← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 146

Sashe 115

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

‘Karfe 8:20 yau ta farka daga baccin da ya d’auketa sabida little ya riga da ya fad’a mata bazata je school yau ba, zuwa yanzu ta ji sau’ki sosai babu inda yake mata ciwo amma ba damar tace zata je school tunda an hanata zuwa. Shaf shaf wanka tayi ta shirya , yau shigar ‘kananan kaya tayi da yayi mugun fito da surar jikinta , kamar a jikinta aka d’inka kayan dan ba ‘karamin shape din jikin ta ya fito mata dashi ba,rigar jikinta Baby pink top ce da ta fito da breast d’inta sosai kamar zasu tsaga rigar su fito waje daga Samanta sai ta saka wata rigar ta d’aure igiyarta yadda jikinta bazai fito ba , a cikin yan kwanakin nan da ta ‘karayi jikinta ba ‘karamun smooth yayi ba , yadda fatar jikinta tayi kyau ko ta wani me samun hutun albarka. Gaban mudubin d’akin ta ‘karasa tana ‘karewa kanta kallo, kyakkyawar yarinyace Abla da fad’in kyaunta ‘bata bakine, sosai Allah ya bata baiwar kyau na fili da na ‘boye, tun daga kan round face d’inta har zuwa kan fararan idanuwanta masu kama da madara , kwayar idanunta ash colours ne masu shegen kyau sai wani ba’kin d’igo dake cikin kwayar idanta kamar tauwada da ya ‘kara haskaka kyan idanta , koya tamotsa idanuwanta sai dogon black lashes d’inta sun kad’a gashi long lashes ne da ita , ko ya mutum ya kalleta sai ya so ya ‘kara kallanta musamman idan ta zuba maka dararan eyes d’inta me matu’kar rikita mutum, gashin girar ta a cike yake sosai gashin black colour kamar wacce akai wa gyaran gira sabida yadda shape d’in girar ta ya fito sosai , hancinta dogo ne da ya ‘kara fito da tsantsan kyan fuskarta, gashi Siriri me kyau duk da baza’a kirashi da siriri ba , d’an kad’an Abla ta motsa lips d’inta , sosai kyawunsu ya fito sosai kalar pink , musamman yadda shape d’in bakinta yake kamar na love , daga gefe gefen fuskarta kyantaccen gashine masu kyau kalar ‘baki da suka kwanta luf luf a kan face d’inta, koya Abla ta motsa bakinta Dimples d’inta ne suke fito wa ta both side kumatunta. Irin su Abla ake kira da coca cola shape , dan ta ko ina Allah ya basu dan a cike suke taf.

Tana gama ‘karewa kanta kallo , wani farin lipgloss ta d’auka ta saka cikin cute love shape lips d’inta , da ya ‘kara haska mata pink lips d’inta , gashin kanta har ya fara fitowa dukda ba’a dad’e ba lokacin da Big Boss ya sa ta yanke amma ba lefi har ya fara dawo, mayafin kayan tayi rolling tare da fesa turare ka d’an ajikinta, duk da ba da yawa ta saka ba , amma ‘kamshin ya cika ko ina ta cikin d’akin , duk Wanda ya san Abla a da ya ganta a yanzu kuma zai iya rantsewa da Allah ba ita bace , Sabida yadda tafito sak a kyakkyawar matashiyar balarabiya. White half slippers ta saka da ya fito da fararan ‘yan ya tsunta , bata zame a ko ina ba sai falourn ‘kasa Inda su little suke , kamar kuwa ta sani , su ka d’ai ne a falour shi da prince kamar daman jiran fitowar ta suke , daga nesa little ya fara furta � wow! Wow! Wow!Lil wannan kyan naki ko a gasar kyau aka je sai kin lashe kowa a kyau�,face d’inta ta d’an kare sabida kunya da maganar sa ta bata � haba yaya little , ka dena tsokana ta fa , kaima kasan ka fini kyau � murmushi ya sakar mata kad’an � No little ki tanbayi yaya Prince , kin fini kyau , da ke da Yaya Big Boss bansan wanene yafi wani kyau ba , ko yaya prince ?� Shima murmushin yayi lokacin da ya furta � yes Lil , kinga da gasar kyau da little ake amma tun ba’aje ko ina ba ya fad’i tunda kin lashesa� wani murmushin Abla ta daki da yasaka dimples d’inta lotsawa � please yaya ku bari kuna sani jin kunyar ku fa � lokaci d’aya suka ‘kyal’kyale da dariya , cikin tsokana prince ya furta � it’s okay mun dena , bakiyi breakfast ba , kar abincinki ya wuce � haka suka jata har dinning sukai serving d’inta abinci, sai da taci da ‘koshi sannan suka dawo falourn,wani channel prince ya saka musu sai suka ci sa’a kuwa ana quiz , kallan little , prince yayi kafin ya mayar da kallansa kan Abla , wani tunanine ya fad’o masa , lokacin d’aya ya ‘kara kallansu � I have a quiz for you ! Duk Wanda ya cinye yana da babbar kyauta!� Murmushi kawai Abla tayi dan tasan ban da ita a ciki ai , � Menene prize d’in mu ?� Cewar little yana kashe masa ido , � Anything you want “prince ya bashi amsa , cikin Sauri little yace are you sure ?� Da yes kawai prince ya bashi amsa kafun ya furta � your time starts now! Duk question d’in da aka fad’a Wanda ya riga fad’ar amsa shine yake da mark� Lil kin yarda ?� Cewar little , kanta tayi knodding alamar Eh , da haka suka fara game quiz d’in, a karan farko little ya cita akai 1-0, a second round ma haka yaci ta akai 2-0, ana 3rd round ne Big Boss da Bobo suka shigo cikin falourn, gabaki d’aya basu kula da shigowarsu ba Sabida yadda suka maida hankali a cikin quiz din da ake, saura kad’an little ya bada amsa tayi saurin fad’an amsar , Daidai lokacin da aka fita short break, amsar da ta fad’a ne little yayi saurin cewa be yadda ba , ba Daidai bane , itama Abla ta kafe akan cewa Daidai ne , cikin dariya prince ya furta oya little explain your self, calculation d’in little ya fara step by step har ya kammala ,murmushin da ya ‘kawata face d’inta Abla ta saki, cikin shau’kin quiz din da suke ta ‘kara furta � Dagaske nake fa yaya little this time around ka fad’i�, amma still little yaki yadda, Big boss da Bobo na bayansu har yanxu basu san da shigowarsu ba , � Sis I told you kece kika fad’i� yanxu ma murmushi Abla ta ‘kara saki � shikenan na yadda idan nice ma fad’i zan zagaye duka gidan nan da rarrafe amma idan ka fad’I zakayi mana rawar monkey ka yadda � cikin sauri Bobo ya toshe bakinsa , baya so yayi dariya har su kula dasu wai rawar monkey , Big boss kuwa fuskarsa na a had’e babu ko single murmushi akan ta , Daidai lokacin da aka dawo bayan Abla tayi explaining nata , a duba mark kuwa Ablan ce tayi Daidai , cikin surprise little ya furta � how comes sister ? Bayan nima abunda nayi kenan� yes Daidai kayi mistake d’inta , 1 d’in da ka saka lokacin farkon solution dinka , zata ‘kara bashi amsa taji daddad’an ’kamshin turarensa , a hankali ta d’ago da eyes d’inta zuwa direction d’in da zuciyarta tafi mata a hasashe, cikin Sauri kuma ta du’kar da kanta ‘kasa , ganinsa shi da Bobo a tsaye hannun gabaki d’aya jikin aljihu sai dogon curly hair dinsa baki da yake shinning, murmushi Bobo ya saki lokacin da little ya furta � welcome back yaya �, har yanzu da murmushin akan face d’in Bobo lokacin da ya ‘karaso falourn , banda Big boss da ya nufi part d’insa batare da ya ‘kara kallan direction d’in da suke ba . Cikin tsokana Bobo ya furta � yau finally little zai yi mana rawar monkey ,� gabaki d’aya dariya suka saki lokaci d’aya, ko good 5 minutes beyi a falourn ba shima ya wuce part d’insa, yayi saura Little da prince sai kuma Abla , a haka suka shiga ba da game d’insu har aka gama suka tashi da equal mark.

Kallan time little yayi ganin lokaci yaja sosai � Lil please can you help me ? Ya’ya zaki kaiwa abinci , Nima sai prince ya tayani na kaiwa yaya nasa food d’in. Yadda ya kira Big Boss da Bobo da sunan yaya sai tayi Tuna’nın Bobo zata kaiwa abinci , su kuma su kai wa Big Boss shiyasa batayi musu ba ta amsa masa da toh , sai da aka gama had’a komai na breakfast d’insu taga little da prince sun d’auki nasu , tana ‘ko’karin tanbayar du part d’in Bobo taji maganar little da ya saka zuciyar ta harbawa kad’an � kiyi Sauri ki kai masa Lil , Ya’ya Big Boss baya san jira , daga haka be gama jira tayi magana ba suka wuce Shida prince , elevator ta kalla kad’an tana sakin ajiyar zuciya � Yau kuma bansan wani kalar hukunci zan samu ba idan nayi wa wannan bawan Allah lefi, Allah yasa baya cikin falourn ma � ta fad’a a hankali , kafun ta d’auki kayan breakfast d’insa ta nufi part d’insa .
Chapter 115 · 0% Book details