← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 146

Sashe 114

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

****** Gabaki d’aya yinin ranar a d’aki ta wuni tana duba littattafan ta , su Eshaal ne suka fad’o mata arai musamman yadda taga Baby tanayi mata abu kamar wacce taga bai warta, tuno da halin Babyn yasa ta d’an saki wani murmushin da kaici, duk rawar kanta husna ta da meta dukda ko wannansu yana da banbanci halaye musamman Baby da taga rashin kwa’bane ya fi lallatata, da ta tuno Eshaal da fanan yadda suka sake da ita duk da babu san ko wacece ba hakan yasa wasu ‘kwalla suka taran mata a cikin ido � Allah sarki Arwa bansan inda kike ba amma har yanxu ina ji a jikina kinanan a raye, Anee kema bansan wani hali kike ba a yanxu amma ina fatan kina hannu na gari �, lokaci d’aya Abla ta saka kuka Sabida tuno irin ‘bakar u’kubar da Suka sha wajan uwar karuwai, ta azabtar dasu sosai kamar ba mutane ba , sabida ganin basu da gata , musamman ita da Arwa, bata san dalili ba , batasan me sukai mata ba amma gabaki d’aya ta fi nuna tsantsan tsanar ta akan ta .

Cikin ‘kan’kanin lokaci ta dunga tuna rayuwar ta a cikin gidan uwar karuwai , moment d’inta da Arwa, Anee , Husna , harta Ilham , � Abla yunwa nake ji� Wannan kalmar kusan kullum idan zata ci abinci da ita take ci cikin zuciyarta sabida yadda Arwa ta saba fad’a mata duk lokacin da ta ji yunwa , ta d’au dogon lokaci tana tunaninsu kafin ta tattara komai ta ajje , ta mayar da hankalinta kan littattafan school d’insa .
3 nayi ta ‘kara nufar d’akin simba , yanxu ma ba ‘karamun mamaki taji ba ganin har ankawo masa a binci, ita kad’ai sai addua take wa little ta dan wannan aikin sane ko aikin prince. Lokacin da ta koma cikin gida Prince ya fita Sabida wani urgent case da yake so ya duba , sai little shima da yake filin Basket Ball, cartoon ta d’an kalla kad’an , lokacin sallar la’asar nayi na koma d’akinta itama .
9:30pm fruit kawai ta d’ansha ta kwanta , sabida duk lokacin da take Al’ada bata san zama cikin mutane dan ba ‘karamun ta kura take yi ba, ta jima a kwance a kan gado kafun bacci ya d’auketa Sam ta manta da coffee d’in da zata kai masa . Sai wajan 11 su Little suka nufi d’aki suma ganin Abla bata fito bane ya sa ya fara zuwa d’akınta, sau biyu yana knocking ba’a bud’e , shiyasa kai tsaye ya bud’e d’akın, acan saman gado ya hango fuskarta jikinta sanye da duvet ga light da ta bari a kunne, batare da wani damuwa ba ya kashe mata light d’in gabaki d’aya ya rufo mata ‘kofar.
*****”Wani irin dogon tsauni take hango wa masu shegen tsawan gaske , gashi ta ko ina wajan babu haske sai duhu ga kukan da ya cika d’urmur dajin, wasu irin manya manya mutanene suka soma biyosu, ta ko ina suna cunna musu huta , da ta juya zata gudu zata ga ana mi’ko mata hannu alamar ta cecesu, kafin tayi wani yun’kurun mutanan wajan zasu ‘kara sakin wani kuka ne gigita mutane da gabaki d’aya dajin, mutane ne daban daban suke mi’ko mata hannu ta cecesu ta ko ina , ga kukan mutane da take ji , wani lokaci kuma kukan ya ri’ki d’e zuwa kukan na miji. Gabaki d’aya manyan halintun sun gama rikita wajan ga feshin Jini ta ko ina � a rud’e Abla ta kwalla wani irin ‘kara sabida mummunan mafarkin da tayi , bud’e idanuwan da zatayi taga gabaki d’aya d’akin yayi duhu, wani ‘karar ta kuma saki a karo na biyu tana toshe kunnuwanta , ji take kamar yanxu ne mutanan suke mata magana, da karkinta take toshe kunnuwanta, nunfashinta har ya fara seizing musamman yadda ta tsani duhu , yau ko iba bud’e bakinta batayi sai jikinta da ya d’au rawa lokaci d’aya .

SORRY FOR THE LATE POST👏👏.

https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written
By
Mss Lee �

🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅
🦅🦅M.W.A🦅🦅

AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__

✨MSS LEE BUSINESS WORLD �

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer) Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.

NOT EDITED

S____32💞

Hankalinta ba ‘karamun tashi yayi ba sabida bala’in duhu da ta ga d’akin yayi mata , ko bakinta bata iya motsawa sabida yadda tayi bala’in rud’ewa , ga wani irin zufa da ya fara wanke mata fuska , a gigice ta fara bin kan gadan da hannu har ta sauka daga kansa , duk da haka bakinta yayi mata nauyin da zata iya yin ihun neman a gaji sai bin bango da take yi cikin tashin hankali , ‘kirjinta har sama da kasa yake yi sabida tasanin tsoran da ya kamata, da ‘kyar ta iya bud’e ‘kofar d’akin ta fito, a rud’e sai faman wai wayan bayanta take , gani take kamar yanzu take yin mugun mafarkin, tun kafun ta ‘bar wajan corridor d’in ta fara ganin duhu duhu na dum light a Wajan . Gashi bazata iya koma wa d’aki ba sabida tsoran da ya kamata , da kyar ta nufi kan stairs nan kuma akwai light me kaloli a wajan, bin ‘katan falourn tayi da kallo ganin ko ina shiru , hatta su little da ta saba ganin su a wajan basa nan , ta juya da niyar komawa kawai tajiyo kamar sautin mutum, a zabure ta juya zata gudu ‘kafarta ta d’an daki d’aya daga cikin stairs din, cikin tsananin bugun zuciya ta yi baya zata fad’i ’kasa , har ta sadakar mutuwa zatayi. Ga mamakinta sai taji kamar abu ya tare ta , cikin sauri ta bud’e idanuwanta ganin lokaci kad’an kuma an hankad’o ta tayi taga taga zata fad’i kafun ta tsaya da ‘kafafunta. Ba kowa bane face Big Boss da tun ihun ta na farko ya jita Sabida yana zaune a falourn , amma gabaki d’aya yadda yake operating system d’in gabansa bazaka ta’ba kawowa yaji wani ihu ba . Lokacin da zata fad’i kuma a maimakon ya ri’kota sai ya d’an tare ta da hannunsa d’aya kafun ya hankad’ata ta Mi’ke da ‘kafafunta. Sun kuyar da kanta ‘kasa Abla tayi ganin ko inda take be kalla ba yayi juya warsa . A hankali ta furta � Nagode !� Kamar wacce tayi magana da Dutse dan ko juyowa be yi ba balantana ya nuna yaji abunda tacen. Dogon ba’kin gashinsa ta zubawa ido har ya wuce daga ganin ta , a hankali ta furta � komai akai wa mutum baza’a ta’ba burgesa ba,jibi kamar wata kayan wanki ya tareni da hannu kamar yaga wani abun cutar wa ,ko ma dai mene ne oho , amma tunda ka tai makeni Nagode � motsin da ta kuma ji ne yasa ba shiri ta ruga a guje ta koma part d’inta , saida tsaya tayi addua sosai kafun ta iya komawa cikin d’akin, wani ajiyar zuciya ta saki lokacin da hasken d’akin ya dawo, har ta ‘karasa kan gadon bakinta da addua , ganin bazata iya koma wa bacci bane yasa ta fara addu’o cikin zuciyar ta , tun tanayi a zaune har ta zame kan gadon kafin baccin da ya ci ‘karfin ta ya d’auketa.
Chapter 114 · 0% Book details