← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 146

Sashe 68

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

🍃🍃🍃🍃🍃🍃

NEW YORK

Tsaye little yake cikin basket ball da suke bugawa shida prince sai sojojin da suke cikin wajan a tsats tsaye , jikinsa sanye yake cikin coffee colour d’in kayan sport , kusan iri d’aya ne kayan jikinsu shida prince dan shima coffee d’in kayane a jikinsa na sport sai faman sakin dariya yake ganin yadda little ya d’an ‘bata fuskar sa , cikin d’an sauri sauri ya ‘karaso Inda yake a tsaye � wai wannan ‘bata fuskar da kake yi na Menene kuma ?� Shima cikin d’an rad’a rad’a little ya furta � kalli fa abunda suke mana , wannan ai zalincine munfi 1 hour muna ball d’innan amma sabida mugunta sunga yaya bobo da yaya big boss basanan shine suke mata mugunta,� kafad’arsa prince ya d’an ta’ba kafun ya furta � don’t worry muma ya kamata Musamu ‘yan team mu rama abunda suke mana� gyara tsayuwarsa little yayi yana bin face d’insu da kallo kafin ya ta’be baki , � yaya Prince Allah kasan da ace ni d’an biyune da babu abunda zai hana nayi musu mugunta duk sai suna bacci zasuga kunamu, yan banza kawai�, yanxu kam dariya sosai prince yake masa cike da sha’kiyanci, gyad’a masa kai little yayi kad’an kafun ya furta � am coming� , be jira jin amsar saba ya bar wajan , sojojin da suke buga basket ball d’in dasu gabaki d’aya suna tsaye suna jiran ganin reaction d’in little ganin ya bar wajan, ko minti 5 cikakkiya little beyi ba ya dawo bayan sa su bruno ne ko wannansu harshan sa a bud’e , sakin baki Prince yayi yana Kallansa kafin ya d’an hararesa � me zamuyi dasu da ka d’akkosu? Please kamayar da su kasan halinsu mugayene Dan rai nan sojojine� shafa kan Bruno little yayi kafin ya furta � yaya prince kamanta lokacin da nake ‘karami? Lokacin ban iya basket ball sosai ba , yaya bobo da yaya big boss suka koya mun? Kamanta simba da su Bruno duk ankoya musu wad’annan abubuwan ?� ‘Dan hararar Bruno prince yayi kafun ya furta � kasan ba koda Yaushe nake san ganinsu ba kasan halin wa’yan nan karnukan�, sorry dis once Kawai fa� little ya bashi amsa , yanxu gyad’a masa kai prince yayi batare da ya furta komai ba , fito little yayi musu take a wajan suka soma girgiza kansu suna bud’e harsunansu, kamar almara little ya sakar musu ball da sun je daidai wajan da sojojin suke zasu bud’e musu farcinansu kamar zasu ya kushesu , cikin Sauri sojojin zasu kauce su kuma su little su saka ball d’in su , sau biyu suna muku hakan , sosai kuma hakan yake saka prince da little cikin nishad’i su kad’ai sai faman sakin dariya suke , dariyar suce ta tsaya ganin yadda sojojin a wannan karan suke kauce wa su bruno duk yadda suka so dakatar dasu , yanxu wani irin fito little ya sakar musu me ‘kara da sunzo inda sojojin suke zasu hankad’asu su fad’i ’kas , gabaki d’aya a maimakon ai ball sai bruno suka dunga fad’ar da sojojin dan sosai akai training d’insu Bruno ko operation za’a fita da su Bruno ake fita dansu kansu sojojine kuma sosai ake biyan su ma’kudan kud’i dukda kasancewarsu karnuka amma sojojine su , ba ‘karamun horo suka shaba kuwa , little da prince tun suna dariyar abunda su Bruno suke har little ya tsugunna sabida dariya , musamman yadda Roby da Bruno suka had’u waje d’aya idan sun fad’ar da soja d’aya sai su hau kansa suyi ta tsalle, wallahi sosai karnukan bobo suka jigata sojojin nan , little tun yana dariyar mugunta har ya so Mayin Murmushi tare da dakatardasu , cikin d’an dariya dariya little ya furta � next idan kuka cigaba da cin mu simba zan d’auko yayi mun filla filla daku wlh� ya karasa yana sakin dariya , ‘keyarsa prince ya d’an duka � wallahi little baka ji� little bayasan ana ta’ba masa gashi idan ba big boss ne ko yaya bobo ba sai kuma uncle da prince dukda wani lokutan idan prince ya ta’ba masa gashin zai fara mita , yanxu ma bakinsa ya d’an ta’be kamar zaiyi kuka yazo zai ta’ba gashin prince , prince yayi saurin gocewa , hakan da yayi ne ya ‘kara har zu’ka little shi a lalle sai ya ta’ba gashin prince , lokaci d’aya suka fara yar guje guje tunda sunsa ba yanxu su big boss zasu shigo cikin gidan ba .

( wa d’annan yaran bakwaji Yasin 😦🙄🥱)�..

✨✨✨✨

*KANO*

Lokacin da Dady ya dawo ya dawo tuni baby tayi bacci gashi Sosai ya siyo mata abunda ta bu’kata har abunda batace ba dady ya siyo mata , gabaki d’aya sai ajje mata a fridge akai , ko tunanin a siyowa Eshaal basuyi ba , suka zauna suka ci kayan makwalashen da Dady ya siyo kafun su wuce part d’insu .

WASHE GARI

Ana kiran sallahr asuba Eshaal ta farka , wanka tayi ta canza kayanta zuwa wasu kafun ta tayar da sallar asuba d’inta , tana id’arwa ta bud’e alqur’anin ta tasoma karatun ba’kara saida ta tabbatar tayi izufi biyu tukunna ta ajje shi, ko cire dogon hijab d’in jikinta batayi ba ta fito falo a Daidai lokacin da AMMA ta fito falourn ita jikinta sanye da hijab , har ‘kasa Eshaal ta tsugunna ta gaisheta kamar yadda ta saba , murmushi AMMA ta sakar mata � kin tashi lapiya ?� Lapiya Lou Amma hope kina lapiya� cewar Eshaal ta furta wa AMMA a shagwa’be , d’an murmushi AMMA ta ‘karasakar mata � lapiya Lou �, itama Eshaal martanin murmushi ta mayar wa da AMMA tana mi’kewa ganin AMMA tana ‘ko’karin nufar d’akın Baby � ah ah AMMA ki barshi yanxu zanje na tayar da ita� bata jira amsar AMMA ba tayi saurin wuce sabida ba’karamun aikin baby bane tayi mata wula’kanci shiyasa ita zataje kome Baby zatayi mata da sau’ki akan tace zatayi wa AMMA , tana shiga kamar ta sani BABY na cikin blanket ta lullu’be jikinta ga ubansanyin da yake tashi cikin d’akin ko tiles ‘kafarka ta ta’ba sai kaji sanyi ta ko ina Ac hurowa take , a hankali ta ‘karasa wajan gadon baby tare da ta’ba pillow d’inta � Baby ?� Shiru bata amsa mata ba � baby� Eshaal ta ‘kara kiran sunanta amma babu reply , akaro na uku da ta kiratane baby ta d’an motsa batare da ta furta komai ba � Baby Kitashi lokacin sallah yayi fa� wani dogon tsaki baby taja tana ‘kara jan blanket d’inta � dallah malama ki fice mun daga d’aki ke wace iriyar mayyace wai ? Inaruwanki idan nayi sallah ko banyi ba bana san shish shigi, wallahi idan baki fita ba akan wacce matar zan wuce , shashasha kawai� cewar baby , Eshaal ta san tabbas zata iya aikata abunda yafi hakan ba shiyasa kawai ta girgiza kanta ta fice daga cikin d’akin.
Tana fitowa ko afuska bata nuna wa AMMA ba ta soma te maka mata da ayyukan gidan daman kusan kullum haka suke tare suke gyaran gidan , abinci ne kawai Eshaal take yiwa su baby dan tasan halin wula’kancinsu, saida ta kammala komai tukunna ta wuce kitchen ta soma girka musu breakfast , cikin ‘kan’kanin lokaci ta kammala , tana duba agogo taga ‘karfe 9:30am , ganin su baby basu fito bane yasa ta zuba musu nasu a cikin plate ita da AMMA , ta kai musu , duk yadda AMMA taso ‘kinci sai da Eshaal ta saka ta taci , suna gamawa Eshaal ta je ta wanke plate , sai a lokacin su baby suka fito , kallan eshall baby tayi tare da ta’be bakinta � Malama kizo ki zuba mun abinci ba canai ki bini da idanuwa ba� banza Eshaal tayi mata zata tsugunna ta gaishe dasu dady kawai taji ya jefo mata wani ‘karamun envelope yana dakatar da ita � bana bu’katar jin komai , gashi kar akaini bakin duniya , saura sati d’aya ku koma u.s � sosai farin ciki ya bayyana a fuskar Eshaal dan har wani murmushi take yi , wani ‘hangare na zuciyarta kuma tana yi mata ba dad’i sabida zata bar AMMA , rai a ‘bace baby ta kalli dady � dady wai kana nufin tare da wannan banzar zan koma school ,gaskiya wallahi bazan yardaba , babu inda zan koma da ita� tana kai ‘karshen zancanta ta wuce fuuuu rai a ‘bace , itama momy tsaki taja wa dady tare da bin bayan baby da Sauri , Eshaal kuwa ko a jikinta , zatayi wa dady Godiya ya daka mata tsawa akan tabar masa falour , da sauri kuwa ta d’auki envelope d’inta tabar d’akin.

✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨

**NEW YORK**
Chapter 68 · 0% Book details