← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 146

Sashe 126

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written
By
Mss Lee �

🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅
🦅🦅M.W.A🦅🦅

AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__

✨MSS LEE BUSINESS WORLD �

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer) Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.

NOT EDITED

S____35💞

Tun da tayi hugging d’in sa be motsa ba , cikin Sauri gabaki d’aya sojojin suka sara mata tare da juya musu baya , hakan da sukai ba ‘karamun jawo hankalin mutane yayi ba , kowa mamakin sa Mene ne had’in Abla da wad’an nan mutanan , musamman yadda suka ga sojojin sun sara mata cikin girmamawa , hatta Eshaal da fanan da suke d’an nesa da ita mamaki ne ya kama su , Abla kuwa bata ma san suna yi ba sabida kukan da take ga zazzafan zazza’bin da ya ‘kara rufe ta , Lumshe eyes d’insa Big Boss yayi musamman yadda yaji Abla ta rungumesa , kusan second 30 suna a haka kafun ya saka hannun sa yana ‘ko’karin zame ta daga jikin sa , Daidai lokacin da Bobo ya fito dasu Alice , gabaki d’ayan su sun farka sai faman ihu suke , Alice babu abunda take kira sai sunan � Big Boss � gabaki d’aya ta fita daga hayyacin ta , fuskarta gabaki d’aya tayi jaga jaga da ita,suna fitowa ta hango Big Boss da Abla , cikin Sauri ta nufi wajan su a haukace , yadda ta nufo wajan ne yasa Big Boss Fasa ture Ablan yayi sai ma ‘kara hugging d’inta da yayi sosai a jikin sa, kasa motsi Alice tayi sai zamewa da tayi ta soma burgima tana ihu � bazai faru ba, bazan yadda ba , Big Boss kai nawa ne , ni kad’ai zaka so , sai na kashe ki , sai na kashe ki da hannu na � ta ‘karasa tana nufo inda Big Boss yake , gabaki d’aya sojojin nan bindugu suka saka wa Alice , da hannu d’aya Bobo ya dakatar dasu dan shima so yake yaga karshen iskancin Alice , tana zuwa zata ta’ba hijab d’in Abla , Big Boss ya tsunka mata mari dama da hagu da har saida Alice ta fad’i ’kasa lokaci d’aya jinta ya d’auke mata , idanuwan ta ne kawai suke motsi da ta mugun zazzaro suna bin bayan Abla da kallo , a hankali Big Boss ya soma tapping bayan ta , kamar Wanda aka yiwa dole ya furta � it’s okay ! Let’s go home � sai a lokacin Abla ta Ankara da abunda tayi cikin sauri tayi ‘ko’karin zamewa ya ‘kara hugging d’inta yana tapping bayan ta , ga Alice da LG da gabaki d’aya sukayi suman wucin gadi, zameta Big Boss yayi a jikinsa , kallo d’aya yayi mata ya d’auke kansa tare da jefa mata Wannan mugun kallan nasa , cikin Sauri Abla ta sunkuyar da kanta Sabida wani yar da taji lokaci d’aya , bata tashi sumewa da al’amuran Big Boss ba sai da ya bud’e mata mota da kansa , hannunta d’aya data ri’ke rigarta ya kamata har wajan motar ya saka ta , tana d’ago da kanta ya jefa mata mugun kallan sa , yadda yayi gabaki d’aya sai ya ‘kara zama kamar masoyan da suka dad’e cikin gogin soyayya, wasu tunani ma suke ko shagwa’ba Abla take masa lokacin da ya kallesa, hakan da yayi ba ‘karamun mamaki ya bawa kowa ba , hatta Bobo kasa motsawa yayi Sabida shock , duk da yasan halin Big Boss sarai yasan abunda yake , mamakin sa be gama ‘karewa ba sai da Big Boss ya rufewa Abla mota, ya zagaya d’ayan side d’in , cikin Sauri Victor ya bud’e masa mota ya shiga.

Jabcon, Alice da LG kuwa gabaki d’aya jansu sojojin sukai har da cikon na hud’un su , ko arzi’kin zama a mota basu samu ba , sai a boot da Robert ya sassakawu, cikin Sauri kuma Robert ya bud’e Bobo mota, ba’a d’auki cikakken mintuna ba gabaki d’aya motocin suka soma tafiya a guje , tun kafin su fito gabaki d’aya aka bud’e musu gate, manya manyan motocin tawagar Big Boss ta nufi right side , motocin Bobo kuma sukayi left side . Gabaki d’aya suna barin wajan makarantar neman hargitsewa dan babu Wanda be shiga rud’un abunda ya faru ba , yan class d’in Abla kuwa kasa magana sukayi sai zazzaro idanuwa da sukai, babu Wanda hankalin be tashi ba , musamman yadda sukaga yadda sojojin nan suka sara wa Abla , kowa tunanin da yake cikin zuciyar sa wacece ita ? Dan ko tanbayar juna sun kasa gani suke suna maganar ta sojojin na zasu dawo, Su Eshaal ma gabaki d’aya jikin su sanyi yayi , da ‘kyar suka iya koma class ganin Abla bata tafi da jakar ta yasa Eshaal ta d’aukar mata.

A cikin mota kuwa tunda Abla ta sunkuyar da kanta ‘kasa ta kasa koda kwakkwaran motsine sai addua da take ta nana tawa cikin zuciyarta , ko idanuwan ta takasa d’akko wa balantana tayi gangancin kallan side d’in da yake . Big Boss kuwa kamar be san da wanzuwar wani halitta a cikin motar ba , musamman yadda ya lumshe eyes d’insa ,Ya d’an jingina da kujerar sa , Abla kuwa neman nutsuwar ta tayi ta rasa sai hannun ta da take mamma tsawa, har suka ‘karasa gida bata sani ba sabida sun kuyar da kanta ‘kasa da tayi , tana jin anyi parking tayi saurin d’ago da idanuwanta , ba shiri ta kama hannun ‘kofar zata fita ganin sun ‘karaso cikin gidan , rai a ‘bace Big Boss ya finciko hannunta, har tana bige wa da abun coffee d’in wajan , d’an ‘karamun ‘kara Abla ta saki kad’an Sabida zafin matse mata hannun ta da yayi , cikin kausash shiyar murya Big Boss ya furta � Are you mad ?� Shiru Abla tayi masa tana d’an sunkuyar da kanta ‘kasa , hannun bata ya ‘kara murd’ewa da Sauri Abla ta saki wani ‘karan tana girgiza masa kai � Dan Allah kayi hakuri�,yar far da hannun nayi kafun ya nuna mata ‘kofar fita , da Sauri ta bud’e kofar ta nufi cikin gida ko wai waya bata yi , su jabcon ma d’akin horo aka kai su , Big Boss na cikin motar amaimakon ya fito sai Victor ya tayar da motar suka bar gidan, a guje suma ragowar sojojin suka mara musu baya.
Chapter 126 · 0% Book details