← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 146

Sashe 13

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

karfe 6:30pm motocin Bobo Suka shigo cikin harabar building d’in gidan ,gabaki d’aya soldiers d’in kowa yashiga taitayinsa , Adil na jin durar motocin ya zabura zai gudu uncle iron man ya mayar dashi kan kujerar da karfi ya dam’ki hannun uncle kuwa , Adaidai side d’in building d’insu motocin nan sukai parking tsawan mintuna biyu da bud’e masa mota da akai kafun ya fito cikin takun manyan sojoji masu ta’kama da izza , yana fito wa daga cikin motar gabaki d’aya sojojin suka sara masa , basu ba hatta wa’yanda suke nesa dashi gaba d’aya kowa sai da ya sara masa , ganin yanda fuskarsa take a had’e ne yasa kowa ‘kara shiga taitayinsa, daga hannunsa na dama wani farin bandage ne daya zagaye tafin hannunsa dashi, a hankali ya soma taku kamar bayasan taka ‘kasa, duk daku d’aya da zaiyi da bugawar zuciyar Adil da gabaki d’aya ya dure, yana zuwa daidai bakin kofar shiga wani green d’in abu ya haska kafun ya fara kiran sunan “Bobo is back�, . Kara damke hannun uncle , Adil yayi gabaki d’aya tausayinsa ne ya kamasu shida prince ganin lokaci d’aya yana neman rikicewa , Bobo na shigowa cikin falon ya tarar dasu su uku a zaune da Sauri ta saka hannunsa me bandage d’in a aljihu, dukda yadda ransa yake a had’e hakan be hana yasassautashi ba , cike da girmamawa ya gaishe da uncle d’insu batare da ya kalli inda prince da Adil suke ba , cikin yar in ina prince ya furta � welcomed back yaya bobo �, batare da ya kalli inda prince yake ba ya d’an jinjina masa kai, Adil ma kamar zaiyi kuka magana a rarrabe ya furta “Ya..Ya Bo…� be karasa maganar saba ya had’iye halamansa sabida kallan da bobo ya jefa masa kafun ya nufi inda Elevator d’insu yake . Fashewa da kuka Adil yayi ganin Bobo ya sharesa,gabaki d’aya rarrashinsa su uncle suka fara cikin sakin yalwataccen murmushi uncle ya furta � Banasan wannan kukan , kaje ka basa hakuri kawai�, kallansa Adil yayi “Amma uncle fushi fa yake dani�, girgiza masa kai prince yayi � kamanta abunda yaya bobo ya koya mana , idan munyi lefi mubada hakuri? Just kaje babu abunda zai maka kaji?�, kallan uncle da prince yayi lokaci d’aya suka d’aga masa kai, da sauri yanufi elevator shima, Daidai part d’in bobo ya tsaya ya’ki shiga, har zai juya sai kuma yasaka turn print d’insa take a Wajan kofar wajan ta bud’e babban falonsa me shegen kyau da ‘kayatuwa ya bayyana , kamshin freshener d’in lavender cedar leaf linen ne ya doki hancinsa, cikin sand’a Adil yasoma tafiya sabida kar aji ‘karar tafiyarsa, babu kowa a falon, kofar da ya gani a bud’e ya nufa bakinsa d’auke da sallama, da Sauri bobo da ke dressing d’in hannunsa yasaka hannun cikin aljihu yana bun fuskar Adil da kallo, sallama yayi Bobo ya amsa masa yana binsa da kallo, a mara rai ce Adil ya furta � Yaya bobo kayi hakuri kaji?� ‘Dan harararsa bobo yayi ,� ni babu ruwana tunda baka jin magana , idan mesu ya dawo sai kayi masa bayani�, da Sauri Adil ya shigo cikin d’akin � Dan Allah yaya bobo na, kawai nayi missing d’insane fa , shine naje na kallesu �, tausayin Adil , Bobo yaji ganin yana ‘ko’karin yi masa kuka � fine , idan ka ‘kara rashin jinka kuma ni babu ruwana, lokacin sallah ya kusa �, ka hakura ? Adil ya tanbaya , gyada masa kai bobo yayi , da Sauri yazo zaiyi hugging d’insa bobo ya dakatar dashi � idan na fito sai ayi hugging d’in, lokaci yana tafiya�, toh kawai Adil yace masa tare da barin d’akin fuskarsa a washe tunda bobo ya hakura, hannunsa me ciwo bobo ya ciro yana ‘kara bin yankan da kallo, ko da wasa yasan bazai bari Adil yaga wannan ciwanba, shiyasa ya ‘karasa dressing d’insa , kafun ya shirya cikin wasu Lious Vuitton d’in kaya riga da wando, daga jikin rigar akwai tanbarin VL me shegen kyau d’aya ‘karawa farar rigar jikinsa kyau , damtsen hannunsa sosai ya fito cikin farar jigar jikinsa, yalwataccen ba’kin gashin kansa duk ya kwanta masa a ‘keyarsa kasantuwar baya tara gashi sosai akansa . Kiraye kirayen sallar magariba ne yasa ya fito daga d’akinsa, lokacin gaba ki d’aya su Adil suna tsaye suna jiran sa, yana fitowa masallacin gidan suka nufa , kamar ydda suka saba kullum jam’i suke bi tare da musulman sojojin, wa’yanda ba musulmai bane sukuma suna kula da tsaran gidan. ‘Ka ida idan suka shiga sallahr magrib basa fitowa sai anyi sallar isha’i, suna idarwa Bobo tare da wasu sojoji manya manya suka nufi wata hanya , Adil zai bisu uncle iron man da prince suka dakatar dashi, zaiyi magana uncle iron man ya katse shi � banasan musu Adil, dare nayi lets go �, girgiza masa kai yayi ya rike hannun uncle na hagu, dayan hannunsa kuma prince ya rike masa . Suna shiga prince ya nufi dinning daman bashi da jumurin yunwa , shima Adil dinning d’in suka nufa shida uncle , James ne yafito yayi serving d’insu , ko wannansu favorite food d’in sa yasoma ci, Adil ne kad’ai be soma cin abincin saba , prince ne ya kallesa � me yasa baka cin abincin ka ?� , spoon d’in sa Adil ya d’auka � ina jiran yaya bobo ne �, ‘karamun tsaki prince ya saki tare da ci gaba da cin abincin sa, kallan Adil, uncle yayi � kaci abincin ka , idan ya dawo zan sashi yaci okay?� , kamar wani ‘karamin yaro ya mikawa uncle ‘karamin d’an ya tsansa alamar Alkawari, shima uncle yatsan nashi ya miko masa suka d’aure waje d’aya alamar promised.
Chapter 13 · 0% Book details