa , ganin ya ‘ki kulasane yasa little fashe masa da kuka � please yaya kazo ka dubata zata iya mutu wa � rai a ‘bace Big boss ya furta � And so ?�, No please Big boss rashin lapiya aka ce , ko sau d’aya ne ka dubata � a miskilance ya furta � uncle…� daga nan be kuma cewa komai ba , cikin kuka little ya furta � please yaya just for my sake kazo ka dubata� yanxu ma shiru Big Boss yayi masa , cikin kuka little ya furta � kace kana sona ? Zaka iyayin komai a kaina ? Amma yanxu I beg you for a thing ka ‘kiyimun shi , why yaya , idan momy na da dady sunanan zasu …� be ‘karasa ba Big Boss ya d’auke fuskar Little da mari, karo na farko a rayuwar little da aka Maresa , Daidai lokacin da Bobo ya shigowa cikin falourn , idanuwan Big Boss sunyi mugun jaa na tsananin ‘bacin rai , jijiyoyin wuyansa gabaki d’aya sun fiffito shi kansa little sai da ya tsora ta , yasan Big boss ya hana maganar iyayensu ko kad’an shima yayi ne bawai dan ya damu dasu ba Kawai so yake ya duba masa lil d’insa , cikin Sauri Bobo ya ‘karaso Inda Big Boss yake sabida yadda yaga condition d’insa, lokaci d’aya little ya fashe masa da kuka , shima prince sosai ya shiga Tashin hankali ganin yayan su, Bobo zai ta’basa ya hankad’ata , a hankali ya ‘karaso Inda little yake , cikin tsananin ‘bacin rai ya furta � how dare you?�, cikin rawar murya little ya furta � please yaya kayi hakuri kar ranka ya ‘bace, please kayı hakuri �, a tsawace Big boss ya buga masa tsawa , karo na farko da little yayi maganar iyayensu dan shida Big boss sunfi kowa tsanarsu tun little bashi da wayo, rai a d’an ’bace Big Boss ya lumshe eyes dinsa be kuma kallansu ba ya wuce part d’insa , fashewa da kuka little yayi tare da hugging din bobo � yaya bobo ! Yaya bobo please ka bashi hakuri yana fushi dani dan Allah ka bashi hakuri, Nima bana sansu kawai na fad’ane sabida ya dubamun sister ne , please yaya am sorry � babu Wanda jikinsa beyi sanyi ba , shi kansa bobo saida jikinsa yayi sanyi ga Tuna’nınsa da ya raba gida uku, be san wani irin hali Abla take ciki ba , da dinsa d’aya Dr tana kan hanya dan tun kafun ya ‘karaso prince ya tura masa message, ga Big Boss s yasan yanxu ransa yayi ‘kololuwar tashi duk Wanda yayi gigin masa magana xai iya sa’ba masa , mutum d’ayane yake iya masa magana ko ransa yana a ‘bace shine little gashi yanxu da little din yake fushi abunda da wuya ya faru dan Big boss xai iya hukunta kowa ya bar little Sabida san d yake masa , ga little da yake ‘ko’karin tayan da hankalinsa, ,idan ba’a masa abunda yake so ba ciwansa xai iya tashi, gabaki d’aya kwakwalwarsa neman tarwatsewa take , ga kukan da little yake masa har cikin zuciyar sa yake jinta , prince kuwa tuni yabar falourn dan beso little yayi maganar mutanan da suka d’auka matattuba , kasa magana uncle yayi sai zama da yayi akan kujera yana nanata � Innalillahi wa inna ilaihi raji’un�. A Daidai lokacin da abunda yake faruwa a ‘kasa , Abla tana Çan cikin mawuyacin hali Sabida ciwan mara , tun tana mutsu mutsu har ta dena Sabida yadda cikin ta ya murd’a mata , lokaci d’aya ta dena nunfashi alamar ta suma gabaki d’aya.
( Tofa yau Big Boss na fushi da little 🥺🥹)�..

https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written
By
Mss Lee �

🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅
🦅🦅M.W.A🦅🦅

AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__

✨MSS LEE BUSINESS WORLD �

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer) Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.

NOT EDITED
Chapter 111 · 0% Book details