Sashe 110
Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
sowa daman tun d’azu Bad Boys suke jiran zuwan Abla , itama Baby tare suka shigo da Bad Boys, ganin Fanan a wajan su Abla yasa ranta ya ‘kara ‘bacı ga wani haushin fanan da take ji, kujera d’aya daga cikin gang d’in Bad Boys ya janyowa Mai dala , cikin wani babba sarwa ya zauna tare da kallan direction d’in Abla , cikin jijji da kai ya d’aga murya akan ta zo ta tsugunna ta bashi hakuri, idan ba haka ba ya sa’ba mata , kallan baka da hankali fanan ta jefa masa dan ba ta tsoransu kwata kwata , tana d’aga masa ‘kafa ne shima Sabida ala’kar da ke tsakaninsu,� bakiji abunda nace ba ?� Cewar Mai dala , kamar yayi magana da dutse haka Abla ta mayar dashi, abincinta take ci hankali kwance , ran Mai dala ba ‘karamin ‘baci yayi ba shiyasa ya bawa d’aya daga cikinsu ya d’akko masa Abla, dariyar shakiyanci yasaka ya nufi inda Abla take , a zuciye fanan ta kallesa � baka da hankali ? Sai kuma ka ta’bata� girgiza mata kai gayen yayi � ah ah fa fanan kinsa ke ta gida ce muna d’ağa miki ‘kafa sabida eh ke Family Mai dala ce amma fa ki kiyaye � zai ‘kara saka hannu zai ta’ba Abla fanan a zuciye ta furta � wallahi idan kuka kuskura kuka ta’bata , sai na kira NANI na fad’a mata � jiyo inda MAI DALA yake yayi , cikin ta’be baki MAI DALA ya furta � share ta yi abunda na saka �. Hannu kuwa ya saka zai ta ‘bata yaji saukar mari a kumatu biyunsa sai sautin Tassss kawai da suka ji, shi kansa Wanda aka mara saida ya saki ‘kara sabida zafin marin da yaji , ba kowa bace face fanan da Abla , fanan ta Maresa a left kuma tunsa , Abla kuma ta Maresa a ‘bangaran daman da , cikin harara Fanan ta kalli Mai Dala � ka shirya amsa kiran Nani� daga nan ta kalli su Eshaal akan su zo su koma class , babu musu kuwa suka bar capterian , Bad boys zasu bisu Mai d’aya yayi saurin da katar dasu � karku bisu , fanan ta shiga cikin wasan , nasan zata iya kiran BiiBii kuma ba abunda zai hana yazo , let’s go� . Suna shiga cikin class Fanan ta basu hakuri, babu Wanda ya nuna wani abu sai ma chocolate d’in da Little ya bata ta fito musu da shi , kamar sun dad’e da sanin juna suka dunga hirar su wanda kusan gabaki d’aya hirar akan further maths ne da suk fara koyawa Abla Wanda akayi a baya . Lokacin da yan class suka fara shigo wa , duk Wanda ya shigo sai ya kalli su Abla ko kiji suna kuskus , a teacher ya shigo class suka fara , a haka idan teacher ya fita wani zai shigo har lokacin short break , yau ma basu fita ba suna class har aka dawo sauran teachers din suka shigo, lokacin Tashi nayi duk suka fito. A lokacin anzo d’aukar Abla , sallama tayi musu ta ‘karasa Wajan little da yake sanye da black p-cap sai wani black mask don fuskarsa , tana zuwa Daidai inda yake ta d’an ta’ba kafad’arsa sai kuma ta sun kuya ‘kasa , dube dube ya fara Abla ta saka masa dariya , sai a lokacin ya kula da ita � Lil ni kika tsoratar ko ?Dont worry zan rama , let’s go home � a haka suka shiga mota suna bar harabar school sai da suka fita babban titi sannan motocin sojojinsu sukai musu combo har gida .