← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 146

Sashe 131

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

****************

Tsaye Abla take jikinta sanye apron da ta d’aura a ‘kugunta sai cap d’insa da ta d’aura shima , gaban ta Flour ne a ciki sai Luru ( kuka ) da ta d’auka a cikin kwalinsa, sai kuma ji’ka’k’kiyar potash ( kanwa ) da itama sai da ta saka aka nemo mata , a dole ta gaji da abincin su, shiyasa take itama taci d’an wake yau , su Little suna falour suna mata dariya sabida jin abinda tace zata yi musu, shi little tunda yake be ta’ba jin sunan d’an wake ba sai a bakinta , hatta Prince ma bai ta’ba jiba sai ayau , ko wannan su sai tsokanarta suke akan ita kad’ai zata ci abin cinta , itama tana musu dariya , uncle na gefe shima yana supporting d’in Abla , sosai tayi musu d’an wake me kyan gani da burgewa , sai cucumber da ta yanka tare da tunatur da attaruhu tare da onion da Koran tattasai cikin wani bwol me shegen kyau, ta samu fresh attaruhu guda biyu ta d’an daddakasu tare da matse leman tsami a ciki , sai wani Maggi cube na ruwa da ta saka tare da mai da ruwa ta had’a ta juya yanda komai zai ji ( Gaskiya duk wacce bata ta’ba cin d’an wake da wannan had’in na Nijer ba gaskiya anbarta Abaya ). Tana gama wa Oil ta soya , Little suna ganin ta fito da d’an waken suka dunga mata dariya � Little yanzu wannan ‘kazantar zakici ? I bet you bazai yi dad’i bafa � dariya tayi masa tana girgiza masa kai � No yaya little kar kazo kuma kace zaka cifa � d’an ya mutsa face d’insa yayi � Ni bazan ci wannan jagwalgwalan ba � hmm kawai Abla tace , cikin wani unique plate ta zuwa ba uncle tare da ruwan Gee da ta had’a , sai cilli powder d’in da sai da ta ‘kara gyara sa shima , tunda Suka ga na uncle suke kallansa , d’an hararar su uncle yayi � ba ci zakuyi ba , tun da kunce ‘kazan tane, mu ku bar mu zamuci � , yes uncle kunce jagwalgwalo ne , but atleast zaku temaka mugada ci muji ya d’an d’anan sa yake , ko little ?� Cewar Prince , da Sauri Little ya furta � yes yaya prince , mu daman bamu ce zamu ci mata ba � ta’be baki uncle yayi � Kunji da gulmar ku �, suma cikin wani plates din ta zuba musu, kafun su soma ci kamar zasu kai baki sai suyi saurin ajjewa suna ya mutsa face , ganin hakan yasa Abla d’auke plates d’in � No Lil please zamu ci fa � da haka Little ya runtse idanuwansa tare da yin 1 spoon , shima prince kallan sa yake yana kira yaji ko zai yi amai, sai da ya cinye tass na bakinsa tukunna ya fara ta’be face d’insa , � bari dai na ‘kara 1 spoon naji”tun daga 2 spoon d’in nan little ya share prince ya soma ci ganin haka shima prince ya d’an d’ana � Amma Little kai mugu ne Wallahi , shine zakayi mun shiru ?� Ita dai Abla dariya kawai take musu, sosai suka ci d’an waken nan , sai da suka ci suka ‘koshi tukunna suka saka game , sun dad’e abunsu suna game , saida suka gaji dan kansu tukunna suka soma hira har wajan 11 idanuwansu biyu, � Naga alama anan zaku kwana � cewar Uncle lokacin da ya mi’ke , shima cikin sauri prince ya mi’ke � har na kusa mantawa da aikina � gabaki d’aya sai kowa ya koma part d’insa .
Abla ko da ta koma d’aki ba bacci tayi ba dan yau gabaki d’aya neman baccin tayi ta rasa , “King The Land � ta saka ta cigaba da kallan korea d’inta , ita kad’ai sai murmushi take , ta dad’e tana kallo har ta soma yin hamma abunta , tun tana tunanin cigaba da kallan har bacci ya soma fusgarta, sai kashe system d’in tayi tayo alwalar baccin ta , cikin ‘kan’kanin lokaci bacci ya d’auke ta .

Washe gari Abla tana idar da sallah bacci ya ‘kara d’aukar , ba ita ta farka ba sai wajan ‘karfe 10 na safe , shaf shaf wanka tayi ta shirya cikin milk d’in riga sai wandon jeans da ta saka da yayi bala’in yi mata kyau , turare ta fesa ka d’an sai ta d’ora doguwar riga akai tare da rolling ta fito falourn , ta tsats tsaye ta tarar dasu Uncle ga wani mutum da sai ro’kan uncle yake akan yana so yana Big Boss , Bobo kuwa na zaune kamar be san yana yi ba , ba kowa bane face Mingus da gabaki d’aya ya fice cikin hayyacinsa , tun jiya yake ‘ko’karin san ganin su Bobo amma sojoji sun hana sa , da ‘kyar ya samu uncle ya sa baki har ya shigo cikin falourn, uncle yana ganin Abla ya sakar mata murmushi � Yawwa Daughter, please jeki kira wo mun Big Boss a sama � shiru Abla tayi kafun fa amsa masa da “Toh � ta nufi hanyar part d’in sa , tana zuwa sau biyu tayi knocking falourn sa shiru babu amsa , tana bud’ewa taga wayam babu kowa a cikin , na biyun ta bud’e ganin baya cikin falourn , kafa d’unta ta d’aga cikin rashin damuwa ta juya da niyar komawa , Daidai lokacin da shi kuma yake bud’e ‘kofar, sau d’aya Abla ta kallesa ta d’auke kanta, kamar wacce aka saka dole ta furta � Ina kwana?� Shiru yayi mata batare da ya amsa ba , itama bata sake gaishe saba ta fad’a masa sa’kon Uncle , ta juya zata soma tafiya ya finciko hannun ta da har sai da tayi ‘kara , ‘ko’karin kwace hannunta take ya ‘kara matse hannun, cikin tsiwa Abla ta d’ago da dara daran idanuwanta da suke faman shinning kamar zatayi kuka , bata re da ta kallesa ba ta ‘kara furta � ka sakar mu hannu na �, ‘kin sakar mata hannun yayi , takai cine ya kama Abla bata san lokacin da ta dam’ki hannun nasa ta gantsarawa cizo ba , sakin hannun nata yayi tare da kallan inda ta cizan har hakwaranta sun fito sosai a wajan, ta juya da niyar barin wajan ya finciko ya ‘kara dawowa baya , cikin Sauri Abla ta soma ja baya zata ‘kara guduwa , ganin yadda yake ‘kara matso tane yasa ta ‘kara ja baya bata san lokacin da ta jingina da bango ba , sai ganin ‘karasowar sa tayi, kauda kai Abla tayi tare da tsuke face d’inta , sosai ya ran’kwafo Daidai face d’inta yana kallan yadda ta tsuke face d’in ta , cikin cool voice ya furta � my food �, yana fad’an hakan ya d’an matsa , itama Abla bata kalle saba tayi wucewarta , sai data ga tabar falourn tukunna ta saki ‘karamun tsaki “My food !� Ajje ni kayi da zan kawo maka abincin, wallahi sai dai ko menene kayi mun amma babu wani abinci da zan kawo maka .

Tana sakkowa ta fad’awa Uncle gashinan zuwa , Mingus na zaune ya buga ta gumi kamar bashine ya gama kuri ba jiya , Abla kitchen ta koma ta had’a kayan breakfast d’inta dakanta cikin d’an ‘karamar tray ,ita kad’ai sai mita take , mistakenly pan d’in da take anfani dashi ya goce gabaki d’aya yayo kanta zai fad’o mata , bata san ya akai ba sai ji tayi an fincikota…�

https://chat.whatsapp.com/B5v9kh9BrGm6wjMuygdK1p

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written
By
Mss Lee �

🦅 MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION 🦅
🦅🦅M.W.A🦅🦅

AREWABOOKS: msslee
WATTPAD : Msslee__

✨MSS LEE BUSINESS WORLD �

💃💃💃💃 Ahayye Yar uwa kina business Amma bakida tambarin kasuwanci wato(logo& flyer) Maza ki garzayo ki kara mutuncin business dinki da customers ta hanyar logo da flyer Zaki jawo hankalin customers
Akwai Abubuwa da yawa dayakamata ace kinadasu a matsayinki na me business 👇🏻
🌹Logo
🌹Flyer
🌹Account sticker
🌹Business card
🌹Menus

🌷 payment received with thanks sticker Se asamiki Sunan business dinki wannan Yana matukar daukar hankalin customers
SANNAN INAYIN WASU ABUBUWAN KAMAR HAKA 👇🏻 🌹🌹 👇🏻
🌹Invitation Card
🌹Save the date
🌹calendar
🌹Book Cover
🌹Political poster
🌹Certificate
🌹Brochures
🌹Kar ku manta akwai Data cikin Sau’ki da arha tare da farashi me sau’kin gaske💃🏻💃🏻💃🏻.
Da sauransu duk a farashi me sauqi kardai na cikaku da surutu😄
Dan samun cikakken bayani zaku iya garxayo wa wajan MSS LEE BUSINESS WORLD , sannan zaku iya mata magana kai tsaye ta number wayarta kamar haka *07041879581*
Muna maraba da kowa da kowa 😍.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1
*PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.

NOT EDITED

S____37💞
Chapter 131 · 0% Book details