Sashe 2
Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin babbar harabar hall dake cikin Columbia university,mutanene zazzaune kowa kaga fuskarsa zaka ga farinciki da annashuwa a cikinta, daga saman stage suma wasu mutanene sanye da suit a jikinsu black colour , daga sama kuma gown ce a jikin su na graduation . Cikin tsantsan turanci da ke fito dako Wana kalma ake kiran sunayen daliban , bayan kowa ya karbi certificate din shi aka fara kiran wasu daga cikin daliban Domin basu award dinsu. Zaune yake cikin shigar suit dinshi fuskarsa sanye da face mask ya dukar da kai sai gashinkansa daya sakko masa har wajan idanuwansa, time to time yana duba diamond watched din dake hannunsa kafun ya mayar kan dan kareriyar wayarsa kirar Samsung, “ADIL BIN MOHAMMED Al_TAUFEEQâ€?, gabaki d’aya kowa jira yake yaga me sunan ya tashi amma kwata kwata Har yanxu babu Wanda ya mike , wata babbar macece ta kara kiran sunan tana duban daliban â€? the most talented person of the session,â€ADIL bin Mohammed Al taufeeq,are you around please â€?, wani na gefensa ne ya dan tabosa “ADIL ,MAAH is calling youâ€?, banza yayi wa na gefen nasa kamar be san da wani halitta a wajan ba , gabaki d’aya idanuwansa nakan wayarsa ,Akaro na uku aka kara kira sunan adil Mohammed Al-taufeeq, yanxu ba mashi da alama ko niyar tashi, â€? YAYA PRINCE â€?, sunan da ya bayyana akan screen din wayarsa , “finallyâ€? ya furta cikin wani daddadan muryarsa kafin ya mike a hankali, gabaki d’aya hall din tafi aka fara bakajin komai sai raf raf raf din tafi dake tashi, da ihu aka kiran “ADEEL, ADEELâ€? Wanda ya mike din cikin wani irin taku ya karasa inda ake kiransa, wani medium box ne brown colour da akayi rapping aka mika masa, kafun matar ta nuna masa wajan mic, har yanxu kansa a sunkuye yake be kalli kowa dake cikin hall din ba, gabaki d’aya hall din shiru ya dauka kowa jira yake yaji speech dinsa,shi kuma ganin yanda kowa yayi shiru ne yasashi dauke kansa shima batare da yace komai ba kusan mintuna uku,â€Little Booâ€?,kalmar ta sauka a kunnansa, da Sauri ya dago eyes dinsa da har yanxu gashi ya karesu,cikin sauri yake kallan mutanan wajan ko zea gansa, daga nesa dashi yaga an daga fingers guda biyu, murmushi ya saki duk da facemask din dake fuskarsa, a nutse ya fara bada speech din da ya dau hankulan mutanan wajan, gabaki d’aya cameras na kansa,yana kammala speech dinsa wajan ya kara daukar tafii da kalmar “ADEEL da ake ta faman kira, yana koma wa aka kara kiran sunansa as the most disciplined , dan guntun tsaki ya saki kamun ya koma, yana karba bece komai ba yayi wucewarsa, idanuwansa akan wajan da aka dago masa fingers dazu, so yake kawai yaga ankammala gabaki d’aya a ‘kage yake da ya bar wajan, akaro na uku aka kara kiransa , jiyay kamar ya make mekiran nasa , gabaki daya takaici duk ya kamasa,a karo na uku aka sake bashi wani gift din , Madam flora na kokarin bashi waje don yayi wani speech din ya bar wajan, a haka aka cigaba da kiran ragowar mutane 4 da zaa bawa gift suma, saida y karbi wasu gift din shima duk acikin student din ya fi kowa karbar gift din kowa ADIL TAUFEEQ zakaji yana kira kowa burinshi yayi hoto dashi, yana gani an gama ya mike da niyar barin wajan , duk yanda friends dinsa ke rokansa suyi hoto ba Wanda ya kula a cikinsu, cikin mutanan ya shiga kai tsaye amma be ga Wanda yake nema ba, kamar yayi kuka ya fita daga hall din, a tsaye ya hango wani black American sanye da black suits, idanuwansa rufe da ba’kin google, gabaki d’aya babu fara a cikin fuskarsa, da sauri ya karasa inda yake gift din hannunsa ya mika masa,cikin girmamawa ya amsa kafin ya sara musu,â€captainâ€? ya kira sunan mutumin, nuni mutumin yayi masa da wasu jerarrun motoci baka ke wuluk da suke zagane da wasu mutane masu kakin sojoji,batare da ya bari ya kuma cewa komai ba, cikin sauri sauri ya nufi wajan motocin, suna ganin sa suka sara masa,motocin ya fara bi da kallo yana jiran yaga ta ina zasu fito,daga bayansa yaji an furta “Littleâ€?, cikin wani daddadan murya, da mugun sauri ya juya tare da ware idanuwansa, beyi wata wata ba kawai ya Dane mutuminâ€? yaya prince dinaâ€? shima Wanda ya ‘Dane rungumeshi yayi a jikinsa a hankali ya furta â€? zaka karyani fa â€?, dariya ya saki yana sauka daga jikin mutumin, wani hadaddan guy ne fari tas dashi , kwata kwata rabin fuskarsa a kulle take sabida p_cap din data rufe masa rabin fuskarsa sai dan medium din bakinsa da ya fito pink dashi, kallan gefe da gefen mutumin yayi kafun ya furta â€? basu dawo bako,â€? ya furta cikin sanyin murya kamar me shirin yin kuka , “why the pity face, so kake BIG BOSS da YAYA BOBO suyi farfesu nane, they’re at home faâ€?, kugu little ya rike kafun ya furta â€? ka tabbata yaya princeâ€?, girgiza masa kai yayi kafin ya furta “toh nayi maka karya , if you like kayi ta zama , ni am going â€?, yana kammala maganar sa wani black American ya bude masa mota ya shiga, da sauri ADIL shima ya zaga daya bangaran nan ma wani American guy ne ya bude masa kofa , da mugun gudu motocin suka fita daga cikin Columbia university suka hau kan babban titin New York , mintuna 15 ne suka kawosu hadaddan street din FIFTH AVENUE dake cikin Garin new york, gabaki d’aya layin shiru kake ji kamar babu wani halitta da ke rayuwa a wajan sai sojojin da ke wucewa time time, Daidai wani babban area da mafi yawanci sojojin suka fi yawa suka nufa, gabaki d’aya sojojin mikewa sukai tare da sara musu, da mugun gudu wasu soldier su hudu suka fara bin bayan motar har suka karaso dai dai wani babban gate me shegen girma da tsaho, ba bata lokaci aka wangale musu gate din motocin su suka shiga ciki, kusan tafiyar mintuna biyu suka kara zuwa wani gate din da ya fi na farkon tsaro , awannan karan sai da aka caje motocin ta waje saida aka tabbatar da lafiyarsu kafun a wangale musu gate dinshima,wata ni’imtacciyar iskace ta fara ratsasu sabida flowers din da suka fara cin karo dasu, a wannan karan tafiyan minti biyar sukayi kan dogon titin dake wajan, wata kafuwar gate ne da kanta take budewa, ta wani slide din waje motocin suka wuce bayan gate din ya aunasu. Daga cikin motar ADIL ne ya dan kalli captain dake driving,â€? captain I give you 3 minutes ka karasar damu, if not zan fada wa big boss ya shigar da kai dakin duhuâ€?, kafun prince dake gefensa yayi magana captain yaja motar da mugun speed â€? azuciyarsa kuma yana auna irin horon da zai fuskanta idan ya karasa , sassaucin sama BOBO yayi mishi hukunci ba BIG BOSS ba, suma ragowar motocin suna ganin haka ko wannansu ya kara speed din motar, duk da sunsan dole su karbi hukunci wajan BOBO.ko gama parking ba ai ba Adil ya fito daga cikin motar ya arta a guje, masu tsaran kowa sunkuyar dakansa yayi cikin girmamawa, kofar babban masion din aka bushe masa , nan ma da mugun gudu ya shiga, wata kofar ya nufa me shegen kyau, yana shiga babban parlor ne ya bayyana me 4 set of designers , Aljannar duniya kenan gabaki d’aya falon sai ka dauka a wata nahiyar kake ba a duniya ba, falo ne da ya amsa sunan sa falo da ko me kudi be isa mallakar saba, naira tayi kuka ga wasu irin Logan modern stainless steel tiered crystal chandelier da ya kara haska falon, ko ina ka waiga haske ne tar, ga sanyin Ac dake busa ko ina na palour , cikin daga murya ya fara kiran â€? UNCLE IRON MAN, YAYA BIG BOSS ,YAYA BOBO,Little is backâ€?, yana maganar yana fincike mask din dake fuskarsa, fatabarakallahu ahsanin khalikin, kyakkyawa ne shi sosai da ya amsa sunan kyau, fari ne shi sosai duk da ba wani babba bane amma kyawunsa ya wuce misali, har yanxu bana iya ganin fuskarsa sabida gashin kansa da ya rufe masa rabin fuska sai kadan daga hancinsa da zaka gane dogone daya fito, sai dan karamin ba’kin shi pink kalo daya fito shima, Prince ne yashigo falon bakinshi dauke da sallama da sauri Little ya kalleshi duk da ba ganin idanuwansa ake sosai ba zaka gane hararar Prince yake, P_cap dinsa Prince ya saki, kyakkyawar sumar kansa itama ta sakko masa har wajan idanuwansa,gyara gashin nasa yayi kyakkyawar fuskarsa ta fito waje , ware idanuwansa yayi a kan little take eyes dinsa dasuka kasance ash colour suka fito waje sabida ware idanuwansa da yayi, shima kyakkyawa ne na ajin karshe , fadar irin kyawunsa ma bata baki ne, fuskarsa bame fadi bace sosai sannan ba doguwa bace, dai dai jikinsa ga dogon hancinsa daya kara fito da kyawun fuskarsa, dan madaidaici bakinsa ya tabe yana kara bin little da kallo ,cikin wani yare ya furta “Ni kake hararaâ€kamar mace little ya rike kugu tare da tura masa baki, a guje prince ya bi bayan little, shima little yana ganin hakan yasa gudu suka fara zagaye falon,â€stop there â€? Prince ya fada yana jefowa little pillow , shima little pillow ya dauka tare da jefowa prince â€? I won’t , ba kaine kace mun my loves sun dawo baâ€?, wani pillow Prince ya dauka ya jefawa little a fuska, ganin hakan yasa shima little daukan pillow, gabaki d’aya sun bata falon duk pillows din kujerun sai da suka sakko da shi kasa,wani pillow Prince ya dauka zai jefa wa little yaji saukar muryar data sashi faduwa â€? If you dare â€?, da Sauri ya jefar da abunda ke hannunsu, Prince ma mikewa yayi shida little suka hade waje daya , kana kallansu kasan basu da gaskiya , Cikin 3 quarter din wandan sojoji da bakar armless ya karaso cikin falon, kakkarfa surar jikinsa da kallo daya mutum zai yi masa yasan yana daga karfe, kyakkyawa ne sosai da ya amsa sunan kyau,