← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 146

Sashe 78

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

falourn tare da daga hannunta sama � Allah kana gani yace basashan Jini basa yanka mutane ,� sai kuma a karo na biyu ta ‘kara bud’e idanuwanta tana bin falourn da kallo, duk da a tsorace take kallansa sosai wajan yayi mata kallo, � kai ta d’akin da zata zauna� cewar bobo yana zama kan kujera , “toh yaya”cewar little , itadai Abla sai binsa a baya take , duk yadda yayi su shiga elevator Abla kin shiga tayi wai zai siyar da ita , dole sai ta kan stairs suka biyu, itadai sai bin ko ina da kallo take a tsorace ta ki yadda tayi masa kallan kurinta, a 1 floor cikin wani d’an corridor little ya bud’e d’aya daga cikin doors d’in wajan da take da nata corridor d’in daban, Babban d’akine a wajan me shegen girma da ‘kayatuwa , cikin d’akin milk colour ne hatta designer din royal bed din dakin milk colour ne , ga wasu set da suke dashi da ya ‘ka wata d’akin kasan tuwar gadon d’akin me kamar shape din circle ne sai ya yiwa dakin kyau, gaban mudubin d’akin kamar ana rayuwa a ciki yadda yake cike taf da kaya a ciki, komai na set din gado kawai a ciki hatta bed side da kwaba duk a kwai a ciki ga wani medium milk carpet a cikin d’akin , daga gefensa ma doguwar sofa ce milk colour sai d’an center d’insa shima, iya haduwa d’akin ya haduwa ko wasu masu kudin albarka dan ba’karamun dukiya aka kashe wa d’akın ba , sosai Abla ta saki baki tana bin d’akin da kallo cike da tsantsan mamaki , haryanxu ba ta yadda ba mutuwa tayi ba Sabida ydda take ganin sabanin abubuwa masu kyau , shima d’akin sai tashin kamshi da sanyin Ac yake ta ko ina , murmushi little ya d’an sakar mata � Nanne d’akin ki� kallan inda yace d’aki Abla tayi cike da mamaki , kafun ta ‘kara kallansa � nan ne d’aki ? Kaji tsoran Allah fa� kansa ya jinjina mata � Nanne d’akinki Dagaske , ki zauna a ciki kafun na kawo miki abinci , zo muje na nuna miki band’akin ki� yana fad’ar hakan ya nufi wata ‘kofar da Sauri ta bi bayansa suna shiga cikin ban d’akin ta kara ja baya � nan kuma wani d’akine ?� No band’akine � cewar little, yadda tsarin toilet din yake sosai zai bawa duk Wanda ya kalli band’akin sha’awa mutum ko yaddar da abu yayi akasa zai iya daukan kayansa Sabida yadda yake da matukar haske babu ko datti a cikin toilet , komai macikin ban d’akin na zamani ne sosai , ga wani dogon glass da yake sha’ke da sabulan wanka , sink ya kunna tare da nuna mata � idan kina san kiyi alwala � sannan ya nuna mata yadda zata kashe shima , sau biyu yana nuna mata , cikin toilet ma sai da ya nuna mata, hatta shaya da yadda zata shiga cikin glass wajan wanka saida ya nuna mata da sabulan wanka da shampoos gabaki d’aya sai da ya nuna mata , sosai tayi mamakin komai tunda take aiki a cikin gidan karuwai bata ta’ba ganin waje ne kyau kamar nan ba , cikin ‘kan’kanin lokaci ta fahimci duk abunda ya nuna mata , hatta mayuka da turare saida ya nuna mata , � ki zauna anan yanxu zan kawo miki abinci � zatayi magana yayi saurin furta � Allah yana gani � yana kai karshen maganarsa ya bar d’akin , sai a lokacin Abla take ‘karabin wajan da kallo , sosai ko ina tayi mata kai , tana kallan gaban mudubi ta kalli fuskarta bata san lokacin da murmushi ya kwace mata ba da har saida dimples dinta ya lo’ba , ko minti 5 little be yi ba ya dawo dauke da tray babba sha’ke da irin kayan abincinsu, sai alokacin yunwar da take ji sosai ya ‘kara tasar mata ganin Abinci , da Sauri ta saka hannu zata soma cin abincin harta manta da little da yake wajan cikin sauri ta d’aki wani samosa da gani tana sawa a baki tayi saurin futo dashi sabida bata saba cin irin abin cin ba , kamar zatayi kuka ganin ta kasa ci, fruit din da ta gani ne ta dauka, tana sawa a baki ta saki wani ajiyar zuciya , sosai ta soma cinsa , fahimtar yunwa take ji sosai ne yasa little barin mata dakin dan taci abincinta sosai. Yana sakkowa falourn direct kujerar da uncle yake zaune akai ya zauna tare da ri’ko hannunsa � please uncle ku Barta ta zauna � gyara zama sosai uncle yayi yana kallansa , � Bobo yayi mun bayanin komai little amma ko na Amince kasan yayanka bazai ta’ba amincewa ba , kasan halinsa sosai , ka bari bobo zai samar mata wani wajan da ban� bobo bai ce masa komai ba, prince shiru yayi shima , a hankali little ya furta � please uncle just for me, mu kwada yi masa magana dan Allah � dungure masa kai uncle yayi � shikenan karkayi mun kuka naga kunnanta sun farayin red alamar kiris kake jira , bari ya zo amma ban maka al’kawarin zamanta ba Indai be amince ba , kansa Little ya jinjina duk da shima shi da cikakken hope d’in yaya big boss xai amince da zamanta , gabaki d’ayansu babu Wanda ya kuwa cewa komai banda bobo da ya nufi part d’insa , basu fi mintuna goma da zamaba Robert ya shigo da wasu manyan ledoji guda shida sai wata ‘karamar jakar trolley tare da ajje musu cike da girmamawa ya furta “the trolley is for madam from Dr Eli and this is for sir � yana kai karshen zan cansa ya juya ya bar falourn , � kayan da bobo ya sa aka wo mata ne � cewar uncle , d’aukan kayan prince da little sukai tunda sun fahimci natane gabaki d’aya har trolley din suka nufi d’akin da take lokacin har ta gama cin abincin ta gaji da jiran dawowar little , Bakinsa d’auke da sallama suka shigo cikin d’akin shida prince , ko wannensu da murmushi kwance kan face d’insa , nuna mata kayan little yayi � ki shirya sai ki Hutu idan , idan lokacin sallah yayi sai kiyi sallah , kinji � wasu hawaye ne suka sakko mata � Nagode sosai � girgiza mata kai little yayi � ki dena gode mana Allah zaki godewa , ki huta kinji baki da lapiya � daga nan basu ‘kara bata chance d’in magana ba ,suka bar d’akın , sosai Abla Tasha kuka tunda take a rayuwa babu Wanda ya ta’ba kautata mata kamar yadda sukai mata , har cikin zuciyarta take jin kaunarsu, kallan kayan tayi sosai ta gane trolley din da suka shigo da ita Sabida irinta baturiyar jiya ta bata amma taki ta’bawa , kamar bazata ta’ba kayan ba sai kuma ta nufi inda trolley din take , tana bud’ewa tayi saurin rufewa sabida abinda taci karo da su, akaro na biyu ta ‘kara bud’e har kulle idanuwanta tayi sabida kunya , cikin akwatin wasu set din pant ne dayawa a ciki sai bra da ta sako mata a ciki , hatta pad sai da ta saka , duk yawanci abunda mace zatayi anfani dashi sai da ta sako mata Sabida tun kafin su shigo Us jiya bobo ya tura mata kud’i kan tayi wa yar 19 years siyayya, shiysa komai ta siyo mata da yawa , sauran ledojin gabaki d’aya dogaran rigunane a ciki , sai kananan kaya, wani irin farin cikine ya kamata kamar wacce aka yiwa kyautar aljanna, har hawayen farin ciki saida Abla tayi , ita kadai sai faman yi musu addua take ga wani irin soyayyarsu da ta shiga cikin zuciyarta . Inda little ya nuna mata a matsarin toilet ta nufa amma gabaki d’aya a tsorace take white bucket d’in da tagani ta d’auka tare da nufar wani waje me kamar fanfo da little ya nuna mata d’azu , tana kunna kuwa sai ga ruwa ya kunnu wani irin dad’ine ya kamata lokaci d’aya inda jerun samulan wankan yake ta nufa shima kamar yadda little ya nuna mata ta dauki d’aya tare da wani sosan wanke me laushi, bata shiga inda little ya nuna mata ba sbida tsoran shiga da take shiyasa a filin wajan ta dunga dirje jikinta dan hatta sabulun wankan da ‘kyar ta iya bud’e shi, yadda take watsa ruwa a jikinta har wani kulle idanuwanta tayi saida ta watsa ruwa Sanranta tukunna ta fito , cike da jin kunya ta d’auko fant da bra dake cikin trolley ta saka , kamar kuma an aunata sabida yadda kayan sukai mata cif cif a jiki, wata maroon d’in doguwar riga ta saka a jikinta da tayi mugun haska fatar jikinta ,ga uwan tulun gashinta da ya dakko mata har gadan maya me shegen tsaho da cukowa , Daidai lokacin da ake kiran sallahr azahar, idanuwanta ne suka sauka kan simfid’ad’d’iya daddumar da take d’akin, ajiyar zuciya kawai ta sauke tare da tada sallar azahar dinta , tana idarwa wani irin bacci ne ya kamata sabida yadda bacci da bata samu tayi ba , ga wani sanyin Ac da ya ‘kara sanya dad’in shiyasa wani irin bacci me dad’I da ta dad’e batayi irin saba ya d’auketa , ba ita ta tashi ba sai lokacin kiran sallar la’asar shima da kyar ta iya bud’e idanuwanta , alwala tayi ta yi sallar la’asar din , tana idarwa shima wani bacci ne ya ‘kara d’aukarta. Allah sarki little tunda ya bar d’akin tunanin yadda xai ro’ki big boss ya bar Abla ta zauna a gidan yake , haka kawai yaji yana kaunar ta zauna a tare da su shiyasa gabaki d’aya ya kasa sakewa , duk yadda prince yake kwantar masa da hankali ya kasa kwantar da hankalinsa duk da shima prince ‘boye fargabarsa yake sabida little , uncle ma Sosai ya fuskanci yanayin face d’insu ya canza amma be ce musu komai, lokacin bobo ya fita daga cikin gidan shiyasa hatta abincin rana Kasa ci yayi sai fruit da ya d’an sha , har aka yi sallar azabar babu Wanda ya kula ,
Chapter 78 · 0% Book details