← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 146

Sashe 66

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

✨✨✨✨

KANO
Momy bata shigo cikin gidan ba sai wajan ‘karge 9 na dare lokacin Baby ta cika tam sabida haushisu da take ji ga haushin Eshaal da ya cikata tun d’azu , ita kad’ai sai kunbure kunbure take shiyasa ta ware volume d’in ‘kida sosai ranta a ‘bace tundaga kan yadda take Danna wayar tata mutum zai fuskanci haka , turo ‘kofar da akai ba sallama ne yasa ta ‘kara Tsuke face din ta sabida tasan ko wacece , itama momy ganin yadda Baby ta had’e mata raine yasa ta ‘karaso cikin d’akin tare da kashe kid’an , a zuciye Baby ta d’ago da idanuwanta ganin momy a kusa da ita yasa ta ja wani dogon tsaki tana d’auke idanuwanta daga kan momyn , itama momyn bata damu da yadda Baby tayi mata tsaki ba sai ma kunnawanta biyu da ta kama � Haba baby na wannan fushin duk da Menene ? Kiyi ha’kuri mana , lokacin da kika kirani bana kusa da wayar sai missed calls d’inki da nagani , kiyi hakuri baby na �, mi’kewa tsaye Baby tayi tana nuna mata ‘kofa cike da rashin kunya ta furta � kizo ki fitarmun daga d’aki bana bu’katar ganin ki , zan kwanta� ri’ko hannunta momy tayi kamar ba Itace babba ta kara sanyaya muryar ta � haba baby na banaso naga ranki na ‘baci haka please baby na , nace kiyi hakuri , bazan sake hakan ba kinji ?� ,d’an kwafa baby tayi tana yatsina fuskarta kafun ta samu waje ta zauna akan fadonta � toh yanxu fad’amun me akai miki acikin gidan nan, naga ranki a’bace haka� sai a lokacin Baby ta kwakwulo kukan muna furci harda hawayenta ta soma labartawa momy karyar da ta had’a har da cewa AMMA da Eshaal haduwa sukai suka dunga dukanta bayan Eshaal ta gama zaginsu gabaki d’ayansu har Dady bata ‘kyaleba� sosai ran momy ya ‘baci sai faman hura hanci take sabida jin karamar Eshaal , a zuciye ta fito daga d’akin Baby, baby na ganin fitarta ta ‘kyal’kyale da dariya tare da bin bayanta da Sauri dan ganin abunda momy zatayi musu , momy tana fitowa ta fara kwallawa Eshaal kira , Daidai lokacin da Eshaal take karatun alqur’ani da sauri ta mayar dashi tare da fitowa waje ko hijab d’in jikinta bata cire ba , tana fitowa falourn ta soma ‘ko’karin dur’kusawa amma momy ta Shakira tare da furta � ina munafukar uwar da kike cewa kina dashi take ? Ke kinzama yar iska komai ya bayyana a jikinki shiyasa kike da bakin magana ?� Kallan baby momy tayi kafun ta furta � jeki kirawo mun d’aya muna furta � cikin Sauri Eshaal ta soma girgiza mata kai � momy babu ruwan AMMA a ciki wallahi duk lefinane� hannu momy ta d’aga ta wanke wa Eshaal fuska da mari � dan uwarki ina magana kina bani amsa ? Ko uwarki Hauwa’u bata İsa ina magana tana mayar mun ba , balantana ke da aka same ki ta gaba da Fatiha� da Sauri Eshaal ta runtse eyes dinta dan aduniya batasan taji ana zagar mata mahaifiyarta da ta mutu , hawaye har ya fara kwantawa akan fuskarta ga tafikan hannun Momy da ya fito rad’au akan face d’inta , lokacin da AMMA tafito ko jira ta tsugunna momy bata bari tayi ba daka kalli fuskar AMMA kuma zakaga alamar bacci ta somayi aka tasota � Muna fuka , annamimiya butulu, uban me zakimun da kike shirin tsugunnawa ‘kasa Sabida muna furci ? Da sai ki d’ago ki kallene cikin ido ai , muna fukar banza muna fukar hofi ke ko kunya ba’kyaji ki zauna ki dunga sharara wa yarinya ‘karya anyama ba asirceta kikayi ba ? Dan gabaki d’aya yanxu na fara xarginki idan bakya bin malamai , da Sauri Amma ta d’ago da idanuwanta ta kalli momy kafun ta sauke idanuwanta tana d’an girgiza kanta kad’an � kiyi hakuri � cewar AMMA , Eshaal kuwa sabida mummunar maganar da suka fad’awa Amma yasa ta fashe da wani saban kukan har cikin zuciyar ta bataso AMMA ta bawa momy hakuri ba , dan momy ba mutum bace azzalumace shekaru kusan nawa tana aiki agidan amma kullum da irin wulakancin da Momy take mata , yadda take kuka ne yasa momy ta hankad’awa AMMA ita tana karkad’e hannayenta a yatsine � shegiya bansan ya akai hannuna ya ta’ba jazasar jikin kiba dan kekam kamar yar shegiya haka kike turrrrrr, ku tattara ku barmun falo keda muna fukarnan yanxu kafun ranku ya ‘baci gabaki d’ayanku.� Hawayenta Eshaal ta goge tare da kama hannun AMMA suka bar wajan dan idan suka ce zasu tsaya sai ta ‘kara ci musu wani mutumci harsunyi nisa momy ta sake daka mata tsawa � muna fukai Menene na ri’ke hannu kuma ? Dallah ki saki juya kowa ya nufi wajan kwanansa , muna fukan banza muna fukan hofi � rabuwar kuwa sukayi kowa ya nufi hanyr makwancinya , Eshaal ji tayi kuka na zuwar mata sosai take a binta akan gadon ta tuntanayi da ‘karfinta har ta soma ajiyar zuciya alamar bacci ya d’auketa . Suna barin wajan momy ta kalli baby � my baby kinyi farinciki ko ? Cikin washe baki sosai baby ta furta � yes nayi farinciki� sai kuma ta kama yanfar d’akinta � momy ki kira dady kice ya taho mun da ice cream sai gasasshiyar kaza da nake so, sannan ya taho mun da kilishi , ina jira� bata jira jin amsar momy ba ta shigo d’akin ta fara danne dannenta a waya ita kad’ai ga headphone da ta saka a kunnanta , tun tana jiran dawowar dady har bacci ya d’auketa da headphone a kunneta.

🍃🍃🍃🍃
🍂🍂🍂🍂🍂🍂

*NEW YOUR CITY*

� No please Big Boss , atleast tunda ya kira , please� cewar bobo , still shiru big boss yayi masa batare da tanka masa ba � ok just for me please , just for Abdulmaleek�, cewar bobo , batare da big boss ya bud’e idanuwansa ba ya furta � and you who are you?� Girgixa kansa bobo yayi ganin missed called d’in his excellency akaro nayi a wannan karan harda just message , yana shiga cikin message din yaga vidoe Alice tsaye wajan fanka ta saka wani igiya zata kashe kanta , rai a’bace shikansa bobo ya furta � Wannan bata da hankali ne ?� Shima sabida yasan his excellency ya kira big boss da wallahi shima babu Inda zaije , wata ‘karamar waya ya d’auka tare da tura musu short message , rai a d’an ’bace yasan idan ya nuna wa big boss wallahi bazasuje ba, shiyasa ya tura message, Big boss kuwa tundaga lokacin da bobo ya tura message yaji alamar an shiga wata ‘kwanar amma ko a fuska be d’ago ba sannan babu wata alama akan fuskarsa tana nan yadda take sai ma ‘kara balance da yayi yana lumshe eye kamar me bacci , 5 minutes motocin suka d’anyi parking , yadda yaga fuskar big boss yasan ransa a ‘bace yake shoulder d’insa ya dafa cikin cool voice kamar bashi ba ya furta � please am sorry, just for your brother kaji ? Ta’be baki big boss yayi kad’an kafun ya furta � 3 minutes only if not saidai ka taho a ‘kafa� d’an murmushi bobo ya saki kafun ya bar motar yana nufa cikin gidan , 2 minutes later ya turowa big boss wani short vidoe kamar bazai dubaba sai kuma ya kalli wayar bayan second 30 , wani message d’in ne ya sake shigowa cikin wayar yana dubawa yaga yadda ta yanka hannunta Jini yana fitowa , ta’be baki ya ‘kwarangwalce ko kuma aljana dan shi gabaki d’aya Alice batayi masa kama da mutum ba da jinsin aljanu tafi masa kama � kawar ta zancan yayi gabaki d’aya yana sakin gajeran tsaki ganin wani message din na bobo , ba tare da ya bud’e message din ba ya ‘karayin balance kan kujera sai da ya d’auki good 5 minutes sannan ya danna wani button lokaci d’aya victor ya bud’e masa mota, a lokacin da zai fito da’kafarsa sai da ya sha izzarsa san ransa kafun ya fito cikin motar rai a ‘bace amma ko a fuska bazaka ga alamar ‘bacin rai atattare dashi ba , mutane biyune suka bi bayansa Victor da Anthony , har yanxu p-cap d’insa na kansa , yanda yake taka ‘kasa kamar bayaso Daidai medium gidan da bobo ya shiga har cikin falour ya taka hatta shi bobo yayi mamakin shigowar big boss d’in Alice kuma tana tsaye kan kujera bayan ta saka rigiyar a wuyanta , big boss na shigowa kai tsaye ya daki kujerar tayi gefe Alice ta fara wutsil wutsil tana neman a gaji , rai a had’e ya furta � you can die now � yana kai Karshen zancansa ya bar falourn.

PAY YOUR 300 into 2681892316 Aisha umar , zenith bank sai a turo da shedar biya ta wannan number 07041879581.

https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt

https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written
By
Mss Lee �

Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

MARUBUCIYAR * Gidan Aunty * and now *IBTISSAM*

💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___
Chapter 66 · 0% Book details