← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 146

Sashe 84

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lumshe idanuwansa yayi sosai sabida ruwan da bobo ya watsa masa me shegen sanyi da har cikin gashin kansa saida yaji sa , a karo na biyu bobo ya ‘kara bud’e wani saban ruwan ya tuttula masa har farar shirt dinsa sai da ya ji’ke , daga inda mutum yake xai iya hango white singlet d’insa da farin fatar jikinsa. A maimakon bobo ya rage ‘karfin Acn sai ‘karawa ma dayayi, a hankali ya Mayar da kansa baya ya jin gına da jikin sofa d’in da yake , sosai jijiyoyin kansa suka mi’ke, wata allurar ya janyo batare da ya bud’e eyes din saba , da Sauri bobo yayi saurin d’auketa yana ja baya � why please? Kanaso kaji wa kanka raunine? Please kabar allurar nan haka �, ko ta kan maganarsa Big Boss be biba sai ma hannun sa d’aya da ya sake wa dressing ya mi’kamasa � Give it back !� Cewar Big boss , Baya bobo yayi kad’an � am sorry gaskiya bazan baka ba �, Lokaci d’aya big boss ya bud’e idanuwansa da sukai mugun yin jaa sosai , yadda idanuwansa sukai jaa sai ya ‘kara fito da kyawun idanunsa kamar ya saka kwalli, � kasan illa kake ‘ko’karin yiwa kanka , me yasa duk lokacin da ranka yake a’bace bazaka iya dannewa ba sai kayi wa kanka wannan allurar ? Please !”cewar Bobo, yanxuma hannunsa Big boss ya mi’ka masa a d’an zuciye ya furta � Give it back �, shima bobo a zuciye ya furta � Bazan bayar ba ! So kake kayi wa kanka illah ? Wazai kula da little? Prince? Uncle? Please ka rage zafin zuciyar nan taka please �, cikin cool voice big boss ya furta “Get out of my room �, bobo zai ‘kara magana cikin zafin rai Big boss ya ‘kara furta � I said get out of here �, girgiza kansa kawai bobo yayi batare da ya ajje allurar ba ya sata cikin aljihunsa tare da barin part d’in . Yana fita Big Boss ya lumshe idanuwansa da sukayi ja sosai, ya dad’e zaune a wajan jikinsa a ji’ke , kusan 10 minutes sai kuma ya tashi ya nufi toilet d’insa . Bobo yana sakko wa ya tarar dasu little a tsaye duk sunyi sarko sarko suna jiran sakkowansa , murmushin da ya sakar musu ne yasasu ajiyar zuciya � why kuka tsaya anan ? Ku dena damun kanku babu abunda ya sameshi , kunsan yanzune lokacin baccinsa , anytime ya tashi zaku gansa ya Fito okay?� A d’an shagwa’be little ya furta � yaya ko zanje na dubasa? Tunda ya fita jiya ban ‘kara ganin saba fa � hannunsa bobo ya kama suka nufi kan kujera � little banda rashin ji kuma kasan yayanka ayyuka sun masa yawa ko?� Kansa little ya d’aga masa � then allowed him to relax jiya be dawo gida da wuri ba ! Kaga yau ko training baza muyi ba , Nima guduwan training din zanyi � da Sauri prince ya matso kusa dashi � Dagaske kake yaya bazayı ba?� Daman a cikin su babu Wanda yafi tsanar motsa jikin nan kamar prince shiyasa bobo yana amsa masa har da wani juyawa yayi na farinciki � hannunsa d’aya ya dunkule tare da furta � yessss�. Yaya � little ya ‘karakiransa , shima amsa masa bobo yayi yana kallansa � yaya please yau munasan zuwa siyayya kaji � tell me what you want sai a kawo muku har gida � da Sauri little yace “No yaya wannan siyayyar little sister ne , kaga ya kamata ta za’bi kayan da take so ko? Please just say yes and bata iyacin abincin mu bafa “kumatunsa bobo ya shafa � Are you happy?� Yes yaya sosai , be bari bobo ya kuma magana ba ya furta � yaya ina farin ciki sosai, I also have a sister now , inaso na sata farin ciki itama , bata da family , ni kuma ina da ku my only family, and now we are 6 not 5, okay ?� Kaifa fi’ilinka ya maka yawa tunda ka samu sister kake behaving sai kace wani babba �.� Uncle bai’karasa maganar da yakeso yayi ba Sabida ‘kamshin turaran Big boss da suka ji daga sama , gabaki d’aya cikin sauri suka kalli direction d’insa , yana tsaye daga bakin elevator d’in da ya fito fuskarsa gabaki d’aya babu fara’a , ba kamar ko da yausheba yau face d’insa tafi ta ko Yaushe had’ewa shiyasa lokaci d’aya little da prince Suka shiga taitayinsu , uncle da bobo kuma idanu kawai suka zuba masa. Kamar ko da Yaushe sanye cikin wasu white d’in kayan Hermes farare tas dasu riga da wando said’an jikin rigar da aka yiwa ado da d’an ba’ki kad’an, Sabida yadda rigar ta kama damtsen hannun sa sosai muscle dinsa suka fito farare tass da su , ‘kafarsa sanye take cikin black d’in Nike Air Max din ta kalmi ,yau hatta gashin kansa be tufkeba kamar yadda ya saba sai nannad’e shi da yayi , hakan ya bawa farar kyakkyawar fuskar fitowa sosai ga Diamond necklace d’insa da kullum baya rabuwa da shi, sau d’aya ya kalli ko wannansu yana d’auke kansa , dan gabaki d’aya yaji maganganunsu, yadda su uncle suke binsa da kallo ne yasa ya ‘kara had’e face d’insa yana takowa a hankali kamar bayasan taka ‘kasa , har ya ‘karasa sama akan white sitter suna binsa da kallo, ko sau d’aya be d’ago ya kallesu ba sai yayi kamar ma baisan da zaman suba, � Morning yaya� cewar prince da little da suka had’a baki kusan a tare , bai amsa musu da baki ba sai lumshe eyes d’insa da yayi kad’an alamar amsawa , gabaki d’aya falourn shiru ne ya biyo ba , sabida mamakin fitowar Big Boss a wannan lokaci , dan yawancin lokuta a wannan lokacin ne yake bacci , d’ago da eyes d’insa yayi ya zubawa little , cikin Sauri little yayi masa fiki fiki ido, d’an motsa lips d’insa gefe d’aya big boss yayi da hakan ya bawa dimple dinsa lotsawa , gabaki d’aya sai suka tsaya kallansa duk da abunda yayi baza’a kirasa murmushi ba sannan baza’a kirasa ya’ke ba , ganin yanda suka wani kallesa ne yasa ya tsuke face d’insa , cikin cool voice d’insa kamar bashi ba ya furta � You are happy because of that thing ( Abla 😂) ryt�, yadda ya kira thing d’inma kamar Wanda aka saka dole , da farko little begane wa yake nufi ba saida yaga kallan da prince yake masa , da Sauri ya furta � yes yaya�, hannu d’aya big boss ya saka ya shafa girarsa da take a tsage kamar ba zai kuma tanka wa ba sai kuma ya ‘kara furta � you all want to leave with her ?� Ya ‘karasa yana kallan prince da little , cikin Sauri suka furta � yes yaya� dan ko magana yayi bayaso ayi masa knodding , sannan bayasan ‘bata lokaci koda kuwa sai yi hour kafun yayi magana . Kansa yayi knodding a hankali, shi kansa bobo kasa magana yayi yasan tunda ya fara kiran Abla da thing ba lalle inuwarsu tazo d’aya ba , bai kai ga ‘Karasa maganar zucin saba sabida saukar muryar big boss da ya ‘karaji � bring her here�, lokaci d’aya gabaki d’aya Suka zaro masa ido, little kuma cikin sauri ya nufi d’akin Abla , � Ba ka yadda ta zauna ba ?� Cewar bobo dan har ga Abla Bayaso big boss yayiwa Abla komai , amma ganin ya sharesa ba tare da ya tanka masa ba ne yasa yayi shiru shima yana jiran yaga me zaiyi, uncle kam sarautar Allah ya zubawa ido shi kansa ya kasa magana dan besan me Big boss zaiyi ba . Ko cikakken 3 minutes little beyi ba suka sakko shida Abla da wani irin masifaffen ‘kamshin turaranta ya do’kosu dukda ko kwatan kamshin turaran big boss beyi ba , kanta a ‘kasa cikin shigar doguwar rigar da tayi purple colour da yayi mata kyau sosai sai veil d’insa da ya ‘kara haskota, tun kafin su ‘karaso cikin falourn bugun zuciyarta ya fara da Sauri Sauri, hannunta har ya fara rawa duk da bata d’aga Kai ta kalli mutanan falourn ba amma ta gane masifaffen ‘kamshin turaran jiya da ta dad’e tana ji cikin hancinta, lokaci d’aya taji kayan cikinta sun juya sabida tsoro dukda bata d’aga fuskarta ba Sabida shakkar d’ago da face d’inta da take , hatta tafiyarta saida ta canza sai faman hard’e ’kafa take , suna shigowa cikin falourn ta d’an d’ago kanta da niyar gaishesu, idanuwanta basu sauka ko ina ba sai a kan face d’insa da ya lumshe , lokaci d’aya ta fara ‘ko’karin birkicewa har wasu kwallane da ita kanta batasan dalilin fitowarsuba suka tarar mata cikin idanuwa, cikin sauri ta d’auke eyes d’inta , muryarta har rawa yake wajen furta � ina.. ina.. kwana…� gabaki d’aya sai suka ‘kara kallansa sabida sunsa da shi take amma kamar Wanda akai magana da gunki, akaro na biyu ta ‘kara furta � ina� kwana � be amsa mata ba , shi kansa little a tsure yake dan gabaki d’aya ya manta be fad’a mata kada tayi Hausa ba, koda ace bata iya turanci ba zai fi mata alkairi akan tayi Hausa a gaban big boss dan yana d’aya daga cikin abunda yayi mugun tsana shiyasa duk lokacin da yake gida basa amfani da Hausa, lokaci d’aya Abla ta fara shash she’kar kukan da bata san dalilin fitowar sa ba, prince har da dafe kai ganin tana ‘ko’karin janyo musu wani hawan ruwan, rai a ‘bace ya bud’e eyes dinsa da sukai mugun ‘kad’awa na ‘bacin rai, wani irin mugun kallo da ya zuba mata lokaci d’aya tayi kneeling dan sosai wani irin tsoran sa ya ‘kara shiga cikin zuciyarta , ita kad’ai bakinta sai rawa yake sabida tsananin tsoran da ya kamata , d’an ta’be bakinsa yayi kad’an yana d’auke eyes dinsa zuwa na little da yayi tsutsu dashi kamar mara gaskiya , akaro na biyu ya ‘kara bud’e bakinsa cikin tsantsan American English d’in da ya zauna masa ya ‘kara furta � duk kun amince da zamanta ?� Da Sauri cikin turancin
Chapter 84 · 0% Book details