← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 146

Sashe 47

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

******** ABUJA NIGERIA A hankali Abla take shash’she’kar kuka gudun kar Binta shagala ta fad’awa uwar karuwai abunda tayi mata , ita kuma ta saka su zinariyya su no mota shiysa tayi zamanta a wajan , ba tsoron binta shagala ko uwar karuwai ne yasa ta kuka ba , zafi da zuciyarta take matane yaşa take kuka , ji kanta take kamar acikin wata ‘kuntacciyar rayuwa , batasan iyayenta ba , bata danginsu ba , bata san a ina suke rayuwa ba , suna mace ko a raye ?, suna tunawa da ita ko sun mata da ita ? So? Bata san shi ba , batasan ya yake ba, abu d’aya ta sani, tun ta sowarta har zuwa yanxu batasan wani abu wai shi gata ba ko farin ciki , abu d’aya ta sani , ta taso cikin kuncin rayuwar, rayuwar da tunda tayi wayo ake mata gori ita da wacce ta tausayawa rayuwar ta lokacin da take jinjira , matar da ta sadaukar da farinciikinta tana kula da ita duk da kasancewarta karuwa. A wannan duniyar barıkin ta koyi abubuwa da yawa aciki,abu d’aya ta sani , in dai kana bukatar abu to tabbas zaka mayar da saka mako,a duniya idan akwai abunda Abla ta tsana to tabbas karuwanci ne na farko, tun tana tunani har baccin wahala ya d’auketa a yadda take a cunkushen nan. A cikin gida kuwa sabida bariki irin na binta shagala ko a fuska bazaka ga alamar ‘bacin rai tattare da itaba duk da abunda Abla tayi mata ya mugun ‘bata mata rai, amma da yake ta san ta kan duniyanci fuskarta cike take da Anna shuwa a ciki, a maimakon Abla da Husna ta tafi d’aki ganin yadda take binta da kallo tun d’azu , har dare ya fara ratsa wa babu Abla babu alamarta , Allah sarki Arwa tun da taga dare yayi sosai bata ga Abla ba ta kasa zama sai faman jiran tsammanin dawowarta take, shiru har wajan shad’aya sosai hankalinta ya Tashi ta kara komawa d’akı ko zata tarar da ita amma shiru babu ita babu alamarta , sai ma Anee dake zaune kankatifarsu sun bud’e ‘kartuwar gashshiyar kaza sai ci suke ga manya manyan kwalin exotic d’insu , da kallo suka bi ta Dashi ganin kamar akwai da Muwa a tattare da ita , ta’be baki ilham tayi kafun ta furta � ke kuma lapiya kamar wacce akai wa mutuwa zaki shigo mana a furgai furgai haka ?� , bansa Arwa mata , sai kum ta mayar da kallanta kan Anee � Anee bakiga Abla ba ?, tun d’azu nake jiran ganin ta amma haryanxu babu ita babu alamarta..�, bata ‘karasa ba sabida dariyar da ilham ta kwashe da ita � Sabida wannan abun ne wai kika burkice haka ?, nasan tana can tana kuka tunda abunda take kurin’boyewa Anta’ba zanso naganta nima ba �, kallan me kike nufi Arwa ta bita dashi, yanxu ma wat dariyar ta ‘kara kwashewa da ita � bani nakar zomanba fa , rataya aka bani,rayuwar kuce dole sai kun gur’bata kamar sauran , dan dole ki zabi d’aya ko ki fara shaye shaye ko ki fara karuwanci , kin ga Anee yanxu shaye shaye ya bi jikinta, husna ta za fara shiga hanyar karuwanci, waccen banzar da ita kuma kinga sai ta zama karuwar gida kawai…�, bata ‘karasa ba sabida yadda Arwa ta daddage ta buge bakın ilham da harsaida tayi ‘karamin kara Sabida taji zafin dukan , zata mike aneee tayi saurin ri’ko � ki manta kawai , kiyi hakuri mana �, fusge hannunta ilham tayi tana nuna Arwa da yatsa � tabbas bakisan wacece ni va shiyasa kika tafka wannan kuskuren , ada inashare duk wani haukanku Sabida na samu biyan bu’kata ta amma banda yanxu , Wallhi dukannan da kikai zaki gane shayi ruwane , Indai nice ilham �, tsaki Arwa ta ja duk da yadda take da tsoro yau saida ta tankawa musu � Menene kuma bamusani ba na halin naki? Kina tunanin bansan cewa labarin da kika babu nacewa iyayenki sun mutu duk karya ne ? Ko kuma siyarda mutumci na da na Abla da kuke shirin yi? Ko muna furta Anee da har kikai sanadiyar sata ta fara shaye shaye , duk da husna kwad’ayi da san zuciyar ta ne ya ja mata wannan ba’kar rayuwar amma kefa? Komai ma rayuwarki ‘karya ce � batare da damuwa da maganganun Arwa ba ilham ta ta’be baki , Aneesa kam sai faman lumshe ido take sabida maganin da ta sha yanxu da alama batajin me suke cewa ma � bakiyi ‘karya ba , duk abunda kika fada hakane sabida banasan naganku cikin farinciki, inaso naga rayuwarku ta gur’bata, inaso naga rayuwarku ta gur’bata kamar yadda tawa take a gur’bace, sau da dama na so kawar dake Sabida idanu da kika samun har kike ‘ki’karin fad’awa abla abunda kikaji muna tattaunawa da uwar karuwai, amma shegiyar Ablar nan kullum cikin bayyana take , maganar da kikaji Hakane,eh Hakane , ni ba nazo nan gidan sabida gata ba , nazone Sabida na lalata rayuwar yan mata masu irin shekaruna kamar yadda kwartan Dije yar kwal wato mahaifiyata yake tan haddi na , yasa na koyi bariki , sanin cewa uwar bariki aminiyar Dije ce yasa nazo gidan nan , kuma nayi sa’a na samekun duk da gabaki d’aya kudin gidadawane marasa tunani kun kasa fahimta , duk da ibtissam taso fahimtar wani abu amma na wuce tunaninta �, ta fad’a tana Kallan Arwa da ta gama shiga shock din maganganun Iham � kınsan Menene abun burgewar, tun ina 12 years na san d’a namiji sannan yanxu a rayuwa ta bani da wani babban buri kamar naga lallace war Abla, wallahi na tsaneta, Sabida duk cikin gidan nan tafi kowa kyau , tafi kowa gashi, tana da jiki me kyau , sosai hakan yake ‘bata mun rai Sabida banaso taji dad’in rayuwa , na fiso taita wahala a haka karta samu farinciki�, idanuwanta akan Arwa ko tsoran wani ya shigo batayi ta cigaba da maganar � bawai na fada miki maganan nan dan naji tsoroba, na fad’a miki abunda ya kamata ki sani sannan kema ki shirya , Indai ni Jinin Dije Yar kwalce �, ta karasa tana bin Arwaa da kallan kaikai ce tai ficewarta daga d’akin tana barin Arwa da Tashin hankali , hannu ta d’ora a sama tana fad’in “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un da ma duk wannan plan din ilham ne ? Shiysa duk lokacin da Suka kwanta suna tashi zasu ga bata nan� tunani Arwa ta somayi , ta fad’awa Abla ko karta fad’a mata , tasan Abla bazata ji dadi ba musamman yanxu da batasan halin da take ciki ba shiysa tayi wa kanta al’kawarin bazata fad’a mata va . A d’akın ta zauna tana jiran tsammanin ganin Ablaa , tun tana saka ran ganinta har bacci ya fara fuskarta, lokaci d’aya kuma wani wahalallan bacci ya d’auketa. Kiran sallah asuba ne ya farkar da Abla daga baccin da ya d’auketa, bakinta d’auke da adduar tashi daga bacci da bud’e idanuwanta , idanuwanta har sun ri’ke , sosai taji zafin wuyanta sabida yadda tayi bacci, tasan yanxu su zinariya suna ta nemanta ganin bata nan , a hankali ta fito daga cikin store din, duk da ydda zuciyar ta take bugawa hakan be hana ta tunkari gidan ba , tana shiga babu kowa. Falon , kai tsaye d’akinsu ta nufa nan ma Arwa da Aneesa kawai ta tarar cikin d’aki, kai tsaye toilet ta nufa ta tsarkaka jikinta , sai datayi sallar isha’i da asuba tana kaiwa Allah kukan ta kafun ta tafi Arwa da Aneesa akan su tashi suyi sallah , gabaki d’ayansu da farin ciki Suke kallanta har da had’a baki wajan furta � kindawo?� Kai Kawai Abla ta d’aga musu dan ko kanta bata san d’aga wa , suna shaf shaf suka tashi sukayi sallah dan Abla ce kawai me tunatar dasu sallah arayuwarsu. Har ‘karfe tara babu Wanda ya shigo d’akin , itama abla bata fito waje ba Sabida zafin da wuyanta yake mata, amma abun mamaki yau gabaki d’aya yaran binta shagala ne suka gyara ko ina na cikin gidan harda kawo musu abunci dukda abunda tayi wa binta shagala, haka kurin bata yadda da abincin ba shiyasa bataci ba ta barshi, tana fitowa falo suka ci Karo da binta shagala taji uban ado, yadda abla take kallanta itama ita take kallo fuskarta cike da murmushin bari ırin nata � baby ba gaisuwa ?� Cewar binta shagala , banza alba tayi mata tayi ficewarta daga gidan , girgixa kai Binta shagala tayi tana bin hanyar da Abla ta fita da kallo, kai tsaye d’akin uwar karuwai ta nufa, ko sallama batayi ba ta banka kofar d’akin ta shiga , lokacin da uwar karuwai take cin chips da Kwai abunta , tana ganin binta ta Soma washe mata baki � kina rayuwa cikin yara ‘kanana bakyaşamın kud’i ta dalilinsu? To Menene anfanin barikin naki? Hajiya duniya ta bun’kasa yanzu da yara zaki samu ma’kudan kudin da har zakiyi ta juya su san ransu, ya kika ganni? Kinsan ba ‘karamin kud’ine ya zauna munba, ta ‘karasa tana juya Orobo (lukuti)d’in jikinta , samun waje uwar karuwai tayi tana jinjina maganar binta shagala kafun ta saki a jiyar zuciya “ban’ki ta taki ba binta amma taya kike tunanin za a fitar da yaran batare da mutane sun Ankara ba ?, dan tabbas inaso na dunga fancanawa cikin daula �, anzo inda take so shiyasa ta saki wani shu’umin murmushi tana kallan kawar ta � wannan ba matsala bane, zan temaka miki amma mutum d’aya zan fara fitar miki da ita , kina zaune zaki samu 20million�, zaro ido uwar karuwai tayi tana furta � 20 million fa kika ce ? �, kanta binta ta jinjina mata alamar hakane , da Sauri uwar karuwai ta furta � na Amince amma wa za a fara fitar wa ?� Yarinyar da na d’auka jiya �, cewar binta , katseta uwar karuwai tayi ta hanyar furta � kardaki kice Abla kike magana ? Kinsan taurin kan yarinyar nan kuwa ? Cikin ‘kan’kanın lokaci zata ‘bata mana shiri me zai hana ki d’auki wata a cikin su ga
Chapter 47 · 0% Book details